Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Luke 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In those days Caesar Augustus issued a decree to register the whole inhabited world. A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma.
2 This was the first registration, when Quirinius was governor of Syria. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)
3 Everyone went to be registered, each to his own town. Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.
4 Joseph too went up from Galilee, from the town of Nazareth, to Judea, to the city of David called Bethlehem, since he belonged to David's house and family, Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.
5 to be registered with Mary, his fiancée, who was expecting a child. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.
6 While they were there, the time came for her to give birth. Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi,
7 She gave birth to her firstborn son, wrapped him in cloths, and laid him in a manger, because the inn had no place for them. ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.
8 Shepherds were in that same region, staying out in the fields, keeping watch over their flock by night. Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.
9 An angel of our Father stood before them; the glory of our Father shone around them, and great fear seized them. Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.
10 The angel told them, "Don't be afraid—I bring good news of great joy for everyone: Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.
11 Today in the city of David, a Savior was born to you—Christ the Lord. Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.
12 This is your sign: you'll find a baby wrapped in cloths, lying in a manger." Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”
13 Suddenly there was with the angel a multitude of the heavenly host, praising our Father and saying, Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,
14 "Glory to our Father in the highest, and on earth peace among those with whom he is pleased!" “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
15 When the angels left them for heaven, the shepherds said to each other, "Let's go straight to Bethlehem and see this thing that has happened, which our Father has made known to us." Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”
16 They hurried off and found Mary and Joseph, and the baby lying in the manger. Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami.
17 When they saw him, they made known what had been told them about this child. Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron,
18 All who heard were amazed at what the shepherds told them. duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa.
19 But Mary treasured up all these things, pondering them in her heart. Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta.
20 The shepherds returned, glorifying and praising our Father for all they'd heard and seen, just as they were told. Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
21 When eight days for his circumcision were complete, he was named Jesus, the name the angel gave before he was conceived in the womb. A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.
22 When their days of purification under the Law of Moses ended, they brought him up to Jerusalem to present him to our Father, Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji
23 (as it is written in our Father's Law, "Every firstborn male will be called holy to our Father"), (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),
24 and to offer a sacrifice as the Law of our Father says: a pair of turtledoves or two young pigeons. don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.”
25 In Jerusalem lived a man named Simeon, righteous and devout, waiting for Israel's comfort, with the Holy Spirit on him. To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
26 The Holy Spirit had revealed to him he wouldn't die before seeing our Father's Christ. An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.
27 Prompted by the Spirit, he entered the temple. As the parents brought in the child Jesus to do for him what the Law required, Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,
28 Simeon took him up in his arms and blessed our Father, saying, sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,
29 "Sovereign Father, now you are letting your servant depart in peace, according to your word. “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.
30 For my eyes have seen your salvation, Gama idanuna sun ga cetonka,
31 which you have prepared in the presence of all peoples: wanda ka shirya a gaban dukan mutane,
32 a light for revelation to the Gentiles, and for glory to your people Israel." haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”
33 His father and mother were amazed at what was said about him. Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.
34 And Simeon blessed them and told Mary, his mother, "This child is appointed for the fall and rising of many in Israel, and to be a sign that is opposed, Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,
35 and a sword will pierce through your own soul also—so that thoughts from many hearts may be revealed." ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”
36 Also there was Anna, a woman prophet, daughter of Phanuel of Asher's tribe, very old, having lived with her husband seven years after her virginity, Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,
37 and a widow until eighty-four, never leaving the temple, worshiping with fasting and prayer night and day. ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.
38 Coming up at that same hour, she gave thanks to our Father and spoke of the child to all awaiting Jerusalem's redemption. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.
39 When they finished everything required by our Father's Law, they returned to Galilee, to their own town of Nazareth. Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.
40 The child grew, becoming strong, filled with wisdom, and our Father's favor was on him. Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.
41 Now his parents went to Jerusalem every year at the Feast of Passover. Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.
42 When he was twelve years old, they went up according to the custom of the feast. Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada.
43 When the festival ended and they left for home, the boy Jesus stayed behind in Jerusalem, unknown to his parents. Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.
44 Thinking he was in the group, they traveled a day's journey, then searched for him among relatives and acquaintances. Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu.
45 When they did not find him, they returned to Jerusalem, searching for him. Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa.
46 After three days they found him in the temple, sitting among the teachers, listening to them and asking them questions. Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi.
47 All who heard him were amazed at his understanding and his answers. Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.
48 When his parents saw him, they were astonished. His mother said, "Child, why have you done this to us? Look, your father and I have been anguished, searching for you." Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”
49 He said to them, "Why were you searching for me? Didn't you know I must be in my Father's house?" Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”
50 But they did not understand the saying that he spoke to them. Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
51 Then he went down with them and came to Nazareth, remaining obedient to them. His mother kept all these things in her heart. Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.
52 Jesus increased in wisdom and stature and in favor with our Father and with people. Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]