Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Daniel 11 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 And I, in the first year of Darius the Mede, stood up to support and strengthen him. A shekara ta fari ta Dariyus mutumin Mede, na ɗauki matsayina domin in goyi baya in kuma kāre shi.)
2 Now I'll tell you the truth: look, three more kings will rise in Persia, then a fourth far richer than all. Strengthened by his wealth, he will stir up everyone against Greece's kingdom. “Yanzu dai, zan faɗa maka gaskiya. Sarakuna uku za su taso a Farisa, sa’an nan kuma na huɗu, wanda zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da zai sami iko saboda dukiyarsa, zai zuga dukan kowane mutum yă yi gāba da masarautar Girka.
3 Then a mighty king will arise, who will rule with great dominion and do as he pleases. Sa’an nan wani babban sarki zai bayyana, wanda zai yi mulki da babban iko yă kuma yi abin da ya ga dama.
4 Once he rises, his kingdom will break apart and split toward the four winds of heaven—not to his descendants, nor with the power he held, for his kingdom will be uprooted and given to others besides them. Bayan da ya bayyana, daularsa za tă wargaje za a rarraba ta zuwa kusurwoyi huɗu na duniya, a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, ba kuwa za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki daularsa a kuma ba wa waɗansu.
5 The king of the south will grow strong; one of his commanders will grow stronger than him and rule—his dominion will be vast. “Sai sarki Kudu zai yi ƙarfi ƙwarai, amma ɗaya daga cikin komandodinsa zai yi ƙarfi fiye da shi, zai kuma yi mulki masarautarsa da iko mai girma.
6 After some years they will ally: the daughter of the king of the south will come to the king of the north to make an agreement. But she won't keep her strength, nor will he or his arm stand. She will be handed over—with her escort, her father, and her supporter—in those times. Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta da kuma wanda ya goyi bayanta.
7 A shoot from her roots will rise in his place, attack the army, enter the north king's fortress, act against them, and prevail. “Wani daga cikin zuriyarta zai taso yă ɗauki matsayinta. Zai kai wa sojojin sarkin Arewa hari yă kuma shiga kagararsa; zai yi yaƙi da su yă kuma yi nasara.
8 He will take their gods captive to Egypt, with their metal images and precious silver and gold vessels; for years he will stay away from the king of the north. Zai ƙwace allolinsu, siffofinsu na ƙarfe da kuma kaya masu daraja na azurfa da na zinariya a kuma kai su Masar. Zai yi ’yan shekaru bai kai wa sarkin Arewa yaƙi ba.
9 The king of the north will invade the king of the south's realm, then return home. Sa’an nan sarkin Arewa zai kai wa sarkin Kudu hari, amma zai janye, yă koma ƙasarsa.
10 His sons will arm for war, gather a vast army that keeps coming, overflows, sweeps through, then renews war to his stronghold. ’Ya’yansa maza za su yi shirin yaƙi za su kuma tattara babbar rundunar sojoji, waɗanda za su yi ta mamayewa kamar rigyawar da ba iya tarewa, kuma za su kai yaƙin har kagararsa.
11 The southern king, enraged, will march out to fight the northern king, who musters a vast army; but the army is given into the southern king's hand. “Sa’an nan sai sarkin Kudu zai kama hanya da fushi zuwa yaƙi da sarkin Arewa, wanda zai tattara babbar rundunar yaƙi, amma za a ci shi da yaƙi.
12 When the crowd is carried off, his heart grows proud; he strikes down tens of thousands, yet fails. Sa’ad da zai kawar da rundunar, sarkin Kudu zai cika da girman kai zai kuma kashe mutane dubbai, duk da haka ba zai kasance mai nasara ba.
13 The king of the north will again raise a horde bigger than before, then after years come with a great army and vast supplies. Sarki Arewa kuma zai ƙara tara babbar rundunar soja, wadda ta fi ta dā girma; bayan waɗansu shekaru kuma, zai tafi yaƙi da babbar rundunar mayaƙa cike da kayan yaƙi.
14 In those times many will rise against the king of the south; violent men of your people will lift themselves up to fulfill the vision, but fail. “A waɗannan lokutan mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin Kudu. Amma waɗansu ’yan kama-karya za su taso daga jama’arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattake su.
15 The king of the north will come, raise a siege ramp, and take a fortified city; the south's forces will not stand, nor its elite troops—no strength remains to stand. Sa’an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin katagar birni don yă ci birnin da yaƙi. Sojojin nan na Kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansu ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa.
16 His invader does as he pleases; none can stand before him. He will stand in the splendid land, destruction in his hand. Wanda ya kai harin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai kafa kansa a Kyakkyawar Ƙasa zai kuma sami ikon da zai hallaka ta.
17 He will set out to enter with his kingdom's full strength, and make terms with him; he will give him a daughter of women to ruin it, but it will not stand or benefit him. Zai yunƙura yă zo da ƙarfin dukan masarautarsa zai kuma nemi haɗinkan sarkin Kudu. Zai kuma ba shi diyarsa yă aura don yă lalatar da mulkin, amma shirinsa ba zai yi nasara ba ko yă taimake shi ba.
18 Then he'll turn to the coastlands and take many, but a commander will end his arrogance, turning it back on him. Sa’an nan zai mai da hankalinsa zuwa ƙasashe a bakin kogi, zai kuma kama da yawansu, amma wani komanda zai kawo ƙarshen faɗin ransa, zai kuma sa faɗin ransa yă koma masa.
19 Then he will turn his face toward the fortresses of his own land, stumble, fall, and be found no more. Bayan wannan, zai juya ga kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe yă fāɗi, ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.
20 In his place will rise one who sends a tax collector for the glory of the kingdom; within a few days he'll be broken—not in anger, not in battle. “Magājinsa zai aiki mai karɓar haraji don darajar masarautarsa. Amma ba da daɗewa ba za a hallaka shi, duk da haka ba da fushi ko cikin yaƙi ba.
21 A despised man will rise in his place, denied royal honor. He'll come in a time of ease and seize the kingdom through flattery. “Magājin wannan sarki zai zama wani mutumin banza wanda ma bai fito daga gidan sarauta ba. Zai taso ba zato ba tsammani, yă ƙwace sarautar ta hanyar zamba.
22 Armies will be swept away before him and broken, and the prince of the covenant as well. Sa’an nan zai shafe mayaƙa masu yawa a gabansa; zai hallaka har da waɗanda suke mulki na alkawari.
23 Once allied with him, he will act dishonestly and grow strong with only a few people. Bayan ƙulla yarjejjeniya da shi, zai yi zamba cikin aminci, kuma zai sami damar hawan mulki da goyon baya mutane kaɗan.
24 In a time of security, he will enter the province's richest regions and do what neither his fathers nor their fathers did—scattering plunder, spoil, and goods among them, devising schemes against fortresses, but only for a time. Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai.
25 He will rouse his strength and courage against the king of the south with a great army. The king of the south will fight with a very great, mighty army—but won't stand, for plots will be devised against him. “Tare da babbar rundunar mayaƙa zai yi ƙarfin hali yă far wa sarkin Kudu da yaƙi. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya.
26 Those who eat his food will break him; his army is swept away, and many fall slain. Waɗanda suke ci daga tanadin sarki za su yi ƙoƙari su hallaka shi; za a share mayaƙansa, kuma za a kashe mutane masu yawa a yaƙin.
27 Both kings' hearts bent on evil will speak lies at one table, but it will fail—the end awaits its appointed time. Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.
28 He returns to his land with great wealth, heart against the holy covenant; he acts, then returns to his land. “Sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai girma, amma zuciyarsa za tă yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai ɗauki mataki a kan wannan abu sa’an nan yă koma ƙasarsa.
29 At the appointed time he will return and head south, but this time won't match the earlier or the latter. “A ƙayyadadden lokaci zai sāke kai wa Kudu hari, amma a wannan karo abin da zai faru zai sha bamban daga abin da ya faru can baya.
30 For ships of Kittim will come against him; he loses heart, turns back, rages against the holy covenant, and acts. He returns and favors those who abandon the holy covenant. Jiragen ruwa yammancin bakin teku za su yi gāba da shi, zuciyarsa kuwa za tă yi sanyi. Sa’an nan zai juya ya huce haushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai komo yă nuna jinƙai ga waɗanda suka juya wa tsattsarkan alkawari baya.
31 His forces will rise, defile the sanctuary fortress, end the daily sacrifice, and set up the abomination that causes desolation. “Mayaƙansa za su taso su ƙazantar da kagarar haikali za su kuma kawar da hadaya ta kullum. Sa’an nan za su kafa abin banƙyama da yake lalatarwa.
32 He will corrupt those who violate the covenant with flattery, but people who know their Father will stand firm and act. Ta wurin daɗin baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi.
33 The wise among the people will teach many, but will fall for a time by sword, flame, captivity, and plunder. “Waɗanda suke da hikima za su wayar da kan mutane da yawa, duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.
34 When they fall, they will receive a little help, and many will join them with flattery. Sa’ad da suka fāɗi, za su sami ɗan taimako, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.
35 Some of the wise will stumble, to be refined, purified, and cleansed until the end time, for it still awaits the set time. Waɗansu masu hikima za su yi tuntuɓe, don a tsabtacce su, a tsarkake su, su yi tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.
36 The king will do as he pleases, lifting and enlarging himself above every god, speaking shocking things against our Father. He will flourish until the wrath is spent, since what is decreed will happen. “Sarkin zai yi abin da ya ga dama. Zai ɗaukaka yă kuma girmama kansa gaba da kowane allah zai kuma faɗa munanan abubuwa a kan Allahn alloli. Zai yi nasara har sai lokacin hukunci ya cika, gama abin da aka ƙaddara zai cika.
37 He will disregard his fathers' gods, women's desired one, and every god—he will set himself above them all. Ba zai kula da alloli iyayensa ba ko wanda mata suke sha’awa, balle ma yă ga darajar wani allah, amma zai ɗaukaka kansa gaba da su duka.
38 Instead he'll honor a god of fortresses, unknown to his fathers, with gold, silver, precious stones, and costly gifts. A maimakonsu, zai ɗaukaka allahn kagarai; allahn da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tsada.
39 With a foreign god he attacks the strongest fortresses. He greatly honors those who acknowledge him, gives them rule over many, and divides land for a price. Zai kai wa kagarai mafi ƙarfi hari da taimakon baƙon allah zai kuma girmama waɗanda suka yarda da shi zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.
40 At the end time, the king of the south will engage him, and the king of the north will storm against him with chariots, horsemen, and many ships. He will invade the lands, overflow, and pass through. “A lokaci ƙarshe sarkin Kudu zai tasar masa da yaƙi, sarkin Arewa kuwa zai tunzura, yă tasar masa da kekunan yaƙi da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, yă ci su da yaƙi, yă wuce.
41 He enters the beautiful land; many fall, but Edom, Moab, and Ammon's chief sons escape his hand. Zai kuma mamaye Kyakkyawa Ƙasa. Ƙasashe masu yawa za su fāɗi, amma Edom, Mowab da kuma shugabannin Ammon za su kuɓuta daga hannunsa.
42 He will stretch out his hand against the lands, and the land of Egypt will not escape. Zai fadada mulkinsa har zuwa ƙasashe masu yawa; Masar ma ba za tă tsira ba.
43 He will rule gold and silver treasures, and all Egypt's riches, with Libyans and Cushites at his heels. Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tsada na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Kush da yaƙi.
44 But news from the east and north will terrify him, and he'll set out in great rage to destroy and annihilate many. Amma labari daga gabas da arewa za su firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, yă karkashe mutane da yawa, yă shafe su.
45 He will pitch his palace tents between the seas and the beautiful holy mountain, then come to his end with no helper. Zai kafa tentin mulkinsa tsakanin tekunan da suke a kyakkyawan tsauni mai tsarki. Duk da haka zai zo ga ƙarshensa, kuma babu wanda zai taimake shi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]