1Two days before Passover and Unleavened Bread, the chief priests and scribes were looking for a way to seize Jesus by trickery and kill him.OHCBTo, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
2For they said, "Not during the feast, or the people might riot."OHCBSuka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”
3While he was in Bethany, in Simon the leper's house, reclining at the table, a woman came with an alabaster flask of pure nard perfume, very costly. She broke the flask and poured it on his head.OHCBYayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.
4There were some who said to themselves indignantly, "Why was this perfume wasted like that?OHCBWaɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?
5For this perfume could have sold for over 300 denarii and given to the poor." And they scolded her.OHCBDa an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”
6But Jesus said, "Leave her alone. Why trouble her? She has done a beautiful thing for me.OHCBYesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.
7For the poor are always with you, and you can do good for them whenever you want; but you won't always have me.OHCBMatalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.
8She has done what she could; she has anointed my body beforehand for burial.OHCBTa yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata.
9Truly, I tell you, wherever the gospel is preached worldwide, what she did will be told in memory of her."OHCBGaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”
10Then Judas Iscariot, one of the twelve, went to the chief priests to betray Jesus to them.OHCBSai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.
11Hearing this, they were glad and promised him money. So he looked for a chance to betray Jesus.OHCBSuka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.
12On the first day of Unleavened Bread, when they sacrificed the Passover lamb, his disciples asked him, "Where do you want us to go and prepare for you to eat the Passover?"OHCBA rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
13He sent two of his disciples, "Go into the city; a man carrying a jar of water will meet you. Follow him,OHCBSai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
14and wherever he enters, tell the house's owner, 'The Teacher says: Where is my guest room, where I may eat the Passover with my disciples?'OHCBGidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’
15And he will show you a large upper room furnished and ready; there prepare for us."OHCBZai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”
16The disciples left, went to the city, found things as he had told them, and prepared the Passover.OHCBAlmajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
17And when it was evening, Jesus came with the twelve.OHCBDa yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.
18While they reclined and ate, Jesus said, "Truly, I tell you, one of you will betray me, one eating with me."OHCBYayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”
19They began to grieve and ask him, one by one, "Is it I?"OHCBSuka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”
20He said to them, "One of the twelve, dipping bread with me into the dish.OHCBYa ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano.
21The Son of Man goes as the Scriptures said about him, but how terrible for that man who betrays him—better if he had never been born."OHCBƊan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”
22As they ate, he took bread, blessed it, broke it, gave it to them, and said, "Take; this is my body."OHCBYayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”
23He took a cup, gave thanks, gave it to them, and they all drank from it.OHCBSai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.
24He said to them, "This is my blood of the covenant, poured out for many.OHCBSai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.
25Truly I tell you, I will not drink wine again until that day when I drink it new in the kingdom of our Father."OHCBGaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”
26And when they had sung a hymn, they went out to the Mount of Olives.OHCBDa suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
27Jesus said to them, "You will all stumble, for it's written: 'I will strike the shepherd, and the sheep will be scattered.'OHCBYesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’
28But after I am raised up, I will go ahead of you to Galilee."OHCBAmma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
29Peter said to him, "Even though they all fall away, I will not."OHCBBitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”
30Jesus said to him, "Truly I tell you, today, this night, before the rooster crows twice, you will deny me three times."OHCBYesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”
31But he insisted, "Even if I must die with you, I will never deny you." They all said the same.OHCBAmma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
32They arrived at a place called Gethsemane, and he told his disciples, "Sit here while I pray."OHCBSuka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.”
33He took Peter, James, and John, and began to feel deep distress and anguish.OHCBYa tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.
34He said to them, "My soul is crushed with grief, to death. Stay here and stay alert."OHCBSai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”
35Going a little farther, he fell to the ground and prayed that, if possible, the hour would pass from him.OHCBSai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a.
36He said, "Abba, Father, all things are possible for you. Take this cup from me—but let it be your will, not mine."OHCBYa ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”
37He returned, found them asleep, and said to Peter, "Simon, are you asleep? Couldn't you stay awake one hour?OHCBSai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya?
38Watch and pray, so you don't fall into temptation. The spirit is willing, but the flesh is weak."OHCBKu yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
39And again he went away and prayed, saying the same words.OHCBYa sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi.
40Again he found them sleeping, eyes heavy, not knowing how to answer him.OHCBDa ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.
41He came a third time and said, "Still sleeping and resting? Enough—the hour has come. Look, the Son of Man is handed over into the hands of sinners.OHCBDa ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.
42Rise, let us be going; see, my betrayer is here."OHCBKu tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”
43While he was still speaking, Judas—one of the twelve—arrived, and with him a crowd with swords and clubs from the chief priests, scribes, and elders.OHCBYana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.
44His betrayer had given them a signal: "The one I kiss is him—seize him and take him away securely."OHCBMai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.”
45He came up to Jesus at once, said, "Rabbi!" and kissed him.OHCBNan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba.
46And they laid hands on him and seized him.OHCBMutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.
47One of the bystanders drew his sword, struck the high priest's servant, and cut off his ear.OHCBSai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.
48Jesus said to them, "Have you come out with swords and clubs to seize me, like a robber?OHCBYesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni?
49Every day I was with you in the temple teaching, and you didn't arrest me. But let the Scriptures be fulfilled."OHCBKowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.”
50And they all left him and fled.OHCBSai kowa ya yashe shi ya gudu.
51And a young man followed him, wearing nothing but a linen cloth. And they seized the young man,OHCBWani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi,
52but he left the linen cloth and ran away naked.OHCBsai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.
53They led Jesus to the high priest, and all the chief priests and elders and scribes gathered.OHCBSuka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.
54Peter had followed at a distance, all the way into the high priest's courtyard, and sat with the guards, warming himself by the fire.OHCBBitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.
55The chief priests and the whole council sought testimony against Jesus to put him to death, but found none.OHCBManyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.
56For many gave false testimony against him, but their testimony did not agree.OHCBDa yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
57And some stood up and gave false testimony against him, saying,OHCBSai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,
58"We heard him say, 'I will destroy this temple made by hands, and in three days build another not made by hands.'"OHCB“Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ”
59Yet even about this their testimony did not agree.OHCBDuk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
60The high priest stood up in the midst and asked Jesus, "You have no answer? What are these men testifying against you?"OHCBSai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”
61He stayed silent, answered nothing. Again the high priest asked him, "Are you the Christ, the Son of the Blessed?"OHCBAmma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”
62Jesus said, "I AM, and you will see the Son of Man seated at the right hand of the Mighty One and coming with heaven's clouds."OHCBYesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”
63And the high priest tore his clothes and said, "What further witnesses do we need?OHCBBabban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma?
64You have heard his blasphemy. What is your decision?" And they all condemned him as deserving death.OHCBKun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa.
65Some began spitting on him, covering his face, and punching him, saying to him, "Prophesy!" Then the guards slapped him.OHCBSai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.
66While Peter was below in the courtyard, one of the high priest's servant girls came,OHCBYayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can.
67seeing Peter warming himself, she looked at him and said, "You too were with the Nazarene, Jesus."OHCBDa ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”
68But he denied it: "I don't know or understand what you mean." Then he went out to the entrance, and a rooster crowed.OHCBAmma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.
69The servant girl saw him and again told the bystanders, "This man is one of them."OHCBDa baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”
70But he denied it again. A little later the bystanders again told Peter, "You truly are one of them, for you're a Galilean."OHCBSai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”
71He began to call down curses on himself and swear, "I don't know this man you're talking about."OHCBSai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”
72At once a rooster crowed a second time. Peter remembered Jesus' words: "Before the rooster crows twice, you will deny me three times." He broke down and wept.OHCBNan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.