Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

James 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Come now, you who are rich, weep and wail over the miseries that are coming upon you. Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku.
2 Your riches have rotted, and your clothes have become moth-eaten. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku.
3 Your gold and silver have rusted; their rust will witness against you and burn your flesh like fire. You piled up riches in the last days. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe.
4 Look: the wages you held back from the workers who mowed your fields cry out, and the harvesters' cries have reached the ears of the Father of heaven's armies. Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.
5 You lived on earth in luxury and indulgence. You fattened your hearts in a day of slaughter. Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka.
6 You have condemned and murdered the righteous one, who does not resist you. Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.
7 So be patient, brothers and sisters, until the Lord's coming. Think of the farmer: he waits patiently for the land's precious fruit, until it gets the early and late rains. Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka.
8 You too must be patient. Strengthen your hearts, because the coming of the Lord is near. Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.
9 Don't grumble against each other, brothers and sisters, or you'll be judged. Look—the Judge stands at the doors. ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa!
10 Brothers and sisters, take the prophets who spoke in the name of our Father as examples of suffering and patience. ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala.
11 See, we call those who endured blessed. You've heard of Job's endurance and seen what our Father brought about—our Father is rich in compassion and mercy. Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
12 Above all, my brothers and sisters, do not swear—neither by heaven, nor earth, nor any other oath. Let your yes be yes and your no, no, so you won't fall under judgment. ’Yan’uwana, fiye da kome, kada ku yi rantsuwa ko da sama, ko da ƙasa ko da wani abu dabam. Bari “I” naku yă zama “I”. “A’a” naku kuma yă zama “A’a”, don kada a hukunta ku.
13 Is anyone among you suffering? Let them pray. Is anyone cheerful? Let them sing praises. Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.
14 Anyone sick among you? Have them call for the church elders, and have the elders pray over them, anointing them with oil in the name of the Lord. Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji.
15 The prayer of faith will save the sick person, and the Lord will raise him up. And if he has sinned, he will be forgiven. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.
16 So confess your sins to each other and pray for each other, that you may be healed. A righteous person's prayer is powerful and effective. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.
17 Elijah was a man like us, and he prayed hard that it not rain; it did not rain on the land for three years and six months. Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.
18 Then he prayed again, and the heavens gave rain, and the earth produced its fruit. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
19 My brothers and sisters, if anyone among you wanders from the truth and someone turns them back, ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi,
20 know this: whoever turns a sinner from their wrong way saves that person's soul from death and covers a multitude of sins. sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]