Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Luke 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Since many have undertaken to compile an ordered account of what has been accomplished among us. Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu,
2 Just as eyewitnesses from the beginning and servants of the word handed these accounts to us, kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara.
3 I too, having traced everything accurately from the start, decided to write it in order for you, most excellent Theophilus, Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus,
4 so that you may know the certainty of the things you have been taught. don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai.
5 In the days of Herod, king of Judea, a priest named Zechariah was in Abijah's priestly division. His wife Elizabeth descended from Aaron. A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ’yar zuriyar Haruna ce.
6 They were both righteous before our Father, walking blamelessly in all his commandments and ordinances. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.
7 But they had no child, because Elizabeth was barren, and both were very old. Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.
8 Now while he was serving as priest before our Father when his division was on duty, Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah,
9 by priestly custom, lot chose him to enter his sanctuary and burn incense. sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare.
10 And the whole crowd of the people were praying outside at the hour of incense. Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna addu’a.
11 Then an angel of our Father appeared to him, standing at the right of the altar of incense. Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare.
12 Zechariah was shaken when he saw him, and fear came over him. Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi.
13 The angel said to him, "Don't be afraid, Zechariah—your prayer has been heard. Your wife Elizabeth will bear you a son; name him John. Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna.
14 You will have joy and gladness; many will rejoice at his birth. Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa,
15 He will be great before our Father, must never drink wine or other alcoholic drinks, and he will be filled with the Holy Spirit even from his mother's womb. gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.
16 And he will turn many of the children of Israel back to their Father. Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu.
17 He will go before our Father in Elijah's spirit and power, turning fathers' hearts to their children, and the disobedient to the wisdom of the righteous, to prepare a people ready for our Father." Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”
18 Zechariah said to the angel, "How will I know this? I'm old, and my wife is well along in years." Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”
19 The angel answered him, "I am Gabriel, who stands in our Father's presence, sent to speak to you and bring you this good news. Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi.
20 And now you will be silent, unable to speak, until the day these things happen, because you did not believe my words, which will come true in their time." Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”
21 Meanwhile the people waited for Zechariah, wondering why he stayed so long in the sanctuary. Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali.
22 When he came out, he could not speak to them, and they knew he had seen a vision in the sanctuary. He kept motioning to them and stayed mute. Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.
23 And when his days of service were ended, he went home. Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida.
24 After these days his wife Elizabeth became pregnant, and for five months she kept herself hidden, saying, Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar.
25 "This is what our Father did for me, in the days he looked on me, to remove my disgrace among people." Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”
26 In month six our Father sent the angel Gabriel to a Galilee town called Nazareth, A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili,
27 to a virgin engaged to a man named Joseph, of the house of David; the virgin's name was Mary. gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu.
28 And he came to her and said, "Greetings, favored one! Our Father is with you." Mala’ikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.”
29 But she was greatly troubled by his words, and wondered what kind of greeting this might be. Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka?
30 The angel said to her, "Don't be afraid, Mary, for you have found favor with our Father. Amma mala’ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.
31 You will conceive in your womb and bear a son, and you will call his name Jesus. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu.
32 He will be great and called Son of the Most High, and our Father will give him the throne of his father David, Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,
33 and he will reign over Jacob's house forever; his kingdom will never end." zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”
34 And Mary said to the angel, "How will this be, since I am a virgin?" Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?”
35 The angel answered her, "The Holy Spirit will come over you, and the Most High's power will shadow you; so the holy child born will be called the Son of our Father. Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.
36 Look, your relative Elizabeth has also conceived a son in her old age—this is the sixth month for her called barren. ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida.
37 For nothing will be impossible with our Father." Gama ba abin da zai gagari Allah.”
38 Mary said, "I am the servant of our Father; let it happen to me as you said." Then the angel left her. Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa.
39 In those days Mary got up and hurried to the hill country, to a town in Judah, A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya,
40 and she entered the house of Zechariah and greeted Elizabeth. inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet.
41 When Elizabeth heard Mary's greeting, her baby leaped in her womb, and she was filled with the Holy Spirit. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.
42 She cried out with a loud voice, "Blessed are you among women, blessed is the fruit of your womb! Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa!
43 And why is this granted to me, that the mother of my Lord should come to me? Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina?
44 For the moment I heard your greeting, the baby in my womb leaped for joy. Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.
45 Blessed is she who believed that there would be a fulfillment of what our Father spoke to her." Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”
46 And Mary said, "My soul magnifies our Father, Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47 and my spirit rejoices in our Father, my Savior, ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48 for he has looked on the humble estate of his servant. For from now on all generations will call me blessed; gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49 for the Mighty One has done great things for me, and holy is his name. gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne.
50 And his mercy is for those who fear him from generation to generation. Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani.
51 He has shown strength with his arm; he has scattered the proud in the thoughts of their hearts; Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.
52 he has brought down the mighty from their thrones and lifted up the humble; Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53 he has filled the hungry with good things, and the rich he has sent away empty. Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi.
54 He has helped his servant Israel, in remembrance of his mercy, Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai
55 just as he spoke to our fathers, to Abraham and to his offspring forever." ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”
56 And Mary remained with her about three months and then returned to her home. Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.
57 Now the time came for Elizabeth to give birth, and she bore a son. Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.
58 Her neighbors and relatives heard our Father had shown her great mercy, and rejoiced with her. Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.
59 On the eighth day they came to circumcise the child, and were going to call him Zechariah after his father, A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne,
60 but his mother answered, "No; he will be called John." amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”
61 And they said to her, "None of your relatives is called by this name." Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”
62 And they made signs to his father, asking what Zechariah wanted the child to be called. Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron.
63 He asked for a tablet and wrote, "His name is John." And everyone was amazed. Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
64 And immediately his mouth was opened and his tongue loosed, and he spoke, blessing our Father. Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.
65 Fear fell on all their neighbors, and all these things were talked about throughout Judea's hill country. Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya.
66 And all who heard kept these things in their hearts, saying, "What then will this child become?" For our Father's hand was with him. Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.
67 And his father Zechariah was filled with the Holy Spirit and prophesied, saying, Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,
68 "Blessed be our Father of Israel, for he has visited and redeemed his people, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69 and has raised up a mighty Savior for us in the house of his servant David, Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda
70 as he spoke through the mouth of his holy prophets long ago, (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
71 that we should be saved from our enemies and from the hand of all who hate us; cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu
72 to show the mercy promised to our fathers and to remember his holy covenant, don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73 the oath that he swore to our father Abraham, to grant us, rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,
74 that we, being delivered from the hand of our enemies, might serve him without fear, don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,
75 in holiness and righteousness before him all our days. cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.
76 And you, child, will be called the prophet of the Most High; for you will go before the Lord to prepare his ways, “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,
77 to give his people the knowledge of salvation through the forgiveness of their sins, don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,
78 because of the tender mercy of our Father, by which the sunrise from on high will visit us, saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,
79 to give light to those who sit in darkness and in the shadow of death, to guide our feet into the way of peace." don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”
80 The child grew, became strong in spirit, and lived in the wilderness until the day he appeared publicly to Israel. Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]