Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Mark 13 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Leaving the temple, one of his disciples said to him, "Teacher, look! What huge stones, what magnificent buildings!" Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!”
2 Jesus said to him, "Do you see these great buildings? Not one stone will remain here on another; all will be torn down." Yesu ya amsa ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”
3 As he sat on the Mount of Olives facing the temple, Peter, James, John, and Andrew asked him privately, Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce,
4 tell us, when will these things happen, and what sign shows all this is about to be fulfilled? “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”
5 Jesus began to tell them: "Watch out that no one deceives you. Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku.
6 Many will come in my name, claiming, 'I am he,' and they will deceive many. Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
7 When you hear of wars and rumors of wars, don't be troubled—these must happen, but the end isn't yet. Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.
8 Nation will rise against nation, kingdom against kingdom, earthquakes in various places, famines—these are the beginning of birth pains. Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.
9 Watch yourselves. They'll hand you to councils and beat you in synagogues. Because of me you'll stand before governors and kings, as a testimony to them. “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.
10 And the gospel must first be proclaimed to all nations. Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.
11 When they arrest and hand you over, don't worry beforehand what to say. Say whatever you're given in that hour—it's not you speaking, but the Holy Spirit. Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12 Brother will betray brother to death, father his child. Children will rise against parents and have them put to death. “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
13 All will hate you for my name, but whoever endures to the end will be saved. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
14 When you see the abomination of desolation standing where it should not be (reader, take note), those in Judea must flee to the mountains. “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’ tsaye inda bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.
15 Let no one on the housetop go down or enter the house to take anything out. Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu.
16 Let no one in the field go back to get their coat. Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa.
17 How dreadful it will be in those days for pregnant women and nursing mothers! Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!
18 Pray that it will not happen in winter, Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi.
19 for those days will bring suffering unmatched since our Father created the world until now—and never to be matched again. Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.
20 Had the Sovereign not shortened those days, no one would survive; but the Sovereign shortened them for the elect he chose. “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin.
21 Then if anyone tells you, 'Look, here is the Christ!' or 'Look, there!' don't believe it. A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata.
22 False christs and false prophets will appear, performing signs and wonders to deceive the elect, if possible. Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.
23 So be on your guard; I have told you everything ahead of time. Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.
24 But in those days, after that suffering, the sun will darken, and the moon will not give its light; “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
25 the stars will fall from the sky, and the powers in the heavens will be shaken. taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’
26 Then they will see the Son of Man coming in clouds with great power and glory. “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma.
27 He will send his angels and gather his chosen from the four winds, from earth's ends to heaven's ends. Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.
28 Learn this from the fig tree: once its branch softens and leaves sprout, you know summer is near. “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan.
29 So also, when you see these things happening, know it's near, at the door. Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.
30 Truly I tell you, this generation will certainly not pass away until all these things have happened. Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru.
31 Heaven and earth will pass away, but my words will never pass away. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
32 But no one knows that day or hour—not the angels in heaven, not the Son, only the Father. “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai.
33 Be on guard! Stay alert! For you do not know when that time will come. Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba.
34 Like a man on a journey: he leaves his house, gives his servants authority—each his own task—and orders the doorkeeper to stay alert. Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.
35 So stay alert, since you don't know when the master of the house comes—evening, midnight, rooster's crow, or dawn. “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne.
36 Otherwise, if he comes suddenly, he may find you sleeping. In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci.
37 What I say to you, I say to everyone: Keep watch!" Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]