Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After this, Jesus traveled around Galilee, not wanting to go into Judea because Jewish leaders there were looking for a chance to kill him. Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi.
2 But the Jewish Festival of Booths was near. Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa,
3 His brothers told him, "Leave here and go to Judea, so your disciples can also see the works you do. sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi.
4 No one seeking public attention hides what he does. If you're doing these things, show yourself to the world." Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.”
5 For not even his brothers believed in him. Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.
6 So Jesus told them, "My time has not yet come, but for you any time is right. Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne.
7 "The world cannot hate you, but it hates me, because I testify that its works are evil. Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne.
8 You yourselves go up to the festival; I'm not going up to this festival, since my time hasn't yet fully come." Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.”
9 After saying this, he stayed in Galilee. Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.
10 After his brothers went up to the festival, he too went up—not openly, but secretly. Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye.
11 So the Jewish leaders were looking for him at the festival and asking, "Where is he?" A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”
12 Much murmuring about him spread among the crowds: some said, "He's good," others, "No, he misleads the crowd." A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.”
13 Yet no one spoke about him openly, for fear of the Jewish leaders. Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.
14 About the middle of the festival, Jesus went up into the temple and began to teach. Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa.
15 The Jewish leaders were amazed and asked, "How does this man know so much without training?" Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”
16 Jesus answered them, "My teaching isn't mine—it's from the one who sent me. Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.
17 Whoever wants to do our Father's will knows if my teaching is from my Father or I speak on my own. Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.
18 Whoever speaks on his own seeks his own glory, but whoever seeks the sender's glory is true, with no falsehood in him. Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.
19 Didn't Moses give you the law? Yet none of you obeys the law. Why are you trying to kill me?" Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”
20 The crowd answered, "You have a demon! Who is trying to kill you?" Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”
21 Jesus replied, "I did one work, and you are all amazed. Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki.
22 "Moses gave you circumcision—not from Moses, but the patriarchs—and you circumcise a man on the Sabbath. Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci.
23 If a man is circumcised on the Sabbath so the law of Moses isn't broken, why are you angry at me for making a whole man well on the Sabbath? To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci?
24 Stop judging by appearances, and judge with right judgment." Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”
25 Then some Jerusalemites said, "Isn't this the man they want to kill? A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba?
26 Yet he speaks openly, and they say nothing to him. Can the rulers truly know this is the Christ? Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi?
27 But we know this man's origin. When the Christ comes, no one will know his origin." Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Then Jesus, teaching in the temple, cried out: "You know me, and know where I'm from. Yet I didn't come on my own—the one who sent me is true, and you don't know him. Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba,
29 I know him, because I am from him, and he sent me." amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.”
30 So they tried to grab him, but no one touched him, because his hour had not yet come. Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
31 But many in the crowd believed in him, asking, "When the Christ comes, will he do more signs than this man did?" Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”
32 The Pharisees heard the crowd murmuring these things about him, so the chief priests and Pharisees sent temple guards to seize him. Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.
33 So Jesus said, "I'm with you a little while longer, and then I go to the one who sent me. Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.
34 You will search for me and not find me; you cannot come where I am." Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”
35 So the Jewish leaders asked each other, "Where does he intend to go that we won't find him? Does he intend to go to our people dispersed among the Greeks and teach the Greeks? Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne?
36 What does he mean: 'You will look for me, but you will not find me,' and 'Where I am, you cannot come'?" Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,’ da kuma ‘Inda nake, ba za ku iya zuwa ba’?”
37 On the last, great day of the festival, Jesus stood and called out, "Whoever is thirsty, let him come to me and drink. A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha.
38 Whoever believes in me, as Scripture said, rivers of living water will flow from his heart." Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.”
39 He said this about the Holy Spirit, whom believers in him were to receive; the Spirit had not yet been given, since Jesus had not yet been glorified. Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
40 When they heard these words, some of the crowd said, "This really is the Prophet." Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
41 Others said, "This is the Christ." But others asked, "How can the Christ come from Galilee? Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.” Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili?
42 Doesn't Scripture say the Christ comes from David's line and from Bethlehem, David's village?" Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?”
43 So the crowd was divided over him. Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.
44 Some of them wanted to seize him, but no one laid a hand on him. Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.
45 So the temple guards returned to the chief priests and Pharisees, who asked, "Why didn't you bring him?" A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
46 The guards answered, "No one ever spoke the way this man does." Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
47 "Have you also been deceived?" the Pharisees answered. Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan?
48 "Has any of the rulers or of the Pharisees believed in him? Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi?
49 But this crowd, who knows nothing of the law—they are under a curse." A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
50 Nicodemus, who had gone to Jesus earlier and was one of their own number, asked them, Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce,
51 "Does our law condemn a man without first hearing him and finding out what he does?" “Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”
52 They replied, "Are you from Galilee too? Search, and see: no prophet arises from Galilee." Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”
53 Then they all went home. Sai kowannensu ya koma gidansa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]