Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Numbers 9 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Our Father spoke to Moses in the Sinai wilderness, in the first month of the second year after they left Egypt: Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai, a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar. Ya ce,
2 "Let the people of Israel keep the Passover at its appointed time. “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.
3 On this month's fourteenth day, at twilight, observe it at its set time, by all its statutes and all its rules." A yi wannan bikin ƙayyadadden lokaci da yamma, a rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, a yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa.”
4 So Moses told the people of Israel that they should keep the Passover. Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,
5 In the wilderness of Sinai, they kept the Passover on day fourteen of the first month, at twilight, as our Father commanded Moses; so the children of Israel did. suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa.
6 Some men were unclean from touching a corpse and could not observe Passover that day, so they came before Moses and Aaron that day. Amma waɗansunsu ba su iya yin Bikin Ƙetarewa a ranar ba gama sun ƙazantu ta wurin taɓa gawa. Saboda haka suka zo wurin Musa da Haruna a wannan rana
7 Those men said to him, "We are unclean from a dead body. Why must we be kept from presenting our Father's offering at its appointed time among the Israelites?" suka ce wa Musa, “Mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa, don me aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran Isra’ilawa a ƙayyadadden lokaci?”
8 And Moses said to them, "Wait here until I hear what our Father will command about this." Musa ya amsa musu ya ce, “Ku dakata sai na sami umarni daga wurin Ubangiji game da ku.”
9 Our Father spoke to Moses, saying, Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
10 "Tell the Israelites: if any of you or your descendants is unclean from a corpse, or off on a distant journey, he may still keep the Passover to our Father. “Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji.
11 In month two, on day fourteen, at twilight, they must keep it, eating it with unleavened bread and bitter herbs. Za su yi bikin da yamma, a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Za su ci naman tunkiya, tare da burodi marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.
12 They are to leave none of it until morning, break no bone of it, and keep it by every statute of the Passover. Kada su bar kome daga cikinsa yă kai safe, ko a karye ƙashinsa. Sa’ad da suke Bikin Ƙetarewa, dole su kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
13 But if a man is clean and not traveling, yet does not keep the Passover, that person must be cut off from his people, because he failed to bring our Father's offering at its set time; that man will bear his sin. Amma in mutumin da yake da tsarki bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi yă yi Bikin Ƙetarewar, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, domin bai miƙa hadaya ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.
14 "If a foreigner living among you wants to keep the Passover to our Father, he must follow the Passover's statute and rule. One statute applies to both foreigner and native of the land." “ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”
15 When the tabernacle—the tent of the testimony—was set up, the cloud covered it; from evening until morning it looked like fire over the tabernacle. A ranar da aka kafa Tenti na Alkawari, sai girgije ya rufe shi. Daga yamma har safe, girgijen da yake bisa tabanakul ya yi kama da wuta.
16 So it was continually: the cloud covered it by day, and the appearance of fire by night. Haka ya ci gaba da kasancewa; girgijen ya rufe shi, da dare kuma sai ya yi kamar wuta.
17 Whenever the cloud lifted from over the tent, the Israelites set out; wherever it settled, the Israelites camped. Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani.
18 At our Father's command Israel's people set out; at our Father's command they camped. As long as the cloud rested over the tabernacle, they remained camped. Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni.
19 When the cloud lingered over the tabernacle many days, the Israelites kept our Father's charge and did not set out. Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba.
20 Sometimes the cloud stayed on the dwelling only a few days: at the command of our Father they camped, at the command of our Father they set out. Wani lokaci girgijen yakan yi ’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi.
21 Sometimes the cloud stayed from evening to morning; when it lifted in the morning, they set out. Whether by day or night, when the cloud lifted, they set out. Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi.
22 Whether two days, a month, or longer, while the cloud remained over the tabernacle, Israel stayed in camp and did not set out; when it lifted, they set out. Ko girgijen ya yi kwana biyu a bisa tabanakul, ko wata guda, ko shekara, Isra’ilawa za su zauna a sansani ba kuwa za su tashi ba; amma sa’ad da aka ɗaga shi, sai su kuma su tashi.
23 At our Father's command they camped; at his command they set out. They kept his charge, at our Father's command through Moses. Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]