1After this, Jesus crossed the Sea of Galilee, also called the Sea of Tiberias.OHCBƊan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),
2A large crowd followed him, because they saw the signs he performed on the sick.OHCBsai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
3Jesus went up on the mountainside and sat down there with his disciples.OHCBSa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.
4Now the Passover, the feast of the Jews, was near.OHCBBikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
5Looking up, Jesus saw a large crowd approaching and asked Philip, "Where can we buy bread for these people to eat?"OHCBSa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”
6He said this to test Philip, for he himself already knew what he was going to do.OHCBYa yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
7Philip answered him, "200 days' wages of bread isn't enough for each of them to get a little."OHCBSai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
8One of his disciples, Andrew, Simon Peter's brother, said to him,OHCBSai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,
9"A boy here has five barley loaves and two fish—but what's that for so many?"OHCB“Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”
10Jesus said, "Have the people sit down." Much grass grew there, so about 5,000 men sat down.OHCBYesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
11Jesus then took the loaves, gave thanks, and distributed them to those seated; likewise with the fish, as much as they wanted.OHCBSa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
12When they were full, he told his disciples, "Gather the leftover pieces, so nothing is lost."OHCBSa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”
13So they gathered the fragments left over from the five barley loaves after the people ate, filling twelve baskets.OHCBSaboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
14So when the people saw the sign he did, they said, "This really is the Prophet coming into the world!"OHCBBayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”
15Knowing they meant to come and seize him to make him king, Jesus withdrew again to the mountain alone.OHCBDa Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
16When evening came, his disciples went down to the sea,OHCBDa yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,
17got in a boat and headed across the sea to Capernaum. It was already dark, and Jesus had not yet reached them.OHCBinda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.
18A strong wind was blowing, and the sea grew rough.OHCBIska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
19After rowing three or four miles, they saw Jesus walking on the water, approaching the boat, and were afraid.OHCBBayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.
20But he said to them, "It is I; do not be afraid."OHCBAmma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”
21So they were glad to take him into the boat, and instantly it reached the shore they were heading toward.OHCBSa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
22The next day, the crowd remaining on the far shore saw that only one boat had been there, that Jesus had not boarded it with his disciples, but that his disciples had gone off alone.OHCBKashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.
23Other boats came from Tiberias near the place where they ate bread after the Lord gave thanks.OHCBSai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.
24So when the crowd saw Jesus and his disciples weren't there, they got in boats and went to Capernaum to look for Jesus.OHCBDa taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25Finding him across the sea, they asked, "Rabbi, when did you get here?"OHCBDa suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”
26Jesus answered them, "Truly, truly, I tell you: you seek me not because you saw signs, but because you ate the loaves and were filled.OHCBYesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.
27Don't work for food that spoils, but for food that lasts to eternal life, which the Son of Man will give you. For on him our Father has set his seal."OHCBKada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”
28Then they said to him, "What must we do to be doing the works of our Father?"OHCBSai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
29Jesus answered them, "This is our Father's work: that you believe in the one he sent."OHCBYesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”
30So they asked him, "What sign will you give, so we may see and believe you? What work will you do?OHCBSai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi?
31Our ancestors ate manna in the wilderness, as it is written: 'He gave them bread from heaven to eat.'"OHCBKakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’”
32Jesus told them, "Truly, truly, I tell you: Moses didn't give you the bread from heaven—my Father gives you the true bread from heaven.OHCBYesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.
33For the bread of our Father is he who comes down from heaven and gives the world life."OHCBGama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
34So they said to him, "Lord, give us this bread always."OHCBSai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”
35Jesus told them, "I am the bread of life. Whoever comes to me will never hunger; whoever believes in me will never thirst.OHCBSa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
36But as I told you, you have seen me and still do not believe.OHCBAmma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.
37All the Father gives me will come to me, and the one who comes to me I will never drive away.OHCBDuk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.
38For I came down from heaven not to do my own will, but the will of him who sent me.OHCBGama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.
39This is the will of him who sent me: that I lose none of all he has given me, but raise them up on the last day.OHCBNufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
40For this is the will of my Father: that everyone who looks to the Son and believes in him should have eternal life, and I will raise them up on the last day."OHCBGama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”
41So the Jews grumbled about him because he said, "I am the bread that came down from heaven."OHCBDa jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”
42They said, "Isn't this Jesus, Joseph's son, whose father and mother we know? How can he now say, 'I have come down from heaven'?"OHCBSuka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”
43Jesus answered them, "Stop grumbling among yourselves.OHCBSai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.
44"No one can come to me unless the Father who sent me draws him, and I will raise him on the last day.OHCBBa mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
45It is written in the Prophets: 'And they will all be taught by our Father.' Everyone who has heard and learned from the Father comes to me.OHCBA rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.
46Not that anyone has seen the Father except the one from him; he has seen the Father.OHCBBa wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
47Truly, truly, I tell you, whoever believes has eternal life.OHCBGaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.
48I am the bread of life.OHCBNi ne burodin rai.
49Your ancestors ate the manna in the wilderness, yet they died.OHCBKakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.
50This is the bread that comes down from heaven, so anyone may eat it and not die.OHCBAmma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.
51I am the living bread come down from heaven. Whoever eats this bread will live forever. The bread I will give is my flesh, for the life of the world."OHCBNi ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”
52Then the Jews argued sharply among themselves, "How can this man give us his flesh to eat?"OHCBSai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
53Jesus told them, "Truly, truly, I tell you, unless you eat the flesh of the Son of Man and drink his blood, you have no life in yourselves.OHCBSai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.
54Whoever feeds on my flesh and drinks my blood has eternal life, and I will raise him on the last day.OHCBDuk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
55For my flesh is true food, and my blood is true drink.OHCBGama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56Whoever feeds on my flesh and drinks my blood remains in me, and I in him.OHCBDuk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.
57As the living Father sent me and I live because of the Father, so whoever feeds on me will live because of me.OHCBKamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.
58This is the bread that came down from heaven. It is not like the bread your ancestors ate and still died. Whoever feeds on this bread will live forever."OHCBWannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.”
59He said these things while teaching in the synagogue at Capernaum.OHCBYa faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum.
60On hearing it, many of his disciples said, "This is a hard teaching. Who can accept it?"OHCBDa jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”
61Aware that his disciples were grumbling about this, Jesus said to them, "Does this offend you?OHCBDa yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?
62"Then what if you see the Son of Man ascending to where he was before?OHCBMe za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!
63The Spirit gives life; the flesh helps nothing. The words I have spoken to you are spirit and life.OHCBRuhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.
64But some of you don't believe." For Jesus knew from the start who didn't believe, and who would betray him.OHCBDuk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65And he said, "This is why I told you: no one can come to me unless the Father enables him."OHCBYa ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
66From this time many of his disciples turned back and no longer walked with him.OHCBDaga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
67So Jesus asked the Twelve, "Do you want to leave too?"OHCBSai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
68Simon Peter answered him, "Lord, to whom should we go? You have the words of eternal life.OHCBSai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.
69We have believed and known you are the Holy One of our Father."OHCBMun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
70Jesus answered them, "Have I not chosen you, the Twelve? Yet one of you is a devil."OHCBSai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”
71He meant Judas, son of Simon Iscariot, one of the Twelve, who was about to betray him.OHCB(Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)