Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 They came to the other side of the sea, to the region of the Gerasenes. Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa.
2 As Jesus left the boat, a man with an unclean spirit met him at once, from the tombs. Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi.
3 He lived among the tombs, and no one could bind him anymore, not even with a chain. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma.
4 For he'd often been bound with shackles and chains, but tore the chains apart and shattered the shackles—no one had strength to subdue him. Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi.
5 Night and day, among the tombs and on the mountains, he cried out constantly, cutting himself with stones. Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai.
6 And when he saw Jesus from a distance, he ran and fell down before him. Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa.
7 Shouting loudly, he said, "What do you want with me, Jesus, Son of the Most High God? I beg you by God, don't torment me!" Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”
8 For Jesus had been saying to him, "Come out of the man, you unclean spirit!" Gama Yesu ya riga ya ce masa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”
9 Jesus asked, "What is your name?" "Legion," he said, "we are many." Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.”
10 He kept begging him not to send them out of the region. Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin.
11 Now a great herd of pigs was feeding there on the hillside. A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo.
12 And they begged him, "Send us to the pigs; let us enter them." Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.”
13 He gave permission. The unclean spirits came out and entered the pigs; the herd—about 2,000—rushed down the cliff into the sea and drowned in the sea. Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.
14 The herders fled and told it in town and country; people came to see what happened. Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru.
15 They came to Jesus and saw the man who had been possessed by the demons, the one who'd had the legion, sitting there, dressed and thinking clearly—and they were afraid. Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro.
16 Eyewitnesses told them what had happened to the demon-possessed man, and about the pigs. Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun.
17 And they began to beg Jesus to leave their region. Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu.
18 As he was getting into the boat, the once-possessed man begged to be with him. Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi.
19 But Jesus refused, telling him instead, "Go home to your own people and tell them how much our Father has done for you, and how he has had mercy on you." Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”
20 He went and began proclaiming in the Decapolis all Jesus had done for him, and everyone was amazed. Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
21 When Jesus crossed again by boat to the other side, a large crowd gathered around him by the sea. Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin.
22 One of the synagogue leaders, named Jairus, came, saw Jesus, and fell at his feet, Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa,
23 and begged him urgently, "My little daughter is dying. Come, lay your hands on her, so she may be healed and live." ya roƙe shi da gaske ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.”
24 So Jesus went with him. And a great crowd followed him and pressed around him. Sai Yesu ya tafi tare da shi. Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.
25 And there was a woman with a discharge of blood that had gone on for twelve years. A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini.
26 She had suffered much under many doctors, spent all she owned, gained nothing, and only grew worse. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni.
27 Hearing about Jesus, she came up behind him in the crowd and touched his cloak. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa,
28 For she kept saying, "If I just touch his garments, I will be made well." domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.”
29 Her flow of blood dried up instantly, and she felt in her body that she was healed of her suffering. Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.
30 At once Jesus, aware that power had left him, turned around in the crowd and asked, "Who touched my clothes?" Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”
31 His disciples said to him, "You see the crowd crushing you, yet you ask, 'Who touched me?'" Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”
32 And he looked around to see who had done it. Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi.
33 But the woman, afraid and trembling, knowing what had happened to her, came, fell before him, and told him the whole truth. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru.
34 He told her, "Daughter, your faith made you well. Go in peace, healed of your suffering." Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”
35 While he was still speaking, people came from the synagogue leader's house, saying, "Your daughter has died. Why bother the Teacher any longer?" Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”
36 But Jesus overheard what they said and told the synagogue leader, "Don't fear, only believe." Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”
37 And he allowed no one to follow him except Peter, James, and John the brother of James. Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub.
38 They came to the synagogue leader's house and Jesus saw chaos—people weeping, wailing loudly. Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa.
39 Entering, he said to them, "Why this commotion and crying? The child isn't dead, just asleep." Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.”
40 They laughed at him. But he sent them all out, took the child's father and mother and his companions, and entered where the child was. Sai suka yi masa dariya. Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take.
41 He took her hand and said to her, "Talitha koum," which means, "Little girl, I say to you, get up!" Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”).
42 At once the girl got up and walked—for she was twelve—and they were instantly overwhelmed with great amazement. Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai.
43 He strictly ordered them to tell no one of this, and said to give her something to eat. Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yă san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]