Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 6 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Darius appointed 120 satraps over the kingdom, stationed throughout the whole kingdom, Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar,
2 and three officials over them, one of them Daniel, so the satraps would answer to them and the king lose nothing. ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome.
3 Daniel outshone the administrators and satraps, because an extraordinary spirit was in him, and the king planned to set him over the whole kingdom. To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa.
4 Administrators and satraps sought grounds to charge Daniel over the kingdom, but found none—no corruption—since he was faithful; no negligence or corruption was found in him. A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula.
5 Then these men said, "We'll find no charge against Daniel unless we find one in his God's law." A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”
6 So the administrators and satraps went together to the king and said, "King Darius, live forever! Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe!
7 All the kingdom's administrators, prefects, satraps, counselors, and governors agreed the king should issue a royal statute and firm decree: whoever petitions any god or man but you, king, for thirty days, will be thrown into the lions' den. Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki.
8 Now, king, issue the decree and sign it in writing, unalterable, under the law of the Medes and Persians, which cannot be revoked. Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”
9 So King Darius signed the document and the ordinance." Sai Sarki Dariyus ya ba da umarnin a rubuce.
10 Learning the decree was signed, Daniel went home to his upstairs room, windows open toward Jerusalem, knelt three times daily, and prayed, giving thanks before his Father as always. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.
11 Then these men came together and found Daniel praying and pleading for mercy before his Father. Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi.
12 They approached the king about the decree: "Did you not sign a decree that for thirty days, anyone petitioning any god or man except you, king, would be thrown into the lions' den?" The king answered, "The matter stands, by the law of the Medes and Persians, unchangeable." Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”
13 They told the king, "Daniel, one of Judah's exiles, ignores you, king, and your signed decree—praying three times daily." Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”
14 Hearing this, the king was deeply troubled, determined to save Daniel, and worked until sunset to rescue him. Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi.
15 Then these men gathered before the king and said, "Know, king: by law of the Medes and Persians, no decree or edict the king issues can be changed." Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”
16 Then the king gave the command, and they brought Daniel and threw him into the lions' den. The king said to Daniel, "May your God, whom you serve continually, rescue you." Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!”
17 A stone was brought, placed over the den's mouth, and sealed by the king with his signet ring and his nobles' rings, so nothing about Daniel could change. Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel.
18 Then the king went to his palace and fasted that night; no entertainment was brought before him, and sleep fled from him. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.
19 Then, at the first light of dawn, the king rose and hurried to the den of lions. Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki.
20 Nearing the den, he cried out to Daniel anxiously. The king said to Daniel, "Daniel, servant of the living God, has your God, whom you serve continually, been able to rescue you from the lions?" Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?”
21 Then Daniel said to the king, "King, may you live forever! Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe!
22 My Father sent his angel and shut the lions' mouths. They haven't harmed me, because I was found innocent before him, and before you, king, I've done no wrong." Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.”
23 The king was overjoyed and ordered Daniel lifted from the den. Daniel was lifted out with no injury at all, for he had trusted in his Father. Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.
24 The king ordered the men who had falsely accused Daniel brought and thrown into the lions' den—with their children and wives. Before they reached the bottom, the lions overpowered them and crushed all their bones. Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su.
25 Then King Darius wrote to all peoples, nations, and languages living on earth: "May your peace overflow! Sa’an nan Sarki Dariyus ya rubuta wa dukan mutane, da al’ummai da kuma mutanen dukan harsunan a duk fāɗin ƙasar. “Bari yă yi nasara sosai!
26 I decree: in all my kingdom, people must tremble and fear before Daniel's God—the living God, enduring forever. His kingdom will never be destroyed; his rule never ends. “Na fitar da doka cewa a cikin dukan iyakar ƙasar mulkina, dole mutane su ji tsoro su kuma girmama Allah na Daniyel. “Gama shi ne Allah mai rai kuma madawwami ne har abada; ba za a taɓa lalace masarautarsa ba, mulkinsa kuma ba za tă taɓa ƙarewa ba
27 He rescues and delivers; he works signs and wonders in the heavens and on the earth; he is the one who rescued Daniel from the power of the lions." Yakan kuɓutar ya kuma ceci; yana yin alamu da al’ajabai a sama da kuma a duniya. Shi ya ceci Daniyel daga ikon zakoki.”
28 So this Daniel thrived in the reign of Darius and of Cyrus the Persian. Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus na Farisa.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]