Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 11 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 A man named Lazarus was sick, from Bethany, the village of Mary and her sister Martha. To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta.
2 Mary—whose brother Lazarus was sick—anointed the Lord with fragrant oil and dried his feet with her hair. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta.
3 So the sisters sent word to him, saying, "Lord, the one you love is sick." Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
4 Hearing this, Jesus said, "This sickness won't end in death, but is for the glory of our Father, so the Son of our Father may be glorified through it." Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.”
5 Now Jesus loved Martha and her sister and Lazarus. Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus.
6 So when he heard Lazarus was sick, he stayed two more days where he was. Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
7 Then after this he said to the disciples, "Let us go back to Judea." Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.”
8 The disciples said to him, "Rabbi, the Jews just now tried to stone you, and you're going back there?" Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
9 Jesus answered, "Aren't there twelve hours in the day? Anyone who walks by day won't stumble - he sees the light of this world. Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan.
10 But if anyone walks at night, he stumbles, because the light is not in him." Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”
11 After this, he told them, "Our friend Lazarus has fallen asleep, but I'm going to wake him." Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
12 So the disciples said to him, "Lord, if he has fallen asleep, he will get better." Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.”
13 Now Jesus had been speaking about his death, but they thought he meant natural sleep. Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
14 So then Jesus told them plainly, "Lazarus has died, Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu,
15 I'm glad for your sake I wasn't there, so you'll believe. But let's go to him." amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.”
16 So Thomas, called the Twin, told the other disciples, "Let's go too, and die with him." Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
17 So when Jesus arrived, he found that Lazarus had already been in the tomb four days. Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari.
18 Bethany was near Jerusalem, about two miles away, Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima,
19 and many of the Jews had come to Martha and Mary to console them about their brother. Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu.
20 When Martha heard Jesus was coming, she went to meet him; Mary stayed sitting in the house. Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
21 Martha said to Jesus, "Lord, if you had been here, my brother would not have died. Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.
22 But even now I know that whatever you ask of our Father, he will give you." Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
23 Jesus said to her, "Your brother will rise again." Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.”
24 Martha said to him, "I know he'll rise again in the resurrection on the last day." Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
25 Jesus told her, "I am the resurrection and the life. Whoever believes in me will live, even though he dies, Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;
26 and everyone who lives and believes in me will never die. Do you believe this?" kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”
27 She said to him, "Yes, Lord; I believe you are the Christ, the Son of our Father, the one coming into the world." Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
28 After saying this, she went and called her sister Mary privately: "The Teacher is here—he's calling for you." Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.”
29 When Mary heard this, she rose quickly and went to him. Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa.
30 Jesus had not yet entered the village; he was still where Martha met him. Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi.
31 The Jews with her in the house, comforting her, saw Mary rise quickly and leave; they followed, thinking she was going to the tomb to weep there. Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
32 Mary came to Jesus, saw him, fell at his feet, and said, "Lord, if you had been here, my brother would not have died." Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
33 When Jesus saw her weeping, and the Jews who came with her also weeping, he groaned in spirit and was troubled. Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu.
34 And he said, "Where have you laid him?" They said to him, "Lord, come and see." Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
35 Jesus wept. Yesu ya yi kuka.
36 So the Jews said, "See how he loved him!" Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37 But some of them said, "Could this man who opened the blind man's eyes not have kept him from dying?" Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”
38 So Jesus, again deeply moved in himself, came to the tomb—a cave with a stone against it. Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse.
39 Jesus said, "Take away the stone." Martha, the dead man's sister, said to him, "Lord, he must smell by now—he's been dead four days." Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”
40 Jesus said to her, "Didn't I tell you: if you believe you'll see our Father's glory?" Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”
41 So they removed the stone. Jesus looked up and said, "Father, I thank you that you heard me. Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni.
42 I knew you always hear me, but I said this for the crowd standing here, so they may believe you sent me." Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
43 When he had said this, he cried out with a loud voice, "Lazarus, come out!" Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”
44 The dead man came out, feet and hands bound with strips of linen, and his face wrapped in cloth. Jesus said to them, "Untie him; let him go." Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”
45 So many of the Jews who came to Mary and saw what Jesus did believed in him. Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.
46 But some of them went to the Pharisees and told them what Jesus had done. Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
47 So the chief priests and Pharisees convened the council and said, "What are we doing? For this man performs many signs. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
48 If we leave him alone, everyone will believe in him, and the Romans will come and take away both our place and our nation." In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
49 But one of them, Caiaphas, high priest that year, told them, "You know nothing at all. Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!
50 Don't you see it's better for you that one man die for the people than the whole nation perish?" Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
51 He didn't say this on his own; as high priest that year, he prophesied Jesus would die for the nation, Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,
52 not only for the nation, but also to gather into one the scattered children of our Father. ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.
53 So from that day on they plotted to put him to death. Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
54 So Jesus no longer moved about openly among the Jews, but withdrew to a town called Ephraim near the wilderness, and stayed there with his disciples. Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
55 The Jews' Passover was near, and many went up from the country to Jerusalem before it to purify themselves. Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa.
56 So they looked for Jesus, asking each other as they stood in the temple, "What do you think? Surely he won't come to the feast?" Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?”
57 The chief priests and Pharisees had ordered that anyone who knew his whereabouts must report it, so they could arrest him. Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]