Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 8 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses, saying: Ubangiji ya ce wa Musa,
2 "Say to Aaron: When you mount the lamps, the seven must shine before the lampstand." “Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ”
3 Aaron did so, lighting its lamps to shine toward the lampstand's front, as our Father commanded Moses. Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
4 The lampstand's work: hammered gold, hammered from base to blossoms—made exactly as our Father showed Moses. Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa.
5 Our Father spoke to Moses, saying: Ubangiji ya ce wa Musa,
6 "Take the Levites from among the people of Israel and cleanse them. “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.
7 To cleanse them, do this: sprinkle purification water on them, run a razor over their whole body, wash their clothes, and be clean. Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu.
8 Let them take a young bull from the herd, its grain offering of fine flour mixed with oil, and you are to take a second young bull from the herd for a sin offering. Ka sa su ɗauki ɗan bijimi tare da lallausan garin hadaya, kwaɓaɓɓe da mai; sa’an nan, kai kuma ka ɗauki ɗan bijimi na biyu na hadaya don zunubi.
9 Bring the Levites before the tent of meeting, and gather the whole community of Israel's people. Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka.
10 When you present the Levites before me, Israelites are to lay hands on the Levites, Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu.
11 Aaron is to wave the Levites before me, an offering from the Israelites, to do my service. Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji.
12 The Levites will lay their hands on the bulls' heads; offer one as a sin offering, one as a burnt offering to me, to atone for the Levites. “Bayan Lawiyawa sun ɗibiya hannuwansu a kan bijiman, sai ka yi amfani da ɗaya a matsayin hadaya don zunubi ga Ubangiji, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa, don yin kafara saboda Lawiyawa.
13 Set the Levites before Aaron and his sons, and present them to me as a wave offering. Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da ’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.
14 Separate the Levites from among Israel's people; the Levites are mine. Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa.
15 Then the Levites will enter to serve the tent of meeting, once you've cleansed and waved them as a wave offering. “Bayan ka tsarkake Lawiyawa, ka kuma miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, sai su zo su yi aikinsu a Tentin Sujada.
16 For they are fully given to me from among Israel's sons, in place of every womb-opener—firstborn of all Israel's sons—I took them for myself. Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.
17 All Israel's firstborn, human or animal, are mine; the day I struck all Egypt's firstborn, I set them apart for myself. Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.
18 And I have taken the Levites in place of all the firstborn among the people of Israel. Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila.
19 I have given the Levites to Aaron and his sons, a gift from Israel's people, to serve Israel's people at the tent of meeting, atone for Israel's people, so no plague strikes Israel's people nearing the sanctuary." Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”
20 Moses, Aaron, and Israel's whole assembly did to the Levites all our Father commanded Moses about the Levites; Israel's people did to them. Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa.
21 The Levites purified themselves from sin, washed their clothes; Aaron offered them as a wave offering before our Father, atoned for them to cleanse them. Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su.
22 After that, the Levites came to serve in the tent of meeting before Aaron and his sons; they did to the Levites as our Father commanded Moses. Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
23 Our Father spoke to Moses, saying: Ubangiji ya ce wa Musa,
24 "This applies to the Levites: from age twenty-five, they are to come to serve in the work at the tent of meeting. “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada,
25 From age fifty they must retire from service work and serve no longer. amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki.
26 They may assist their brothers at the tent of meeting by standing guard, but do no work. This is how you are to assign the Levites' duties." Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]