Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Then Solomon began building our Father's house in Jerusalem, on Mount Moriah, where our Father had appeared to his father David, at the site David had prepared on Ornan the Jebusite's threshing floor. Sai Solomon ya fara ginin haikalin Ubangiji a Urushalima, a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga mahaifinsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Ornan mutumin Yebus.
2 He began building in the second month, second day, in the fourth year of his reign. Ya fara ginin a rana biyu ga wata na biyu a shekara ta huɗu ta mulkinsa.
3 These are the foundations Solomon laid for building the house of our Father: length about ninety feet by the earlier standard, width about thirty feet. Tushen da Solomon ya kafa don ginin haikalin Allah tsawonsa kamun sittin, fāɗinsa kamun ashirin ne (bisa ga tsohon ma’auni).
4 The portico across the house's front, along the width of the house, was about thirty feet wide; its height was 120 feet. He covered the inside with pure gold. Shirayin da yake gaban haikalin kuma kamun ashirin ne da ya nausa ya ƙetare, fāɗin ginin kuma tsayinsa kamu ashirin ne. Ya shafe cikin da zinariya zalla.
5 He paneled the large room with cypress wood, covered it in fine gold, and added palm trees and chains. Ya shafe babban zauren da fir, ya kuma rufe shi da zinariya mai kyau; ya yi masa ado da zāne-zānen itatuwan dabino da kuma jerin zāne-zāne.
6 He adorned the house with precious stones for beauty, and the gold was from Parvaim. Ya yi wa haikalin ado da duwatsu masu daraja. Zinariyar da ya yi amfani da su kuwa zinariya Farwayim ne.
7 He covered the house—beams, thresholds, walls, doors—with gold, and carved cherubim on the walls. Ya shafe ginshiƙan saman ɗaki, madogaran ƙofofi, bangaye da kuma ƙofofin haikalin da zinariya, ya sassaƙa kerubobi a bangayen.
8 He made the Most Holy Place, its length matching the house's width—about thirty feet—and its width also thirty feet. He overlaid it with about twenty-three tons of fine gold. Ya gina Wuri Mafi Tsarki, tsawonsa daidai da fāɗin haikalin. Tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuwa kamu ashirin. Ya shafe cikin da talenti ɗari shida na zinariya zalla.
9 Nails weighed about twenty ounces of gold; he covered the upper rooms with gold. Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya zalla.
10 In the Most Holy Place he made two carved cherubim, gilded them. Cikin Wuri Mafi Tsarki ya yi kerubobi biyu, ya kuma shafe su da zinariya.
11 Together the cherubim's wings spanned about thirty feet: one wing of the first cherub, about seven and a half feet, touched the house wall; its other wing, also about seven and a half feet, touched the second cherub's wing. Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.
12 The second cherub's wing, about seven and a half feet, touched the house wall; its other wing, also about seven and a half feet, joined the first cherub's wing. Haka ma fiffiken kerub na biyu ɗin tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo bangon haikalin, ɗaya fiffiken shi ma tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub na farko.
13 The wings of these cherubim spread about thirty feet; they stood on their feet, facing the main hall. Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban zauren.
14 He made the curtain of blue, purple, and crimson yarn and fine linen, with cherubim woven into it. Sai ya yi labule mai ruwan shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, ya kuma ƙunshi hotunan kerubobin da aka saƙa a cikinsa.
15 In front of the house he made two pillars, each about fifty-three feet tall, topped with a capital about seven and a half feet high. A gaban haikalin ya yi ginshiƙai biyu, waɗanda tsawonsu ya kai kamu talatin da biyar, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.
16 He made chains like a necklace, put them atop the pillars, made one hundred pomegranates, and fastened them to the chains. Ya saƙa sarƙoƙi, ya kuma sa su a bisa ginshiƙan. Ya kuma yi rumman ɗari ya rataya wa sarƙoƙin.
17 He set up the pillars in front of the temple, one to the right, one to the left, naming the right one Jachin and the left one Boaz. Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya a kudu, ɗaya kuma a arewa. Ya kira wanda yake kudun, Yakin, na arewan kuwa ya kira Bowaz.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]