Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 King Nebuchadnezzar, to all peoples, nations, and languages living throughout the earth: May your peace be multiplied. Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!
2 I am glad to declare the signs and wonders the Most High God has done for me. Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina.
3 How great are his signs, and how mighty are his wonders! His kingdom is an everlasting kingdom, and his dominion is from generation to generation. Alamunsa da girma suke, ayyukansa da girma suke! Mulkinsa mulki ne na har abada; sarautarsa kuma za tă dawwama daga zamani zuwa zamani.
4 I, Nebuchadnezzar, was at ease in my house and flourishing in my palace. Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa.
5 I saw a dream that frightened me; thoughts on my bed and visions in my head terrified me. Na yi mafarkin da ya ba ni tsoro. A sa’ad da nake kwance a gadona, siffofi da wahayoyi da suka bi ta cikin tunanina sun firgita ni.
6 So I ordered all Babylon's wise men brought before me to tell me the dream's meaning. Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin.
7 Then the magicians, enchanters, Babylonians, and astrologers entered. I told them the dream, but they could not interpret it for me. Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba.
8 Finally Daniel came before me—named Belteshazzar after my god's name, the holy gods' spirit in him—and I told him the dream. A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.)
9 Belteshazzar, chief magician, I know the spirit of the holy gods is in you, and no mystery baffles you—tell me the visions of my dream that I saw, and their meaning. Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini.
10 The visions in my mind while in bed: I saw a tree in the middle of the earth, very tall. Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai.
11 The tree grew and became strong, and its top reached to heaven, and it was visible to the ends of the whole earth. Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya.
12 Its leaves were beautiful and its fruit abundant, and in it was food for all. Wild animals found shade under it, and the birds of the heavens lived in its branches, and all flesh was fed from it. Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci.
13 In my visions in bed I saw a watcher, a holy one, coming down from heaven. “A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama.
14 He shouted: Cut down the tree, chop its branches, strip its leaves, scatter its fruit. Let animals flee from under it, birds from its branches. Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa.
15 But leave the stump of its roots in the earth, bound with a band of iron and bronze, in the grass of the field. Let him be drenched with the dew of heaven, and let his portion be with the wild animals in the grass of the earth. Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye. “ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya.
16 Let his human mind be taken away and a beast's mind be given to him, and let seven periods of time pass over him. Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai su wuce a kansa.
17 The sentence is by the decree of the watchers, the decision by the word of the holy ones, so that the living may know that the Most High rules over the kingdom of men and gives it to whom he will and sets over it the lowliest of men.' “ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’
18 This is the dream I, King Nebuchadnezzar, saw. Tell me its meaning, Belteshazzar, for my kingdom's wise men can't explain it, but you can—the spirit of the holy gods is in you. “Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.”
19 Then Daniel, called Belteshazzar, was stunned briefly, alarmed by his thoughts. The king said, "Belteshazzar, don't let the dream or its meaning alarm you." Belteshazzar answered, "My lord, may the dream be for your haters, its meaning for your enemies!" Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!
20 The tree you saw grew strong, its top reaching heaven, visible to all the earth, Itacen da ka gani; wanda ya yi girma da ƙarfe, da tsayinsa ya taɓa sararin sama, wanda ana ganinsa ko’ina a duniya,
21 beautiful leaves, abundant fruit, food for all—wild animals lived beneath it, birds of the sky nested in its branches. wanda ganyayensa masu kyau ne yana da ’ya’yan itace da yawa, wanda yake ba da abinci ga duka, yana ba da wurin hutu ga namun jeji, kuma rassansa suna ɗauke da sheƙar tsuntsayen sama.
22 It is you, king—you have grown and become strong; your greatness has grown, reaching heaven, your dominion to the ends of the earth. Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya.
23 Because the king saw a watcher, a holy one, come down from heaven, saying: Cut down the tree, destroy it—but leave the stump of its roots in the ground, bound with a band of iron and bronze in the field's grass. Let him be drenched with the dew of heaven; his portion with the wild animals, until seven periods of time pass over him. “Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’
24 This is the interpretation, my king: the Most High's decree has come upon my lord the king, “Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina.
25 you'll be driven from people to live among wild animals, eating grass like oxen, drenched with the dew of heaven, until seven times pass over you and you know the Most High rules the human kingdom, giving it to whoever he chooses. Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
26 The command to leave the stump and its roots in the ground: your kingdom will be restored to you once you know Heaven rules. Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki.
27 So, king, accept my advice: break from your sins through righteousness, your wrongdoing through mercy to the poor, so your prosperity may continue. Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”
28 All this came upon King Nebuchadnezzar. Duk wannan kuwa ya faru da sarki Nebukadnezzar.
29 Twelve months later, he was walking on the roof of Babylon's royal palace. Bayan wata goma sha biyu, a sa’ad da sarki yake takawa a bisan saman ɗakin fadar Babilon,
30 The king said, "Is this not great Babylon I built as a royal house by my mighty power, for the glory of my majesty?" sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?”
31 The words were still in the king's mouth when a voice fell from heaven: "King Nebuchadnezzar, this is said to you: the kingdom has left you. Tun kalmomin suna cikin bakinsa sai ya ji murya daga sama tana cewa, “Wannan shi ne abin da aka zartar a kanka, Sarki Nebukadnezzar. An karɓe ikon mulkinka.
32 You'll be driven from people, living with wild animals, eating grass like an ox. Seven periods will pass over you, until you know the Most High rules mankind's kingdom and gives it to whomever he wills." Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.”
33 At once the word came true against Nebuchadnezzar: driven from people, he ate grass like cattle, his body soaked by the dew of heaven, until his hair grew like eagle feathers, his nails like bird claws. Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
34 When the days ended, I, Nebuchadnezzar, raised my eyes to heaven, and my reason returned. I blessed the Most High, praised and honored the One who lives forever, whose rule is everlasting, whose kingdom spans every generation. A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada. Mulkinsa dawwammamen mulki ne; sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani.
35 All the inhabitants of the earth are counted as nothing, and he does according to his will among the host of heaven and among the inhabitants of the earth; and no one can hold back his hand or say to him, "What have you done?" Dukan mutanen duniya ba a bakin kome suke ba. Yakan yi abin da ya gamshe shi da ikokin sama da kuma na mutanen duniya. Babu mai hana shi ko yă ce masa; “Me ka yi?”
36 Then my sanity returned; my majesty and splendor returned for my kingdom's glory. My advisers and nobles sought me; I was restored over my kingdom, and surpassing greatness was added to me. A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā.
37 Now I, Nebuchadnezzar, praise, exalt, and honor Heaven's King, for all his works are right, his ways just; those walking in pride he can humble. Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]