Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 15 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 At dawn the chief priests, elders, scribes, and the whole council consulted together, bound Jesus, led him away, and handed him over to Pilate. Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.
2 Pilate asked him, "Are you the King of the Jews?" "You say so," Jesus replied. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
3 The chief priests kept accusing him of many things. Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.
4 So Pilate questioned him again: "Have you no answer? See how many charges they bring against you." Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”
5 But Jesus said nothing more, and Pilate was amazed. Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
6 Now at the festival, Pilate used to release one prisoner for them—whoever they asked for. Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
7 A man called Barabbas was in prison with the rebels who had committed murder during the uprising. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.
8 The crowd came up and began asking Pilate to do for them what he always did. Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.
9 "Do you want me to release for you the King of the Jews?" Pilate answered, Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10 for he knew it was out of envy that the chief priests had handed him over. Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
11 But the chief priests stirred up the crowd to have him release Barabbas for them instead. Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
12 "So what do you want me to do with the one you call King of the Jews?" Pilate asked them again. Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
13 Crucify him!" they shouted back. Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
14 "Why? What evil has he done?" Pilate asked. But they shouted all the louder, "Crucify him!" Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
15 To satisfy the crowd, Pilate released Barabbas to them. He had Jesus flogged, and handed him over to be crucified. Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
16 Soldiers led him away into the palace (the governor's headquarters) and called together the whole company of soldiers. Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.
17 They dressed him in purple, twisted together a crown of thorns, and set it on him. Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.
18 And they began to salute him: "Hail, King of the Jews!" Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”
19 They kept beating his head with a staff, spat on him, and knelt in mock homage to him. Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a.
20 After mocking him, they stripped off the purple and put his own clothes on him, then led him out to crucify him. Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
21 They forced a passerby coming from the countryside—Simon of Cyrene, father of Alexander and Rufus—to carry his cross. Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.
22 They brought Jesus to the place called Golgotha (which means Place of a Skull). Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).
23 They offered him wine mixed with myrrh, but he did not take it. Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.
24 They crucified him. They divided his clothes among them, casting lots for what each would get. Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.
25 It was nine in the morning when they crucified him. Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
26 The written notice of the charge against him read: THE KING OF THE JEWS. Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa.
27 They crucified two rebels with him, one on his right and one on his left. Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
29 Those passing by insulted him, shaking their heads, saying, "Ha! You who tear down the temple and build it in three days, Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,
30 save yourself and come down from the cross!" sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”
31 Likewise the chief priests and scribes mocked him among themselves: "He saved others; himself he can't save. Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!
32 Let the Christ, King of Israel, come down from the cross now, so we can see and believe." Those crucified with him also insulted him. Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
33 At noon, darkness came over the whole land until three in the afternoon. Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.
34 At three in the afternoon Jesus cried out loudly, "Eloi, Eloi, lema sabachthani?" meaning, "My God, my God, why have you forsaken me?" A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
35 When some of those standing nearby heard this, they said, "Listen, he's calling Elijah." Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.”
36 One ran, filled a sponge with sour wine, put it on a reed, and gave him a drink. "Let him be," he said, "let's see if Elijah comes to take him down." Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.”
37 With a loud cry, Jesus breathed his last. Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.
38 And the curtain of the temple was torn in two from top to bottom. Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.
39 The centurion facing Jesus saw how he breathed his last and said, "Truly this man was the Son of God." Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”
40 Women were also watching from a distance, including Mary Magdalene, Mary the mother of James the younger and Joses, and Salome. Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.
41 These women had followed him in Galilee and served him; many others who came up with him to Jerusalem were also there. A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.
42 Evening had come, and since it was Preparation Day—the day before the Sabbath. Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai
43 Joseph of Arimathea, a prominent council member who himself was waiting for the kingdom of our Father, dared to go to Pilate and ask for Jesus' body. Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
44 Pilate was surprised he was already dead; summoning the centurion, he asked if Jesus had been dead long. Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.
45 When he learned from the centurion that it was so, he granted the body to Joseph. Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.
46 Joseph bought linen, took the body down, wrapped it in the cloth, and laid it in a tomb cut from rock. Then he rolled a stone against the tomb's entrance. Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.
47 Mary Magdalene and Mary the mother of Joses saw where he was laid. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]