Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 So when Jesus knew the Pharisees heard he was making and baptizing more disciples than John. Yesu ya ji labari cewa Yahudawa sun ji cewa ya wuce Yohanna samun masu bi, yana kuma yin musu baftisma,
2 (though Jesus himself was not baptizing, but his disciples were), ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, almajiransa ne.
3 he left Judea and went back to Galilee. Da ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili.
4 And he had to pass through Samaria. To, ya zama dole yă bi ta Samariya.
5 So he came to a town of Samaria called Sychar, near the field Jacob gave his son Joseph. Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf.
6 Jacob's well was there. Jesus, tired from the trip, sat down at the well—about noon. Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.
7 A woman of Samaria came to draw water. Jesus said to her, "Give me a drink." Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?”
8 (For his disciples had gone into the town to buy food.). (Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.)
9 The Samaritan woman said, "You're a Jew; why ask me, a Samaritan woman, for a drink?" (Jews don't associate with Samaritans.). Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.)
10 Jesus answered her, "If you knew our Father's gift, and who asks you, 'Give me a drink,' you'd have asked him, and he'd have given you living water." Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”
11 The woman said to him, "Sir, you have nothing to draw with, and the well is deep. Where then do you get this living water? Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai?
12 Are you greater than our father Jacob, who gave us the well, drank from it himself, with his sons and livestock?" Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ’ya’yansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?”
13 Jesus said to her, "Everyone who drinks of this water will be thirsty again, Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa,
14 but whoever drinks the water I give him will never thirst again; that water will become in him a spring of water welling up to eternal life." amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”
15 The woman said to him, "Sir, give me this water, so I won't get thirsty or come here to draw water." Sai macen ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.”
16 Jesus said to her, "Go, call your husband, and come back here." Sai ya ce mata, “Je ki zo da mijinki.”
17 The woman answered, "I have no husband." Jesus told her, "You're right to say you have no husband. Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji.
18 For you've had five husbands, and the man you have now isn't your husband. You've spoken the truth." Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.”
19 The woman said to him, "Sir, I see that you are a prophet. Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne.
20 Our fathers worshiped on this mountain, but you say Jerusalem is where people must worship." Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.”
21 Jesus told her, "Woman, believe me: an hour is coming when you'll worship the Father neither on this mountain nor in Jerusalem. Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba.
22 You worship what you don't know; we worship what we know—salvation comes from the Jews. Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.
23 But a time is coming, and now is, when true worshipers worship the Father in spirit and truth—for the Father seeks such worshipers. Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
24 The Father is spirit, and those who worship him must worship in spirit and truth." Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
25 The woman said to him, "I know Messiah—the one called Christ—is coming. When he comes, he will tell us everything." Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”
26 Jesus said to her, "I am he—the one speaking to you." Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”
27 Just then his disciples returned, amazed he was talking with a woman. Yet no one said, "What do you want?" or, "Why talk with her?" Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”
28 So the woman left her water jar and went back to town and said to the people, Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane,
29 "Come, see a man who told me everything I ever did. Could this be the Christ?" “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?”
30 They left the town and were coming to him. Sai suka fita daga garin suka nufa inda yake.
31 Meanwhile the disciples were urging him, "Rabbi, eat." Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci abinci mana.”
32 But he said to them, "I have food to eat that you know nothing about." Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.”
33 So the disciples said to one another, "Has anyone brought him something to eat?" Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”
34 Jesus said to them, "My food is doing the will of the one who sent me and finishing his work. Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.
35 Don't you say, 'Four months more, then harvest comes'? Look, I tell you: raise your eyes, see the fields—white for harvest. Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi.
36 Already the harvester earns wages, gathering fruit for eternal life, so that planter and harvester may rejoice together. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.
37 For here the saying holds true: 'One plants and another harvests.' Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’
38 I sent you to reap what you didn't work for. Others worked, and you have entered into their labor." Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”
39 Many Samaritans from that town believed in him because of the woman's testimony: "He told me everything I ever did." Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”
40 When the Samaritans came to him, they asked him to stay with them; he stayed two days. To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu.
41 And many more believed because of his word. Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.
42 They told the woman, "It is no longer because of what you said that we believe—we've heard for ourselves, and we know this man truly is the Savior of the world." Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”
43 After the two days he departed from there for Galilee. Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili.
44 (For Jesus himself had testified that a prophet has no honor in his own hometown.). (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.)
45 When he arrived in Galilee, the Galileans welcomed him, having seen all he did in Jerusalem at the feast—they too had gone to the feast. Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can.
46 He went again to Cana in Galilee, where he had turned water to wine. A royal official's son was sick at Capernaum. Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum.
47 Hearing that Jesus had come from Judea to Galilee, he went to him and begged him to come down and heal his son, who was about to die. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.
48 So Jesus said to him, "Unless you people see signs and wonders, you will never believe." Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”
49 The royal official said to him, "Sir, come down before my child dies." Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.”
50 Jesus said to him, "Go; your son will live." The man believed what Jesus told him and left. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.
51 As he was going down, his servants met him and told him that his boy was living. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa.
52 So he asked them the hour he improved, and they said, "Yesterday at the seventh hour, the fever left him." Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.”
53 So the father knew this was the hour when Jesus told him, "Your son will live." He and his whole household believed. Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.
54 This was now the second sign that Jesus did when he had come from Judea to Galilee. Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]