Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 When the day of Pentecost arrived, they were all together in one place. Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
2 Suddenly a sound like a violent, rushing wind came from heaven and filled the entire house where they sat. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
3 What looked like divided tongues of fire appeared and rested on each one of them. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
4 All were filled with the Holy Spirit and began speaking in other tongues, as the Spirit gave them words to say. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
5 At that time devout Jews from every nation under heaven were living in Jerusalem. To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.
6 When this sound rang out, a crowd gathered, confused, since each one heard them speak in his own language. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.
7 They were amazed and astonished, saying, "Are not all these who are speaking Galileans? Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?
8 How is it, then, that each of us hears them in our own native language? To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?
9 Parthians, Medes, and Elamites; those who live in Mesopotamia, Judea and Cappadocia, Pontus and Asia, Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,
10 Phrygia, Pamphylia, Egypt, the parts of Libya near Cyrene; visitors from Rome, Jews and converts to Judaism; Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma
11 Cretans and Arabs—we hear them telling in our own tongues the mighty works of our Father!" (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”
12 They were all amazed and perplexed, saying to one another, "What does this mean?" A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”
13 But others mocked and said, "They are full of sweet wine." Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”
14 But Peter stood with the eleven, raised his voice, and declared to them: "Men of Judea, everyone living in Jerusalem—know this and listen carefully to my words. Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.
15 These people are not drunk, as you suppose, for it is only nine o'clock in the morning. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!
16 No, this is what was spoken through the prophet Joel: A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,
17 'And in the last days, says our Father, I will pour out my Spirit on all people; your sons and your daughters will prophesy, your young men will see visions, and your old men will dream dreams. “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18 Even on my male servants and my female servants in those days I will pour out my Spirit, and they will prophesy. Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.
19 I will show wonders in the heavens above and signs on the earth below—blood and fire and billows of smoke. Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
20 The sun will be turned to darkness and the moon to blood, before the great and glorious day of the Lord comes. Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
21 And everyone who calls on the name of the Lord will be saved.'" Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
22 "Men of Israel, hear these words: Jesus of Nazareth—a man our Father attested to you through miracles, wonders, and signs our Father did through him among you, as you yourselves know. “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.
23 This man, handed over by our Father's set plan and foreknowledge, you crucified and killed by the hands of lawless men. An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
24 But our Father raised him, freeing him from death's agony, since death could not hold him. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
25 For David says of him: 'I saw our Father always before me, for he's at my right hand, so I won't be shaken.' Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
26 Therefore my heart was glad and my tongue rejoiced; moreover, my body also will rest in hope. Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege,
27 For you will not abandon my soul to the grave, nor let your Holy One see decay. gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
28 You have shown me the paths of life; you will fill me with gladness in your presence." Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
29 "Brothers, I can tell you plainly: our ancestor David died, was buried, and his tomb remains with us to this day. “’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.
30 Since he was a prophet, he knew our Father had sworn an oath to seat one of his descendants on his throne, Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.
31 he foresaw and spoke of the Christ's resurrection, that he was not abandoned to the grave, nor his body saw decay. Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba.
32 This Jesus our Father raised up, and we are all witnesses of it. Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.
33 So, lifted up to our Father's right hand, having received the promised Holy Spirit from the Father, he poured out what you now see and hear. An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.
34 For David never went up into heaven, but he himself says: "Our Father said to my Lord, 'Sit at my right hand, Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
35 until I make your enemies a footstool for your feet.'" sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’
36 "So let the whole house of Israel know for certain: our Father made this Jesus, whom you crucified, both Lord and Christ." “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
37 Cut to the heart at this, they asked Peter and the other apostles, "Brothers, what should we do?" Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”
38 Peter said to them, "Repent, and each of you be baptized in the name of Jesus Christ for the forgiveness of your sins, and you will receive the gift of the Holy Spirit. Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.
39 For the promise is for you, your children, and all far off—as many as the Sovereign our Father will call to himself." Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40 And with many other words he warned and urged them, saying, "Save yourselves from this corrupt generation." Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.”
41 So those who welcomed his message were baptized, and about 3,000 people were added that day. Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
42 They devoted themselves to the apostles' teaching and deep communion, to the breaking of bread and the prayers. Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a.
43 Awe came over everyone, and many wonders and signs were done through the apostles. Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa.
44 All who believed were together and had all things in common. Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare.
45 They sold their property and possessions and distributed the proceeds to all, as anyone needed. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
46 Every day, devoting themselves together in the temple, breaking bread house to house, they shared food with joyful, sincere hearts, Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya,
47 praising our Father, with favor among all the people. The Lord added to their number daily those being saved. suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]