Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Peter and John were going up to the temple at around three in the afternoon, the hour of prayer. Wata rana, Bitrus da Yohanna suna haurawa zuwa haikali a lokacin addu’a da ƙarfe uku na rana.
2 A man lame from birth was carried and placed daily at the temple gate called Beautiful, to beg from those entering the temple. To, sai ga wani da aka haifa gurgu ana ɗauke da shi zuwa ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, inda akan ajiye kowace rana, don yă yi bara daga masu shigowa cikin filayen haikali.
3 Seeing Peter and John about to go into the temple, he asked them for money. Da ya ga Bitrus da Yohanna suna gab da shiga, sai ya roƙe su kuɗi.
4 And Peter, gazing at him with John, said, "Look at us." Bitrus kuwa ya kafa masa ido, haka ma Yohanna. Sai Bitrus ya ce, “Dube mu!”
5 And he fixed his attention on them, expecting to receive something from them. Saboda haka mutumin ya mai da hankalinsa a kansu, yana fata samun wani abu daga gare su.
6 Peter said, "I own no silver or gold, but I give you what I have: in the name of Jesus Christ of Nazareth, rise and walk." Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.”
7 Taking his right hand, he raised him up; instantly his feet and ankles grew strong. Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi.
8 Jumping up, he stood, began walking, and entered the temple with them, walking, jumping, and praising our Father. Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah.
9 And all the people saw him walking and praising our Father. Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah,
10 They recognized him as the beggar who sat at the temple's Beautiful Gate, and were filled with wonder and amazement at what had happened to him. sai suka gane cewa shi ne mutumin nan wanda dā yake zama yana bara a bakin ƙofar haikalin da ake kira Kyakkyawa, suka kuwa cika da mamaki da tsoro a kan abin da ya faru gare shi.
11 As he held on to Peter and John, all the people ran to them at the portico called Solomon's, utterly astonished. Tun mai bawan yana riƙe da Bitrus da Yohanna, dukan mutanen suka yi mamaki, suka zo wurinsu a guje a inda ake kira Shirayin Solomon.
12 Seeing this, Peter said to the people, "Israelites, why does this amaze you? Why stare at us, as if by our own power or godliness we made him walk? Da Bitrus ya ga haka, sai ya ce musu, “Mutanen Isra’ila, don me wannan ya ba ku mamaki? Don me kuke kallonmu sai ka ce da ikon kanmu ne ko kuwa don ibadarmu ne muka sa wannan mutum ya yi tafiya?
13 The God of Abraham, Isaac, and Jacob, the God of our fathers, glorified his servant Jesus, whom you handed over and denied before Pilate, when Pilate decided to release him. Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi.
14 But you denied the Holy and Righteous One, asking that a murderer be given to you. Kuka yi mūsun sanin Mai Tsarki da Mai Adalci kuka roƙa a sakar muku mai kisankai.
15 You killed the Author of life; our Father raised him from the dead. To this we are witnesses. Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan.
16 His name, through faith in his name, has made this man strong—the very man you see and know. And faith in Jesus has given him this complete health right before your eyes. Ta wurin bangaskiya cikin sunan Yesu ne wannan mutum da kuke gani kuka kuma sani ya sami ƙarfi. Da sunan Yesu, da kuma bangaskiyar da take samuwa ta wurinsa ne ya ba shi cikakkiyar warkarwa, yadda dukanku kuke gani.
17 "And now, brothers, I know that you acted in ignorance, as did also your rulers. “To, ’yan’uwa, na san cewa, kun aikata wannan cikin jahilci ne, yadda shugabanninku suka yi.
18 But our Father fulfilled what he predicted through all the prophets: his Christ would suffer. Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa cewa, Kiristinsa zai sha wahala.
19 Repent, then, and turn back, so your sins are wiped out, Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,
20 that times of refreshing may come from our Father's presence, and that he may send the Christ appointed for you, Jesus, don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan.
21 whom heaven must receive until all things are restored, about which our Father spoke through his holy prophets long ago. Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.
22 Moses said, 'Your Father will raise up a prophet like me for you, from your brothers. Listen to him in everything he tells you.' Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai tasar muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku; dole ku saurari duk abin da ya faɗa muku.
23 Anyone who does not listen to that prophet will be utterly destroyed from among the people.' Duk wanda bai saurare shi ba za a ware shi gaba ɗaya daga mutanensa.’
24 All the prophets who spoke, from Samuel onward, also announced these days. “Tabbatacce, dukan annabawa daga Sama’ila zuwa gaba, dukansu da suka yi magana, sun rigya faɗin waɗannan kwanaki.
25 You are the sons of the prophets and of the covenant our Father made with your fathers, telling Abraham, 'By your offspring all the families of the earth will be blessed.' Ku kuwa magādan annabawan ne da kuma na alkawarin da Allah ya yi da kakanninku. Ya ce wa Ibrahim, ‘Ta wurin zuriyarka, dukan kabilan duniya za su sami albarka.’
26 Our Father raised up his servant and sent him to you first, to bless you by turning each of you from your evil." Da Allah ya tashe bawansa, ya aike shi da fari zuwa gare ku don yă albarkace ku ta wurin juye kowannenku daga mugayen hanyoyinku.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]