Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 After this there was a feast of the Jews, and Jesus went up to Jerusalem. Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.
2 By the Sheep Gate in Jerusalem is a pool with five covered porches, called Bethesda in Aramaic. To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar.
3 In these lay a multitude of the sick—blind, lame, and paralyzed. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.
5 One man was there who had been sick for thirty-eight years. Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas.
6 Seeing him lying there and knowing he had already been there a long time, Jesus asked, "Do you want to be healed?" Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”
7 The sick man answered him, "Sir, I have no one to put me in the pool once the water stirs—while I'm on my way, someone else gets in first." Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”
8 Jesus said to him, "Get up, take up your mat, and walk." Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.”
9 At once the man became well, picked up his mat, and walked. That day was the Sabbath. Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya. A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,
10 So the Jews told the healed man, "It's the Sabbath—you're not allowed to carry your mat." saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.”
11 He answered them, "The man who healed me told me, 'Take up your mat and walk.'" Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ”
12 They asked him, "Who is the man who told you, 'Take it up and walk'?" Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
13 But the healed man didn't know who it was, since Jesus had slipped away into the crowd there. Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
14 Later Jesus found him in the temple and said, "You are healed now. Stop sinning, or something worse may happen to you." Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”
15 The man went away and told the Jews that it was Jesus who had made him well. Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16 And so the Jews began persecuting Jesus, because he was doing these things on the Sabbath. To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.
17 But Jesus answered them, "My Father is working until now, and I too am working." Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”
18 So the Jews sought even more to kill him: he not only broke the Sabbath but called our Father his own Father, making himself equal to him. Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
19 So Jesus said to them, "Truly, truly, I tell you: the Son can do nothing on his own, but only what he sees the Father doing. Whatever the Father does, the Son does the same. Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.
20 "For the Father loves the Son and shows him everything he does; he will show him greater works than these, so you will be amazed. Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma.
21 For as the Father raises the dead and gives life, so the Son too gives life to anyone he wants. Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama.
22 For the Father judges no one, but has entrusted all judgment to the Son, Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan,
23 so everyone honors the Son as they honor the Father; whoever doesn't honor the Son doesn't honor the Father who sent him. don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
24 Truly, truly, I tell you: whoever hears my word and believes the one who sent me has eternal life and won't face judgment—they have passed from death to life. “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.
25 Truly, truly, I tell you, an hour comes, and is now here, when the dead will hear the voice of the Son of our Father, and those hearing will live. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.
26 For as the Father has life in himself, he gave the Son to also have life in himself. Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa.
27 And he has given him authority to execute judgment, because he is the Son of Man. Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
28 Don't be astonished at this—an hour is coming when everyone in the tombs will hear his voice, “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa
29 and come out—those who did good, to the resurrection of life; those who did evil, to the resurrection of judgment. su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.
30 By myself I can do nothing. I judge as I hear; my judgment is fair, because I seek not my own will but the will of the One who sent me. Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
31 "If I testify about myself, my testimony is not valid. “In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce.
32 There is another who testifies about me, and I know his testimony about me is true. Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce.
33 You sent messengers to John, and he has testified to the truth. “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya.
34 Not that I accept human testimony, but I say these things so that you may be saved. Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto.
35 John was a burning, shining lamp, and you were willing to rejoice briefly in his light. Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
36 But I have testimony greater than John's: the works my Father gave me to finish—the very works I'm doing—testify that my Father sent me. “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni.
37 And my Father who sent me has himself testified about me. You've never heard his voice or seen his form, Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba,
38 and you don't have his word remaining in you, since you don't believe the one he sent. maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
39 You search the Scriptures, thinking they hold eternal life—yet they themselves testify about me, Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina,
40 yet you refuse to come to me so that you may have life. duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
41 I do not accept glory from people, “Ni ba na neman yabon mutane,
42 but I know you—that you do not have the love of our Father within you. na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.
43 I have come in my Father's name, and you don't receive me; if another comes in his own name, you'll receive him. Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.
44 How can you believe, when you accept glory from one another and don't seek the glory from the only God? Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
45 Don't think I will accuse you before my Father. Moses, in whom you've hoped, accuses you. “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.
46 For if you believed Moses, you would believe me, because he wrote about me. Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.
47 But if you do not believe his writings, how will you believe my words?" Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]