Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Jesus again taught by the sea. So large a crowd gathered around him that he got into a boat on the water and sat, while the whole crowd was on land by the sea. Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a ciki a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan.
2 He taught them many things in parables, and in his teaching he said to them: Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce,
3 "Listen! A sower went out to sow. “Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.
4 And as he sowed, some seed fell along the path, and the birds came and devoured it. Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su.
5 Other seed fell on rocky ground, lacking much soil, and sprang up at once since the soil had no depth. Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi.
6 When the sun rose, the plants were scorched, and since they had no root, they withered. Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa.
7 Other seed fell among thorns, and the thorns grew up and choked it, yielding no grain. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba.
8 Other seed fell into good soil, producing grain that sprouted, grew, and yielded thirty, sixty, one hundred times what was sown." Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”
9 And he said, "Whoever has ears to hear, let him hear." Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
10 When he was alone, those around him, together with the Twelve, asked him about the parables. Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan.
11 He said to them, "To you is given the secret of the kingdom of our Father, but to those outside, everything comes in parables, Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai.
12 so that 'they may look but not perceive, and hear but not understand, and not turn and be forgiven.'" Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”
13 He said to them, "You don't understand this parable? Then how will you understand all the parables? Sai Yesu ya ce musu, “Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan?
14 The sower sows the word. Manomi yakan shuka maganar Allah.
15 These are the ones on the path where the word is sown: once they hear, Satan comes immediately and takes away the word sown in them. Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.
16 These are the ones sown on rocky ground, who hear the word and immediately receive it with joy. Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.
17 But they have no root in themselves, lasting only briefly; when trouble or persecution comes because of the word, they fall away at once. Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.
18 And others are the ones sown among thorns. These are those who hear the word, Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar,
19 but worries of this age, the deceit of wealth, and desires for other things enter and choke the word, and it produces no fruit. amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani.
20 And these are the ones sown on good soil: they hear the word, accept it, and produce fruit—thirty, sixty, one hundred times over." Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”
21 He told them, "Does anyone bring in a lamp to put it under a basket or bed—not on a stand? Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba?
22 Nothing is hidden except to be revealed; nothing is secret except to surface. Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili.
23 If anyone has ears to hear, let him hear." Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”
24 He told them, "Watch what you hear. The measure you use will be measured to you—and more added. Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.
25 For whoever has will be given more; whoever doesn't, even what he has will be taken from him." Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
26 He said, "This is what the kingdom of our Father is like: a man scatters seed on the ground. Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.
27 Night and day, asleep or awake, the seed sprouts and grows, though he doesn't know how. A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba.
28 The soil yields grain on its own—first blade, then head, then full kernel in the head. Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya.
29 But when the grain ripens, he immediately sends the sickle, since harvest has come." Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”
30 He said, "What can we compare the kingdom of our Father to, or what parable can we use for it? Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi?
31 It's like a mustard seed, the smallest of all seeds when sown on the ground. Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona.
32 Yet once sown, it grows up and becomes the largest of all garden plants, producing branches so big that birds of the air can nest in its shade." Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.”
33 With many such parables he spoke the word to them, as they were able to hear. Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta.
34 He spoke to them only in parables, but privately explained everything to his own disciples. Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome.
35 That day, when evening came, he said to them, "Let us cross over to the other side." A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, “Mu ƙetare zuwa wancan hayi.”
36 They left the crowd and took him along, just as he was, in the boat, other boats accompanying him. Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi.
37 A fierce windstorm came up. Waves broke over the boat, so that it was already being swamped. Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa.
38 But Jesus was asleep in the stern on the cushion. They woke him and said, "Teacher, don't you care that we're dying?" Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”
39 He got up, rebuked the wind, and told the sea, "Peace! Be still!" The wind stopped, and it grew totally calm. Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.
40 He said to them, "Why are you so afraid? Do you still have no faith?" Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”
41 They were terrified and asked one another, "Who then is this, that even the wind and the sea obey him?" Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]