Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Once again Jesus entered the synagogue, and a man with a withered hand was there. Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu.
2 They watched closely to see if he'd heal the man on the Sabbath, to accuse Jesus. Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.
3 Jesus said to the man with the withered hand, "Stand up and come forward." Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”
4 Then he asked them, "Is it lawful on the Sabbath to do good or to do harm, to save life or to kill?" But they stayed silent. Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.
5 He looked around at them in anger, grieved by their hardness of heart, and told the man, "Stretch out your hand." He stretched it out, and his hand was restored. Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
6 Then the Pharisees went out and immediately began plotting with the Herodians how they might destroy him. Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu.
7 Jesus withdrew with his disciples to the sea; a large crowd from Galilee followed, and from Judea, Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi.
8 from Jerusalem, Idumea, beyond the Jordan, and the region around Tyre and Sidon—hearing all he was doing, a great crowd came to him. Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi.
9 He told his disciples to keep a small boat ready, because of the crowd, so they wouldn't crush him. Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi.
10 For he had healed so many that all who had diseases were pressing forward to touch him. Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi.
11 Whenever the unclean spirits saw him, they fell before him, shouting, "You are the Son of God!" Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”
12 But he firmly warned them not to reveal him. Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi.
13 Jesus went up the mountain and called those he wanted; they came to him. Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.
14 He appointed twelve, named apostles, so they could be with him and he could send them out to preach, Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi,
15 and to have authority to drive out demons. don kuma su sami ikon fitar da aljanu.
16 These are the twelve he appointed: Simon, to whom he gave the name Peter; Ga sha biyun da ya naɗa. Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);
17 James son of Zebedee, and John his brother, whom he named Boanerges, meaning Sons of Thunder; Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);
18 Andrew, Philip, Bartholomew, Matthew, Thomas, James son of Alphaeus, Thaddaeus, Simon the Zealot, Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,
19 and Judas Iscariot, who betrayed him. da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
20 He went home; the crowd gathered again, so he and his disciples couldn't even eat. Sai Yesu ya shiga wani gida, taro kuma ya sāke haɗuwa, har shi da almajiransa ma ba su sami damar cin abinci ba.
21 When his family heard, they went out to restrain him, for they said, "He's out of his mind." Da ’yan’uwansa suka sami wannan labari, sai suka tafi don su dawo da shi, suna cewa, “Ai, ya haukace.”
22 The scribes who came down from Jerusalem said, "He has Beelzebul," and, "By the prince of demons he drives out demons." Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
23 So Jesus called them to him and spoke in parables: "How can Satan drive out Satan? Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?
24 If a kingdom is divided against itself, that kingdom cannot stand. In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba.
25 And if a house is divided against itself, that house will not be able to stand. In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.
26 And if Satan opposes himself and is divided, he cannot stand; his end has come. In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.
27 No one can enter a strong man's house and take his goods without first tying up the strong man—then he can plunder the house. Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa.
28 Truly I tell you, all sins and insults against God will be forgiven children of mankind, whatever they say, Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi.
29 but whoever blasphemes against the Holy Spirit never has forgiveness; they are guilty of an eternal sin," Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”
30 for they were saying, "He has an unclean spirit." Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”
31 His mother and brothers arrived and, standing outside, sent to him, calling him. Sai mahaifiyar Yesu tare da ’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi.
32 A crowd sat around him and said to him, "Look, your mother and your brothers are outside, asking for you." Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.”
33 He answered them, "Who are my mother and my brothers?" Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?”
34 Looking around at those sitting in a circle around him, he said, "Here are my mother and my brothers! Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana!
35 Whoever does the will of our Father is my brother and sister and mother." Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]