Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 10 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 "Truly, truly, I tell you: whoever doesn't enter the sheepfold through the gate, but climbs in another way, is a thief and a robber. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.
2 But the one who enters by the gate is the shepherd of the sheep. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.
3 The gatekeeper opens for him, and the sheep hear his voice. He calls his own sheep by name and leads them out. Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje.
4 After bringing all his own out, he goes ahead of them, and the sheep follow him because they know his voice. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.
5 They will never follow a stranger—they'll run from him, since they don't know the voice of strangers." Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”
6 Jesus told them this figure of speech, but they didn't grasp what he meant. Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.
7 So Jesus said again, "Truly, truly, I tell you, I am the gate for the sheep. Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.
8 "All who came before me are thieves and robbers, but the sheep did not listen to them. Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba.
9 I am the gate; whoever enters through me will be saved, going in and out, finding pasture. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo.
10 The thief comes only to steal, kill, and destroy. I came so they may have life, and have it in abundance. Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
11 "I am the good shepherd. The good shepherd lays down his life for the sheep. “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.
12 The hired hand, not a shepherd, doesn't own the sheep. Seeing the wolf coming, he leaves the sheep and flees—the wolf snatches and scatters them. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.
13 The man runs away because he is a hired hand and cares nothing for the sheep. Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.
14 "I am the good shepherd. I know my own and my own know me, “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni,
15 as the Father knows me and I know the Father, and I lay down my life for the sheep. kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.
16 I have other sheep not of this fold; I must lead them too, and they will hear my voice. They will become one flock, one shepherd. Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.
17 This is why the Father loves me: I lay down my life only to take it up again. Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.
18 No one takes it from me, but I lay it down on my own. I have authority to lay it down, and authority to take it up again. This charge I received from my Father." Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”
19 These words brought division among the Jews once again. Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa.
20 Many of them said, "He is demon-possessed and out of his mind. Why listen to him?" Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”
21 But others said, "These aren't a demon-possessed man's words. Can a demon open blind eyes?" Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”
22 Then came the Feast of Dedication at Jerusalem. It was winter, Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa.
23 and Jesus was walking in the temple, in Solomon's Colonnade. Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon,
24 The Jews surrounded him and said, "How long will you hold us in suspense? If you are the Christ, tell us plainly." sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”
25 Jesus answered, "I told you, and you don't believe. The works I do in my Father's name testify about me, Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.
26 but you do not believe, because you are not my sheep. Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
27 My sheep listen to my voice; I know them, and they follow me. Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.
28 I give them eternal life, and they will never perish, and no one will snatch them from my hand. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
29 My Father, who gave them to me, is greater than all; no one can snatch them out of the Father's hand. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.
30 I and the Father are one." Da ni da Uba ɗaya ne.”
31 Again the Jews picked up stones to stone him. Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi,
32 Jesus replied, "I have shown you many good works from the Father. For which of these are you going to stone me?" amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”
33 "We're stoning you not for good work," they said, "but for blasphemy, because you, a mere man, claim to be God." Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”
34 Jesus answered them, "Is it not written in your Law: 'I have said you are gods'? Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’ ?
35 If he called them 'gods,' to whom the word of my Father came—and Scripture cannot be broken, Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’
36 what about the one the Father set apart and sent into the world? Why accuse me of blasphemy for saying, 'I am the Son of our Father'? to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’
37 "If I am not doing the works of my Father, then do not believe me. In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.
38 But if I do them, even if you won't believe me, believe the works, so you'll know and keep knowing the Father is in me, and I in the Father." Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.”
39 Again they tried to seize him, but he escaped their grasp. Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.
40 Jesus then went back across the Jordan, to the place where John had first been baptizing, and stayed there. Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna
41 Many came to him, saying, "John performed no sign, but all John said about this man was true." mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”
42 And in that place many believed in him. A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]