Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 8 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 But Jesus went to the Mount of Olives. Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun.
2 At dawn he came again to the temple; all the people came to him, and he sat down and taught them. Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yă koya musu.
3 The scribes and Pharisees brought a woman caught in adultery and stood her in the middle. Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron
4 They said to him, "Teacher, this woman was caught in the act of adultery. suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina.
5 Now in the Law, Moses commanded us to stone such women. So what do you say? A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?”
6 They said this to test him, seeking grounds to accuse him. But Jesus bent down and wrote on the ground with his finger." Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi. Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa.
7 When they kept questioning him, he stood up and said to them, "Whichever of you has no sin, cast the first stone at her." Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.”
8 And once more he bent down and wrote on the ground. Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
9 Hearing this, they left one by one, starting with the oldest, until Jesus was left alone with the woman standing there. Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin.
10 Jesus stood up and said to her, "Woman, where are they? Has no one condemned you?" Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11 She said, "No one, Lord." Jesus said, "I don't condemn you either. Go, and from now on, don't sin anymore." Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.” Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”
12 Jesus spoke to them again: "I am the world's light. Whoever follows me will never walk in darkness but will have the light of life." Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”
13 So the Pharisees said to him, "You are bearing witness about yourself; your testimony is not true." Sai Farisiyawa suka tambaye shi suka ce, “Ga kai dai, kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”
14 Jesus replied, "Even if I testify about myself, my testimony is true, because I know where I came from and where I'm going; but you don't know where I come from or where I'm going. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba.
15 You judge according to the flesh; I judge no one. Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a.
16 Even if I judge, my judgment is true, since I do not judge alone, but I and the Father who sent me. Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni.
17 In your Law it is written that the testimony of two people is true. A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.
18 I testify about myself, and the Father who sent me testifies about me." Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
19 They asked, "Where is your Father?" Jesus answered, "You know neither me nor my Father. If you knew me, you would know my Father also." Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?” Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.”
20 He said this while teaching in the temple, in the treasury; no one seized him—his hour had not yet come. Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
21 So he told them again, "I am going away. You will look for me and die in your sin. Where I am going, you cannot come." Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”
22 So the Jews said, "Will he kill himself, since he says, "You can't come where I'm going"?" Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?”
23 He said to them, "You're from below; I'm from above. You're of this world; I'm not of this world. Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne.
24 I told you that you'll die in your sins; if you don't believe I AM, you'll die in your sins." Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”
25 So they said to him, "Just who are you?" Jesus said to them, "Exactly what I've said from the start. Suka ce, “Wane ne kai?” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku.
26 I have much to say and judge about you, but the One who sent me is true; what I heard from him, I tell the world." Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shari’a. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.”
27 They did not understand that he had been speaking to them about the Father. Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne.
28 So Jesus told them, "When you lift up the Son of Man, then you'll know that I AM, and that I do nothing on my own, but say these things as the Father taught me. Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.
29 The one who sent me is with me; he hasn't left me alone, because I always do what pleases him." Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”
30 As he was saying these things, many believed in him. Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.
31 Jesus then told the Jews who had believed him, "If you remain in my word, you are truly my disciples, Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.
32 and you will know the truth, and the truth will set you free." Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
33 They answered him, "We are Abraham's descendants, never enslaved to anyone. How can you say, 'You will become free'?" Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”
34 Jesus answered them, "Truly, truly, I tell you: everyone who keeps sinning is sin's slave. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.
35 The slave does not remain in the house forever; the son remains forever. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.
36 So if the Son sets you free, you will be free indeed. Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske.
37 I know you are Abraham's descendants; yet you seek to kill me because my word has no space in you. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku.
38 I speak what I've seen with my Father, and you do what you heard from your father." Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”
39 They answered, "Abraham is our father." Jesus said, "If you were Abraham's children, you'd do the works Abraham did, Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi.
40 but now you want to kill me—a man who told you the truth I heard from my Father. Abraham didn't do this. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba.
41 You do your father's works." They said to him, "We weren't born of sexual sin. We have one Father—God himself." Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.” Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”
42 Jesus said to them, "If God were your Father, you'd love me, for I came from God and am here. I didn't come on my own—he sent me. Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.
43 Why don't you understand my speech? Because you cannot bear to hear my word. Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi.
44 You belong to your father, the devil, and want to carry out his desires. He was a murderer from the beginning, not standing in truth, since no truth is in him. When he lies, he speaks from his own nature, since he's a liar and the lie's father. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
45 But because I tell the truth, you do not believe me. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!
46 Who among you convicts me of sin? If I speak truth, why don't you believe me? Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni?
47 Whoever is from our Father hears his words; you don't hear because you're not from our Father." Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
48 The Jews replied, "Aren't we right in saying that you are a Samaritan and have a demon?" Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Aha, ai, gaskiyarmu da muka ce kai mutumin Samariya ne, kana kuma da aljani.”
49 Jesus answered, "I do not have a demon, but I honor my Father, and you dishonor me. Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni.
50 But I'm not seeking my own glory; our Father seeks it, and he judges. Ba na nema wa kaina ɗaukaka, amma akwai wani wanda yake neman mini, shi ne kuma alƙali.
51 Truly, truly, I say to you, if anyone keeps my word, he will never see death." Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”
52 The Jews said to him, "Now we know you have a demon. Abraham died, as did the prophets, yet you say, 'Whoever keeps my word will never taste death.' Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.
53 Are you greater than our father Abraham, who died? The prophets died too! Who do you claim to be?" Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”
54 Jesus answered, "If I glorify myself, my glory is nothing. It is my Father who glorifies me, of whom you say, 'He is our God.' Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.
55 You don't know him, but I know him. If I said I didn't know him, I'd be a liar like you. But I know him and keep his word. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa.
56 Your father Abraham rejoiced that he would see my day. He saw it and was glad." Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”
57 So the Jews said to him, "You're not yet fifty years old, and you've seen Abraham?" Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”
58 Jesus said to them, "Truly, truly, I say to you, before Abraham was, I AM." Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!”
59 So they grabbed stones to throw at him, but Jesus hid himself and slipped out of the temple. Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]