Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Acts 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 While Peter and John were speaking to the people, the priests, the temple captain, and the Sadducees came up to them, Sai firistoci da shugaban masu gadin haikalin da kuma Sadukiyawa suka hauro wurin Bitrus da Yohanna yayinda suke cikin magana da mutane.
2 greatly annoyed because they were teaching the people and proclaiming the resurrection from the dead in Jesus. Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu.
3 They arrested them and put them in custody until the next day, since it was already evening. Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai kashegari.
4 But many who heard the message believed, and the men's number reached about 5,000. Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.
5 The next day their rulers, elders, and teachers of the law gathered together in Jerusalem, Kashegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima.
6 with Annas the high priest, Caiaphas, John, Alexander, and all who were of the high-priestly family. Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist.
7 They stood them in the middle and asked, "By what power or by what name did you do this?" Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa, “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”
8 Then Peter, filled with the Holy Spirit, said to them, "Rulers of the people and elders, Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu, “Masu mulki da dattawan mutane!
9 if we're questioned today about a good deed to a sick man, how he was healed. In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi,
10 Know this, all of you and all Israel's people: by the name of Jesus Christ of Nazareth, whom you crucified, whom our Father raised from the dead—by him this man stands before you well. to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.
11 This Jesus is "the stone you builders rejected, which has become the cornerstone." Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’
12 Salvation is in no one else; no other name under heaven is given among people by which we must be saved." Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”
13 Seeing Peter and John's boldness, and realizing they were uneducated, ordinary men, they were amazed and recognized they had been with Jesus. Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
14 Seeing the healed man standing with them, they had nothing to say against it. Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi.
15 So they ordered them to leave the council, and then they conferred among themselves, Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna.
16 saying, "What should we do with these men? A notable sign has happened through them, plain to all who live in Jerusalem, and we cannot deny it. Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba.
17 But to stop this from spreading further among the people, let's warn them to speak to no one in this name again." Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”
18 They called them and ordered them not to speak or teach at all in Jesus' name. Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.
19 Peter and John answered them, "You judge whether it's right before our Father to listen to you rather than to him. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.
20 For we cannot help speaking about what we have seen and heard." Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”
21 After more threats, they released them, finding no way to punish them because of the people, since all were glorifying our Father for what happened. Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22 For the man who had received this sign of healing was over forty years old. Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in.
23 Once released, they went to their own people and reported all the chief priests and elders had said to them. Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu.
24 Hearing this, they raised their voices together to our Father and said, "Sovereign Father, you made heaven, earth, sea, and everything in them. Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.
25 You spoke by the Holy Spirit through the mouth of our father David, your servant: "Why did the nations rage and the peoples plot in vain?" Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa, “ ‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?
26 The kings of the earth took their stand, and the rulers gathered together against our Father and against his Anointed." Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’
27 For truly, in this city, Herod and Pontius Pilate gathered with the Gentiles and peoples of Israel against your holy servant Jesus, whom you anointed, Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe.
28 to do whatever your hand and your plan had decided beforehand should happen. Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.
29 Now, Father, see their threats, and let your servants speak your word with all boldness, Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali.
30 as you reach out your hand to heal, and signs and wonders occur through the name of your holy servant Jesus. Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
31 After they prayed, the place they were gathered in shook; all were filled with the Holy Spirit and spoke the word of our Father boldly. Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.
32 All the believers were one in heart and soul; no one called any possession their own, but held everything in common. Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi.
33 With great power the apostles testified to the Lord Jesus's resurrection, and great grace rested on them all. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.
34 No one among them was needy: all who owned land or houses sold them and brought the price of what was sold, Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar,
35 and laid it at the apostles' feet, and it was distributed to each according to their need. su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
36 Joseph, a Levite from Cyprus, whom the apostles called Barnabas (which means Son of Encouragement), Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa)
37 sold a field he owned, brought the money, and laid it at the apostles' feet. ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]