Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 7 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In Belshazzar king of Babylon's first year, Daniel dreamed and saw visions in his head on his bed. He wrote the dream, summarizing the matters. A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa.
2 Daniel said: In my night vision I saw the four winds of heaven churning the great sea. Daniyel ya ce, “A cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga kusurwoyi huɗu na sama suna gurɓata babban teku.
3 And four great beasts came up out of the sea, each different from the others. Sai ga dabbobi huɗu, kowannensu ya yi dabam da sauran, suna fitowa daga teku.
4 The first was like a lion, with eagle's wings. I watched until its wings were torn off; it was lifted off the ground, set on two feet like a human, and given a human heart. “Na farkon ya yi kamar zaki kuma yana da fikafikai kamar gaggafa. Ina kallo, sai aka fizge fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.
5 A second beast appeared, like a bear, raised up on one side, three ribs in its mouth between its teeth. It was told, 'Get up, eat much flesh.' “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’
6 After this I watched: another beast, like a leopard, with four bird wings on its back, four heads, and given authority to rule. “Bayan haka, na duba, a gabana kuwa ga wata dabba wadda ta yi kamar Damisa, a bayanta kuma tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu. Wannan dabbar tana da kawuna huɗu, aka kuma ba ta iko tă yi mulki.
7 After this, in my night vision, a fourth beast appeared—dreadful, terrifying, incredibly strong, with huge iron teeth. It devoured, crushed, and trampled the rest underfoot, different from every beast before it, with ten horns. “Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma.
8 While I watched the horns, another—a little horn—rose among them, and three of the first horns were uprooted before it. It had eyes like human eyes and a mouth speaking boastfully. “Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya.
9 As I watched, thrones were set in place, and the Ancient of Days, our Father, took his seat. His clothing was white as snow; the hair of his head was like pure wool. His throne was flaming with fire, and its wheels were all ablaze. “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.
10 A river of fire flowed out, streaming from before him. Thousands of thousands served him, and 10,000 upon 10,000 stood before him. The court sat, and the books were opened. Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.
11 I watched because of the boastful words the horn spoke; I watched until the beast was killed, its body destroyed and given to the burning fire. “Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta.
12 The rest of the beasts lost authority but had their lives prolonged for a set time and season. (An tuɓe sauran dabbobin daga mulkinsu, amma aka bar su su rayu na wani lokaci.)
13 In my night vision I looked, and there before me, coming with the clouds of heaven, was one like a son of man. He approached the Ancient of Days, our Father, and was led into his presence. “A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa.
14 And he was given authority, glory, and a kingdom, so that all peoples, nations, and languages would serve him. His dominion is an everlasting dominion that will not pass away, and his kingdom is one that will never be destroyed. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.
15 I, Daniel, was troubled in spirit, and the visions that passed through my mind alarmed me. “Ni, Daniyel, ruhuna ya damu ƙwarai, kuma wahayin da ya ratsa tunanina ya dame ni.
16 I approached one of those standing there and asked him the truth about all this. He told me, revealing its interpretation. Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a can, na tambaye shi gaskiya ma’anar waɗannan al’amura. “Don haka sai ya faɗa mini, ya kuma ba ni fassarar waɗannan al’amura.
17 'These four great beasts are four kings who will rise from the earth. ‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.
18 But the holy ones of the Most High, our Father, will receive and possess the kingdom forever, forever and ever. Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’
19 Then I wanted the truth about the fourth beast, different from all others—most terrifying, iron teeth, bronze claws—devouring, crushing, and trampling what remained underfoot. “Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta.
20 I also wanted to know about the ten horns on its head, and the other horn that came up before which three fell—the horn with eyes and a boastful mouth, appearing bigger than the rest. Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma.
21 As I watched, this horn was waging war against the holy ones and was defeating them, Ina cikin dubawa, sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka yana kuma cin nasara a kansu,
22 until the Ancient of Days, our Father, came, judgment was given for the holy ones of the Most High, our Father, and the holy ones' time came to possess the kingdom.' sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki.
23 He said: 'The fourth beast is a fourth kingdom on earth, unlike all other kingdoms. It will devour, trample, and crush the whole earth. “Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta.
24 The ten horns: ten kings will arise from this kingdom. After them another arises, different from the first, and subdues three kings. Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku.
25 He will speak words against the Most High, our Father, oppress the holy ones of the Most High, our Father, and try to change the set times and the law. The holy ones will be handed to him for a time, times, and half a time. Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.
26 But the court will sit in judgment, and his dominion will be taken away, consumed and destroyed forever. “ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada.
27 Kingdom, dominion, and greatness of all kingdoms under heaven will be given to the people, the holy ones of the Most High, our Father. His kingdom is a kingdom without end; all rulers will serve and obey him.' Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’
28 This ends the matter. I, Daniel—my thoughts terrified me, my face turned pale, but I kept it to myself. “Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]