Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 9 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 As Jesus passed by, he saw a man who had been blind from birth. Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho.
2 His disciples asked him, "Rabbi, who sinned, this man or his parents, that he was born blind?" Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”
3 "Neither this man nor his parents sinned,' Jesus answered, 'but this happened so the works of our Father might be revealed in him. Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.
4 We must do the works of the one who sent me while it is day; night comes, when no one can work. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.
5 As long as I am in the world, I am the light of the world.'" Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”
6 Saying this, he spat on the ground, made mud from the saliva, and smeared it on the man's eyes. Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin.
7 He told him, "Go, wash in the pool of Siloam" (meaning Sent). So the man went, washed, and returned able to see. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
8 Neighbors and those who'd seen him begging before said, "Isn't this the one who used to sit and beg?" Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?”
9 Some said, "That's him." Others said, "No, he just looks like him." He kept saying, "I'm the one." Waɗansu suka ce shi mana. Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.” Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.”
10 So they asked him, "Then how were your eyes opened?" Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?”
11 He replied, "The man called Jesus made mud, smeared it on my eyes, and told me, 'Go to Siloam and wash.' So I went, washed, and could see." Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”
12 They said to him, "Where is he?" He said, "I do not know." Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
13 They brought the man who had been blind to the Pharisees. Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa.
14 Now it was a Sabbath day when Jesus made the mud and opened his eyes. To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce.
15 So the Pharisees also asked him again how he had gained sight. He told them, "He put mud on my eyes, and I washed, and I see." Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.”
16 Some Pharisees said, "This man isn't from God—he doesn't keep the Sabbath." Others said, "How can a sinful man do such signs?" So they were divided among them. Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban.
17 Again they asked the blind man, "What do you say about him, since he opened your eyes?" He said, "He is a prophet." A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”
18 The Jews did not believe he had been blind and gained sight, until they summoned the parents of the man who had gained sight. Yahudawa dai ba su yarda cewa dā shi makaho ne ya kuma sami ganin gari ba, sai da suka kira iyayen mutumin.
19 They asked them, "Is this your son you say was born blind? How then does he now see?" Suka tambaye su, “Wannan ɗanku ne? Shi ne wanda kuka ce an haife shi makaho? To, ta yaya yake gani yanzu?”
20 His parents answered, "We know that this is our son and that he was born blind. Iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san shi ɗanmu ne, mun kuma san cewa an haife shi makaho.
21 But how he now sees, we don't know; or who opened his eyes, we don't know. Ask him—he's an adult; he'll speak for himself." Sai dai yadda yake gani yanzu, ko kuma wa ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi. Ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”
22 His parents said this, fearing the Jews, since the Jews had already agreed that if anyone confessed Jesus as the Christ, he would be expelled from the synagogue. Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore shi daga majami’a.
23 That was why his parents said, "He is of age; ask him." Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24 So they called the once-blind man again and said, "Give God the glory. We know this man is a sinner." Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”
25 He replied, "Whether he's a sinner, I don't know. I know one thing: I was blind, now I see." Sai ya amsa ya ce, “Ko shi mai zunubi ne ko babu, ni dai ban sani ba. Abu ɗaya fa na sani, dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani!”
26 They said to him, "What did he do to you? How did he open your eyes?" Sai suka tambaye suka ce, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?”
27 He answered them, "I already told you, and you didn't listen. Why do you want to hear it again? Do you also want to become his disciples?" Ya amsa ya ce, “Na riga na gaya muku ba ku kuwa saurara ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”
28 And they reviled him, saying, "You are his disciple, but we are disciples of Moses. Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne!
29 We know God spoke to Moses, but we don't know where this man is from." Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.”
30 The man answered them, "Here's the amazing thing: you don't know where he's from, yet he opened my eyes. Sai mutumin ya ce, “Cabɗi, yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe idanuna.
31 We know God doesn't listen to sinners, but if anyone reveres God and does his will, God listens to him. Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.
32 Never since the world began has anyone heard of someone opening the eyes of a person born blind. Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho.
33 If this man were not from God, he could do nothing." Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.”
34 They answered him, "You were born entirely in sin, yet you teach us?" and threw him out. Sai suka amsa suka ce, “Kai da aka haifa cike da zunubi; za ka yi karambanin koyarwar da mu!” Sai suka kore shi.
35 Jesus heard they had thrown him out, and finding him, said, "Do you believe in the Son of Man?" Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?”
36 He answered, "And who is he, sir, so I can believe in him?" Sai mutumin ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.”
37 Jesus said to him, "You have seen him, and it is he who is speaking with you." Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.”
38 He said, "Lord, I believe," and he worshiped him. Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada.
39 Jesus said, "I came into this world for judgment, so those who don't see may see, and those who see may become blind." Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”
40 Some Pharisees with him heard this and said, "Are we blind too?" Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?”
41 Jesus told them, "If you were blind, you would have no sin; but since you say, 'We see,' your sin remains." Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]