Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Luke 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In Tiberius Caesar's fifteenth year, when Pontius Pilate was governor of Judea, Herod was tetrarch of Galilee, his brother Philip of the region of Ituraea and Trachonitis, and Lysanias of Abilene, A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.
2 under high priests Annas and Caiaphas, our Father's word came to John son of Zechariah in the wilderness. A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.
3 He went through the whole Jordan region, preaching a baptism of repentance for the forgiveness of sins, Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.
4 as it is written in the book of the words of Isaiah the prophet: "A voice of one calling in the wilderness: Prepare the way for the Lord, make his paths straight. Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.
5 Every valley will be filled in, and every mountain and hill made low. The crooked roads will become straight, and the rough ways smooth, Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.
6 and all flesh will see the salvation of our Father." Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”
7 John said then to the crowds coming to be baptized by him: "You brood of vipers! Who warned you to flee the coming wrath? Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?
8 So produce fruit worthy of repentance. Don't start telling yourselves, 'We have Abraham as our father.' For I tell you, our Father can raise up children for Abraham from these stones. Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.
9 Already the axe lies at the root of the trees; every tree not bearing good fruit is cut down and thrown into the fire." An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”
10 And the crowds asked him, "What then should we do?" Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?”
11 He replied, "Whoever has two shirts, share with the one who has none; whoever has food, do the same." Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”
12 Tax collectors also came to be baptized, and they said to him, "Teacher, what should we do?" Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”
13 "Collect no more than you are required to," he told them. Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”
14 Soldiers also asked him, "And us—what should we do?" He said to them, "Don't extort anyone by force or false charges; be satisfied with your wages." Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”
15 The people were expectant, all wondering in their hearts whether John himself might be the Christ. Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa.
16 John answered them all, "I baptize you with water. But one stronger than I is coming—I'm not worthy to untie his sandal strap. He will baptize you with the Holy Spirit and fire. Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.
17 Winnowing fork in hand, he will clear his threshing floor, gather the wheat into his barn, but burn the chaff with fire that can't be put out." Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
18 And with many other words of exhortation, John proclaimed the good news to the people. Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.
19 But John confronted Herod the tetrarch about Herodias, his brother's wife, and about all the evil Herod had done, Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi,
20 Herod added this to all the rest: he locked John up in prison. Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.
21 When all the people were baptized, Jesus was baptized too. As he prayed, heaven opened, Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe,
22 and the Holy Spirit descended on him in bodily form like a dove. And a voice came from heaven: "You are my beloved Son; in you I delight." Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”
23 Jesus was about thirty when he began his ministry, the son—so it was thought—of Joseph, son of Heli, To, Yesu kansa yana da shekaru kusan talatin da haihuwa sa’ad da ya fara aikinsa. An ɗauka shi ɗan Yusuf ne, ɗan Heli,
24 the son of Matthat, the son of Levi, the son of Melchi, the son of Jannai, the son of Joseph, ɗan Mattat, ɗan Lawi, ɗan Melki, ɗan Yannai, ɗan Yusuf,
25 the son of Mattathias, the son of Amos, the son of Nahum, the son of Esli, the son of Naggai, ɗan Mattatiyas, ɗan Amos, ɗan Nahum, ɗan Esli, ɗan Naggai,
26 the son of Maath, the son of Mattathias, the son of Semein, the son of Josech, the son of Joda, ɗan Ma’at, ɗan Mattatiyas, ɗan Semeyin, ɗan Yosek, ɗan Yoda,
27 the son of Joanan, the son of Rhesa, the son of Zerubbabel, the son of Shealtiel, the son of Neri, ɗan Yowanan, ɗan Resa, ɗan Zerubbabel, ɗan Sheyaltiyel, ɗan Neri,
28 the son of Melchi, the son of Addi, the son of Cosam, the son of Elmadam, the son of Er, ɗan Melki, ɗan Addi, ɗan Kosam, ɗan Elmadam, ɗan Er,
29 the son of Joshua, the son of Eliezer, the son of Jorim, the son of Matthat, the son of Levi, ɗan Yoshuwa, ɗan Eliyezer, ɗan Yorim, ɗan Mattat, ɗan Lawi,
30 the son of Simeon, the son of Judah, the son of Joseph, the son of Jonam, the son of Eliakim, ɗan Simeyon, ɗan Yahuda, ɗan Yusuf, ɗan Yonam, ɗan Eliyakim,
31 the son of Melea, the son of Menna, the son of Mattatha, the son of Nathan, the son of David, ɗan Meleya, ɗan Menna, ɗan Mattata, ɗan Natan, ɗan Dawuda,
32 the son of Jesse, the son of Obed, the son of Boaz, the son of Salmon, the son of Nahshon, ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,
33 the son of Amminadab, the son of Admin, the son of Arni, the son of Hezron, the son of Perez, the son of Judah, ɗan Amminadab, ɗan Ram, ɗan Hezron, ɗan Ferez, ɗan Yahuda,
34 the son of Jacob, the son of Isaac, the son of Abraham, the son of Terah, the son of Nahor, ɗan Yaƙub, ɗan Ishaku, ɗan Ibrahim, ɗan Tera, ɗan Nahor,
35 the son of Serug, the son of Reu, the son of Peleg, the son of Eber, the son of Shelah, ɗan Serug, ɗan Reyu, ɗan Feleg, ɗan Eber, ɗan Sala,
36 the son of Cainan, the son of Arphaxad, the son of Shem, the son of Noah, the son of Lamech, ɗan Kainan, ɗan Arfakshad, ɗan Shem, ɗan Nuhu, ɗan Lamek,
37 the son of Methuselah, the son of Enoch, the son of Jared, the son of Mahalalel, the son of Cainan, ɗan Metusela, ɗan Enok, ɗan Yared, ɗan Mahalalel, ɗan Kainan,
38 the son of Enosh, the son of Seth, the son of Adam, the son of our Father. ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]