Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 16 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When the Sabbath ended, Mary Magdalene, Mary the mother of James, and Salome bought spices to go anoint him. Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.
2 Very early on the first day of the week, just after sunrise, they went to the tomb. A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan,
3 They asked each other, "Who will roll the stone away from the tomb's entrance for us?" sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”
4 But looking up, they saw the stone—very large—already rolled away. Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne.
5 They entered the tomb and saw a young man dressed in a white robe, seated on the right. They were alarmed. Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.
6 "Don't be alarmed," he said. "You're looking for Jesus the Nazarene, who was crucified. He's risen—he isn't here. Look, the place they laid him. Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.
7 But go, tell his disciples and Peter, 'He goes ahead of you to Galilee. You will see him there, as he told you.'" Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ”
8 Trembling and amazed, the women fled the tomb, telling no one—they were afraid. Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.
9 Rising early the first day of the week, Jesus appeared first to Mary Magdalene, from whom he had driven seven demons. Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.
10 She went and told those who had been with him, who were mourning and weeping. Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka.
11 Hearing Jesus was alive and seen by her, they did not believe it. Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba.
12 Afterward Jesus appeared, in a different form, to two of them walking in the country. Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye.
13 They went back and reported it to the others, but they did not believe them either. Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba.
14 Later Jesus appeared to the eleven as they reclined at a meal and rebuked their lack of faith and hardness of heart, because they hadn't believed those who saw him risen. Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.
15 He said to them, "Go into all the world and proclaim the good news to all creation. Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.
16 Whoever believes and is baptized will be saved, but whoever does not believe will be condemned. Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.
17 And these signs will follow those who believe: in my name they'll drive out demons, speak in new tongues. Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna.
18 They will pick up snakes with their hands; if they drink deadly poison, it won't harm them; they will lay hands on the sick, and they will recover." Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”
19 After speaking to them, the Lord Jesus was taken up into heaven and sat at the right hand of our Father. Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah.
20 They went out and preached everywhere, the Lord working with them, confirming his word through accompanying signs. Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]