Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

1 Peter 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Peter, apostle of Jesus Christ, to the chosen exiles scattered through Pontus, Galatia, Cappadocia, Asia, and Bithynia. Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,
2 Chosen by our Father's foreknowledge, made holy by the Holy Spirit, to obey Jesus Christ and be sprinkled with his blood: grace and peace multiplied to you. waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.
3 Blessed is our Father, and the Father of our Lord Jesus Christ: by his great mercy he gave us new birth into a living hope through Jesus Christ's resurrection from the dead, Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,
4 into an inheritance that can never perish, spoil, or fade, kept in heaven for you, da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku,
5 protected through faith by our Father's power for the salvation ready to be revealed in the last time. ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.
6 You rejoice greatly in this, though now, briefly, you may have had to be distressed by various trials. A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri.
7 These have come so that your faith—tested and found genuine, worth more than fire-refined gold that still gets destroyed—may bring praise, glory, and honor when Jesus Christ appears. Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.
8 Though you've never seen him, you love him; though you don't see him now, you trust him, rejoicing with joy beyond words and full of glory, Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,
9 for you are receiving the goal of your faith, the salvation of your souls. gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
10 Prophets who spoke of the grace meant for you investigated and searched carefully into this salvation, Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse,
11 searching for the time and situation the Spirit of Christ in them pointed to, when he predicted Christ's sufferings and the glories after them. suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.
12 It was revealed to them: they served not themselves but you, when they spoke of these things now announced to you through those who preached the good news to you by the Holy Spirit sent from heaven. Even angels long to look into these things. Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.
13 So, minds braced for action and fully sober, hope completely on the grace to be brought to you when Jesus Christ is revealed. Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi.
14 As obedient children, don't let yourselves be shaped by the desires you once followed in your ignorance. Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci.
15 But just as the one who called you is holy, so be holy in all you do; Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi;
16 for it is written: "Be holy, because I am holy." gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
17 Since you call on a Father who judges every deed without favoritism, spend your exile time here in reverent fear. Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.
18 You know silver and gold—things that decay—didn't rescue you from the empty life passed down from your ancestors, Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba,
19 but with Christ's precious blood, a lamb without defect or stain. sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani.
20 Chosen before the world's foundation, revealed in these last times for your sake. An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku.
21 Through him you believe in our Father, who raised him from the dead and glorified him, so your faith and hope are in our Father. Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
22 Having purified your souls by obeying the truth for sincere love of the brothers, love each other deeply from a pure heart. Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.
23 For you have been born again—not of perishable seed but imperishable—through the living, enduring word of our Father. Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah.
24 For, "All people are like grass, and all their glory like the flowers of the field; the grass withers and the flowers fall, Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,
25 but the word of our Father endures forever." And this is the word that was preached to you. amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]