Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 5 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 King Belshazzar held a great feast for 1,000 nobles, drinking wine in the presence of the 1,000. Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su.
2 While tasting the wine, Belshazzar ordered in the gold and silver vessels his father Nebuchadnezzar took from Jerusalem's temple, for the king, his nobles, wives, and concubines to drink from. Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su.
3 Then they brought the gold vessels taken from the temple, our Father's house in Jerusalem; the king, his nobles, wives, and concubines drank from them. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su.
4 They drank the wine and praised the gods of gold, silver, bronze, iron, wood, and stone. Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.
5 Just then a human hand's fingers appeared and wrote on the plaster of the king's palace wall opposite the lampstand, and the king watched the hand writing. Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu.
6 The king's face changed color, his thoughts terrified him, his hips gave way, and his knees knocked. Sai fuskarsa ta ruɗe, ya kuma ji tsoro ƙwarai har gwiwoyinsa suka yi ta bugun juna, ƙafafunsa kuma suka rasa ƙarfi.
7 The king shouted for the enchanters, astrologers, and fortune-tellers, telling Babylon's wise men, "Whoever reads this writing and tells me what it means will wear purple, a gold chain on his neck, and rule third in the kingdom." Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
8 Then all the king's wise men came in, but none could read the writing or tell him its meaning. Sa’an nan sai dukan masu hikima suka zo ciki, amma ba su iya karanta rubutun ba ko su faɗa wa sarki abin da yake nufi.
9 So King Belshazzar grew even more terrified, his face paler still, and his nobles were bewildered. Saboda haka Sarki Belshazar ya firgita ƙwarai kuma fuskarsa ta ƙara ruɗewa. Hakimansa kuma suka rikice.
10 At the king's and his nobles' words, the queen entered the banquet hall, saying, "King, live forever! Don't let your thoughts terrify you or your face turn pale. Sai sarauniya, da jin muryoyi na sarki da na hakimansa, ta shiga babban ɗakin liyafar. Ta ce, “Ya sarki, ranka yă daɗe! Kada ka firgita! Kada fuskarka ta ruɗe!
11 A man in your kingdom has the spirit of the holy gods. In your father's days he showed insight, understanding, and wisdom like the gods' wisdom. King Nebuchadnezzar your father—your father the king—made him chief of magicians, enchanters, astrologers, and fortune-tellers, Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba.
12 because extraordinary spirit, knowledge, and understanding—interpreting dreams, explaining riddles, untying knots—were found in this Daniel, whom the king named Belteshazzar. Now call Daniel; he will interpret." Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”
13 Daniel was brought before the king, who asked, "Are you Daniel, one of the Judean exiles my father the king brought from Judah? Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda?
14 I heard the spirit of the gods is in you—light, understanding, and rare wisdom found in you. Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima.
15 The wise men and enchanters were brought before me to read this writing and tell me its meaning, but couldn't. An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba.
16 I've heard you can interpret and untie knots. If you read this writing and tell me its meaning, you'll wear purple, a gold chain on your neck, and rule third in the kingdom." Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
17 Daniel answered the king, "Keep your gifts; give your rewards to another. Still, I will read the king the writing and tell him its meaning. Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.
18 Your Majesty, the Most High our Father gave your father Nebuchadnezzar the kingdom, greatness, glory, and majesty. “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba.
19 Because of the greatness he gave him, all peoples, nations, and languages trembled and feared before him. He killed whom he wished, let live whom he wished, raised whom he wished, humbled whom he wished. Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.
20 When his heart grew proud and his spirit hardened into arrogance, he was deposed from his royal throne and his glory taken away. Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.
21 He was driven from people, his mind made like an animal's; he lived with wild donkeys, was fed grass like an ox, and the dew of heaven soaked him—until he knew the Most High our Father rules the kingdom of men and sets over it whomever he chooses. Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
22 But you, Belshazzar his son, have not humbled your heart, though you knew all this. “Amma kai ɗansa, Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka.
23 Instead, you lifted yourself against heaven's Sovereign. You had his house's vessels brought before you, and you, your nobles, wives, and concubines drank wine from them. You praised gods of silver, gold, bronze, iron, wood, and stone—gods that cannot see, hear, or know anything. But the One holding your breath in his hand, who owns all your ways—our Father—you have not honored. A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
24 Therefore he sent the hand that wrote this inscription. Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan.
25 This is the writing that was inscribed: MENE, MENE, TEKEL, PARSIN. “Wannan shi ne rubutun da aka yi, Mene, mene, tekel, farsin
26 This is what it means: MENE—our Father counted your kingdom's days and ended it. “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene , Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe.
27 TEKEL—you have been weighed on the scales and found wanting. “Tekel , An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa.
28 PERES—your kingdom has been divided and given to the Medes and Persians." “Feres , An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.”
29 Then Belshazzar gave the order, and they clothed Daniel in purple, put a gold chain on his neck, and proclaimed him third ruler in the kingdom. Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.
30 That very night Belshazzar, king of the Babylonians, was killed. A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa,
31 And Darius the Mede received the kingdom, being about sixty-two years old. Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]