Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 King Nebuchadnezzar made a gold statue, about ninety feet tall and nine feet wide, and set it up on the Dura plain in Babylon province. Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon.
2 King Nebuchadnezzar sent for the satraps, prefects, governors, counselors, treasurers, judges, magistrates, and all provincial officials to come to the dedication of the image he had set up. Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa.
3 Then satraps, prefects, governors, counselors, treasurers, judges, magistrates, and all provincial officials gathered to dedicate the statue King Nebuchadnezzar set up, and stood before the statue Nebuchadnezzar set up. Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa.
4 Then the herald proclaimed loudly, "Peoples, nations, and languages—you are commanded: Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare.
5 When you hear the horn, flute, lyre, harp, zither, bagpipe, and all music, fall down and worship the gold image King Nebuchadnezzar set up. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
6 Anyone who doesn't fall down and worship will immediately be thrown into a blazing fiery furnace." Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.”
7 As soon as all peoples heard the horn, flute, lyre, harp, zither, and every kind of music, all peoples, nations, and languages fell down and worshiped the golden image King Nebuchadnezzar had set up. Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
8 At that time certain astrologers came forward and maliciously accused the Jews. A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari suka zo gaba suka yi karar Yahudawa.
9 They said to King Nebuchadnezzar, "King, may you live forever! Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe,
10 You, king, decreed: whoever hears the horn, flute, lyre, harp, zither, bagpipe, and any music must fall down and worship the gold image, Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya,
11 and whoever does not fall down and worship will be thrown into a blazing fiery furnace. kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta.
12 Some Jews you put in charge of Babylon province—Shadrach, Meshach, and Abednego—disregard you, king. They won't serve your gods or worship the gold statue you set up." Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”
13 Furious, Nebuchadnezzar ordered Shadrach, Meshach, and Abednego brought; they were brought before the king. Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki,
14 Nebuchadnezzar said, "Shadrach, Meshach, Abednego, is it true you don't serve my gods or worship the gold statue I set up? sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa?
15 Now if you're ready—when horn, flute, lyre, harp, zither, bagpipe, and every kind of music sound, fall down and worship the image I made—good. But if you don't worship, you'll be thrown at once into a blazing fiery furnace. What god can rescue you from my hands?" Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
16 Shadrach, Meshach, and Abednego answered the king, "Nebuchadnezzar, we don't need to answer you about this. Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu.
17 If our Father, whom we serve, can rescue us, he will rescue us from the blazing furnace and from your hand, king. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka.
18 But if not, know this, king: we won't serve your gods or worship the gold statue you set up." Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.”
19 Then Nebuchadnezzar, furious, his expression changed toward Shadrach, Meshach, and Abednego; he ordered the furnace heated seven times hotter than normal. Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā.
20 He ordered some of his strongest soldiers to bind Shadrach, Meshach, and Abednego and throw them into the blazing furnace. Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar.
21 So these men, tied up in cloaks, trousers, turbans, and other garments, were thrown into the blazing fiery furnace. Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta.
22 Because of the king's harsh order and furnace's extreme heat, the fire's flame killed the men who lifted up Shadrach, Meshach, and Abednego. Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego,
23 These three men—Shadrach, Meshach, and Abednego—fell bound into the blazing furnace. waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar.
24 Then King Nebuchadnezzar, astonished, rose in haste. He asked his advisers, "Didn't we throw three bound men into the fire?" They answered the king, "True, king." Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.”
25 He said, "Look—I see four men, unbound, walking in the middle of the fire, unharmed; the fourth looks like a son of the gods." Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.”
26 Nebuchadnezzar went to the blazing furnace's door and said, "Shadrach, Meshach, and Abednego, servants of the Most High God, come out here!" Shadrach, Meshach, and Abednego came out of the fire. Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar,
27 The satraps, prefects, governors, and king's counselors gathered and saw fire had no power over these men's bodies—hair not singed, robes unharmed, no smell of fire on them. Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba.
28 Nebuchadnezzar said, "Blessed be the God of Shadrach, Meshach, and Abednego! He sent his angel and rescued his trusting servants. They defied the king's command and were willing to die rather than serve or worship any god but their own God. Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.
29 I decree: any people, nation, or language that speaks anything against the God of Shadrach, Meshach, and Abednego will be cut to pieces, their houses turned to rubble—since no other god can rescue like this." Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.”
30 Then the king promoted Shadrach, Meshach, and Abednego in the province of Babylon. Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]