Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 10 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In Cyrus king of Persia's third year, a message was revealed to Daniel, called Belteshazzar—true, about a great war. He understood it, gaining insight into the vision. A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.
2 In those days I, Daniel, was mourning for three full weeks. A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku.
3 I ate no fine food; no meat or wine touched my mouth; I used no oil at all, until three weeks passed. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.
4 On the twenty-fourth day of month one, I stood on the bank of the great river—the Tigris. A rana ta ashirin da huɗu ga watan farko, a sa’ad da nake tsaye a bakin babban kogi, Tigris,
5 I looked up and saw a man in linen, a belt of fine gold of Uphaz around his waist. na ɗaga kaina na duba sai ga wani mutum tsaye sanye da rigar lilin, ya yi ɗamara da zinariya zalla daga Ufaz kewaye da ƙugunsa.
6 His body like beryl, his face like lightning, his eyes like torches of fire, his arms and legs like polished bronze, and the sound of his words like a roaring crowd. Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a.
7 I, Daniel, alone saw the vision; the men with me didn't see it, but great trembling fell on them, and they fled and hid. Ni, Daniyel, kaɗai ne na ga wahayin; mutanen da suke tare da ni ba su gani ba, amma wata irin babbar razana ta auko musu har suka gudu suka ɓuya.
8 Left alone, I saw this great vision. No strength remained in me; my face turned deathly pale, and I kept no strength. Sai aka bar ni ni kaɗai, ina juyayi wannan babban wahayi, ba ni da sauran ƙarfi, fuskata ta yamutse kuma ba ni da sauran ƙarfi.
9 Then I heard his words, and hearing them, I fell face down on the ground in a deep sleep. Sai na ji yana magana, da ina sauraronsa, sai na shiga barci mai nauyi, na kuwa fāɗi rubda ciki.
10 Suddenly a hand touched me and set me trembling on my hands and knees. Sai hannu ya taɓa ni ya sa makyarkyata a hannuna da ƙafafuna.
11 He said to me, "Daniel, dearly loved man, understand the words I speak to you; stand up, for I am now sent to you." When he spoke this word to me, I stood up, trembling. Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.
12 He said to me, "Don't be afraid, Daniel. From the first day you set your heart to understand and humbled yourself before your Father, your words were heard, and I came because of your words. Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni.
13 But the prince of Persia's kingdom opposed me twenty-one days; then Michael, one of the chief princes, came to help me, for I was left there with Persia's kings. Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa.
14 I came to help you understand your people's future in days to come, for the vision is for days still ahead." Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.”
15 As he spoke these words to me, I turned my face to the ground, unable to speak. Yayinda yake faɗin mini haka, sai na sunkuyar da kaina ƙasa shiru, ba magana.
16 Then one like a man touched my lips. I opened my mouth and began to speak. I said to the one standing before me, "My lord, the vision has filled me with pain, and I have no strength left. Sai wani wanda ya yi kama da mutum ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako.
17 How can I, your servant, speak with you, my lord? No strength remains in me now, no breath is left." Yaya ni bawanka zan iya magana da kai, ranka yă daɗe? Ƙarfina ya ƙare kuma ina numfashi da ƙyar.”
18 Again the one who looked like a man touched me and strengthened me. Har yanzu wannan wanda yana kama da mutum ya taɓa ni ya kuma ba ni ƙarfi.
19 He said, "Don't be afraid, treasured one. Peace to you; be strong, be strong!" His words strengthened me, and I said, "Speak, my lord, for you have strengthened me." Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.” Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.”
20 He said, "Do you know why I came to you? Now I return to fight Persia's prince; then, as I leave, Greece's prince comes. Sai ya ce mini, “Ka san abin da ya kawo ni gare ka? Ba da jimawa ba zan koma in yi yaƙi da mai mulkin Farisa, kuma idan na tafi, mai mulkin Hellenawa zai taso;
21 But first I'll tell you what's written in the Book of Truth: none stands firmly with me against them but Michael, your prince." amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]