Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 9 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In the first year of Darius son of Xerxes, a Mede, made king over the Babylonian realm. A shekara ta fari da mulkin Dariyus ɗan Zerzes (wanda yake Bamediye), wanda aka mai da shi sarki a masarautar Babiloniyawa
2 In his reign's first year, I, Daniel, understood from the books how many years our Father told Jeremiah the prophet: seventy, to complete Jerusalem's ruins. a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.
3 So I turned my face to the Sovereign Father, to seek him in prayer and pleading, with fasting, sackcloth, and ashes. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.
4 I prayed to my Father, confessing: "Sovereign Father, great and awesome, keeping covenant and faithful love for those loving him and keeping his commands, Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa,
5 we have sinned, done wrong, done evil, rebelled, turning from your commands and rulings. mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.
6 We haven't listened to your servant prophets speaking in your name to our kings, princes, ancestors, and all the land's people. Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.
7 Righteousness is yours, Sovereign Father, but ours is open shame today—Judah's people, Jerusalem's residents, all Israel, near and far, in every land where you drove them for their unfaithfulness to you. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.
8 O our Father, open shame belongs to us—our kings, princes, and ancestors—because we sinned against you. Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.
9 To the Sovereign Father belong mercy and forgiveness, for we have rebelled against him, Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;
10 and we disobeyed our Father's voice to walk in his laws set before us through his servants the prophets. ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.
11 All Israel broke your law and turned away, refusing to obey your voice. So the curse and the sworn oath written in the Law of Moses, our Father's servant, poured out on us, because we sinned against him. Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.
12 He confirmed his words against us and our judges who judged us, bringing great disaster on us; nothing under all heaven matches what happened to Jerusalem. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.
13 As written in the Law of Moses, all this disaster came on us; yet we have not sought our Father's favor by turning from our sins and understanding your truth. Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba.
14 So our Father readied the disaster and brought it on us, for our Father is righteous in all he does; but we did not obey his voice. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.
15 And now, Sovereign Father, you brought your people out of Egypt with a strong hand and made yourself a name lasting to this day—we sinned, we did wrong. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.
16 Sovereign Father, by all your righteous acts, turn your anger and rage from your city Jerusalem, your holy mountain—for our sins and our ancestors' wrongdoing made Jerusalem and your people a disgrace to all around us. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.
17 Now, our Father, hear your servant's prayer and pleas, and shine your face on your desolate sanctuary, for your own sake, Sovereign Father. “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango.
18 Turn your ear toward us, my Father, and hear; open your eyes, see our ruins and the city called by your name. We bring our pleas before you not for our righteousness but your great mercy. Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka.
19 Sovereign Father, hear! Sovereign Father, forgive! Sovereign Father, listen and act! Don't delay, for your sake, my Father, because your city and your people bear your name." Ya Ubangiji, ka saurara! Ya Ubangiji ka gafarta! Ya Ubangiji, ka ji ka kuma yi wani abu! Saboda sunanka, ya Allahna, kada ka yi jinkiri, domin da sunanka ake kiran birninka da jama’arka.”
20 Still speaking, praying, confessing my sin and my people Israel's sin, laying my plea before my Father for my Father's holy hill, Yayinda da nake magana da addu’a, ina furta zunubina da zunubin mutanena Isra’ila ina miƙa koke-kokena ga Ubangiji Allahna saboda tudunsa mai tsarki,
21 while I was still praying, Gabriel, the man I saw earlier in the vision, reached me, flying fast, about the time of the evening offering. yayinda nake cikin addu’a, sai Jibra’ilu, mutumin nan da na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta yamma.
22 He gave me insight, speaking with me and saying, "Daniel, I have now come out to give you insight and understanding. Ya umarce ni ya kuma ce mini, “Daniyel, yanzu na zo domin in ba ka hikima da ganewa.
23 As your pleas began, a word went out, and I came to tell you, for you are deeply loved. So weigh the word and understand the vision: Da zarar ka fara addu’a, an amsa, wadda na zo in faɗa maka, gama ana ƙaunar ka sosai. Saboda haka, ka yi lura da saƙon ka kuma fahimci wahayin.
24 "Seventy weeks are decreed for your people and your holy city: to end wrongdoing, finish sin, atone for guilt, bring in everlasting righteousness, seal vision and prophet, and anoint a most holy place. “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.
25 Know therefore and understand: from the time the command goes out to restore and rebuild Jerusalem until the coming of the Anointed One, the Prince, there will be seven weeks and sixty-two weeks. It will be rebuilt with streets and a moat, but in troubled times. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.
26 And after the sixty-two weeks the Anointed One will be cut off and will have nothing. The people of the prince who is to come will destroy the city and the sanctuary. Its end will come like a flood, and to the end there will be war; desolations are decreed. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara.
27 He will confirm a covenant with many for one week; mid-week he will stop sacrifice and offering. On a temple wing he will set up an abomination that causes desolation, until the decreed end pours on the desolator." Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai. A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”,
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]