Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 8 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In King Belshazzar's third year, a vision appeared to me, Daniel, after the earlier one. A shekara ta uku ta mulkin sarki Belshazar, ni, Daniyel, na ga wahayi, bayan wancan da na riga gani.
2 In the vision I was in the citadel of Susa, in Elam province; and in the vision I was beside the Ulai Canal. A cikin wahayin, na ga kaina a mafakar Shusha a yankin Elam; a wahayin na ga ina a bakin Kogin Ulai.
3 I looked up: a ram stood before the canal, two tall horns—one taller than the other, the taller coming up last. Na ɗaga ido, a gabana kuwa sai ga rago mai ƙahoni biyu, yana tsaye a gefen mashigin kogin, ƙahonin kuma suna da tsawo. Ɗaya daga cikin ƙahonin ya fi ɗayan tsawo. Wanda ya fi tsawon shi ne ya tsiro daga baya.
4 I watched the ram charging west, north, and south. No animal could stand against him, none could rescue from his power. He did as he pleased and grew great. Na lura da ragon sa’ad da ya kai karo wajen yamma da arewa da kudu. Babu wata dabbar da ta iya ƙarawa da shi, babu kuma wanda ya iya kuɓuta daga ikonsa. Ya yi yadda ya ga dama, ya kuma zama mai girma.
5 As I was considering this, suddenly a male goat came from the west across the whole earth without touching the ground; it had a prominent horn between its eyes. Yayinda nake tunani game da wannan, farat ɗaya sai ga bunsurun da yake da sanannen ƙaho tsakanin idanunsa ya ɓullo daga wajen yamma, yana ratsa dukan duniya ba ya ko taɓa ƙasa.
6 He came to the two-horned ram I saw standing by the canal and ran at it in raging power. Ya zo wajen rago mai ƙahoni biyu ɗin nan da na riga na gani tsaye a gefen mashigin kogin nan ya tasar masa da fushi mai zafi.
7 I saw him reach the ram, enraged, striking and shattering its two horns. The ram had no strength to stand against him; the goat threw it down and trampled it, and no one could rescue the ram from his power. Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, ya kai wa ragon hari. Ya kakkarya ƙahoninsa nan biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, bai iya kāre kansa daga bunsurun ba. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.
8 The goat grew very great, but at its full strength the great horn broke, and four prominent horns grew up in its place toward the four winds of heaven. Bunsurun kuwa ya ƙasaita, amma a ƙwanƙolin ikonsa sai aka karye babban ƙahonsa, kuma a wurin da ƙahon nan ya kasance waɗansu sanannun ƙahoni huɗu suka tsiro suna fuskantar kusurwoyin nan huɗu.
9 From one of them a little horn came out, growing very great toward the south, east, and the glorious land. Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa.
10 It grew great, up to the host of heaven, casting down to earth some of the host and of the stars, and trampled them. Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su.
11 It made itself great against the Prince of the host; the Prince's regular offering was removed and his sanctuary's place thrown down. Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa.
12 Because of wrongdoing, the army was handed over to it with the daily offering; it threw truth to the ground and acted and thrived. Saboda tawaye, sai aka ba da rundunar tsarkaka da kuma hadayar ƙonawa ta kowace rana ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara.
13 Then I heard a holy one speaking, and another holy one asked the speaker, "How long is the vision—the regular offering, the wrongdoing that brings desolation, sanctuary and host handed over to trampling?" Sa’an nan na ji mai tsarkin nan yana magana, wani mai tsarki kuma ya ce da wancan, “Har yaushe wannan wahayi zai tabbata, wahayi game da hadaya ta kullayaumi, da tawayen da yake kawo lalacewa, da kuma miƙa wuri mai tsarki da kuma na rundunar da za a tattake a ƙarƙashin sawu?”
14 He told me, "For 2,300 evenings and mornings; then the sanctuary will be restored to its rightful state." Sai ya ce mini, “Zai ɗauki safiya da yamma 2,300; sa’an nan za a sāke tsarkake wuri mai tsarki.”
15 As I, Daniel, watched the vision seeking to understand, one like a man stood before me. Yayinda ni, Daniyel, nake duban wahayi ina ƙoƙari in fahimce shi, sai ga wani a gabana wanda ya yi kama da mutum.
16 I heard a human voice from the Ulai calling, "Gabriel, make this man understand the vision." Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.”
17 He came near where I stood, and as he drew close I was terrified and fell facedown. He said to me, "Understand, son of man: the vision is for the time of the end." Da ya zo kusa da inda nake tsaye, na firgita na kuma fāɗi rubda ciki. Ya ce da ni “Ɗan mutum, ka gane da cewa wannan wahayi yana magana ne a kan kwanakin ƙarshe.”
18 As he spoke, I fell into a deep sleep, face to the ground; but he touched me and set me on my feet. Yayinda yake magana da ni, barci mai nauyi ya kwashe ni, da nake kwance rubda ciki. Sai ya taɓa ni ya kuma tashe ni tsaye.
19 He said, "Listen, I will tell you what will happen in the later time of the wrath, for it concerns the appointed time of the end. Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe.
20 The ram you saw with the two horns is the kings of Media and Persia. Rago mai ƙahoni biyu da ka gani, yana a madadin sarakunan Medes da Farisa ne.
21 The shaggy goat is Greece's king; the great horn between his eyes is the first king. Bunsurun kuwa sarkin Girka ne, kuma babban ƙahon da yake tsakanin idanunsa, sarki na farko ne.
22 The broken horn, four rising in its place: four kingdoms rise from his nation, but without his power. Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba.
23 At the end of their reign, when sinners reach full measure, a fierce-faced king skilled in intrigue will arise. “Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito.
24 His power will be great—but not his own—and he will cause terrible destruction, prosper, and act. He will destroy the mighty and the people of the holy ones. Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka.
25 By cunning he makes deceit thrive under his hand, and in his heart he lifts himself up. Without warning he destroys many, and rises against the Prince of princes—yet he will be broken, by no human hand. Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.
26 The vision of the evenings and mornings told to you is true, but seal it up, for it concerns days far off." “Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.”
27 I, Daniel, was overcome and sick for days. Then I got up and did the king's business, but the vision left me appalled, beyond understanding. Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]