Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 4 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 He made a bronze altar thirty feet long, thirty feet wide, and fifteen feet high. Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma.
2 He made the cast-metal Sea, round: fifteen feet across, seven and a half high, forty-five around. Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye.
3 Below the rim, figures of oxen encircled it, about seven to every foot around the Sea, cast in two rows as one piece with it. Ƙasa da da’ira kuwa, akwai siffofin bijimai kewaye da ita, goma ga kowane kamu guda. An yi zubin bijiman a jeri biyu a gefe guda na kwatarniya.
4 The Sea stood on twelve oxen, three facing north, three west, three south, three east, resting on them, their hindquarters all inward. Tekun ya tsaya a kan bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku na fuskantar yamma, uku na fuskantar kudu, uku kuma na fuskantar gabas. Tekun ya zauna a kansu, kuma ƙarfafun bayansu suna wajen tsakiya.
5 About three inches thick, its rim like a cup's, like a lily's flower, holding about 17,000 gallons. Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku.
6 He made ten washing basins, five south, five north, to rinse what was used for the burnt offerings; the Sea was for the priests to wash in. Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.
7 He made ten gold lampstands as specified, five for the temple's south side, five for the north. Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa.
8 He made ten tables, placed them in the temple—five south, five north—and one hundred gold basins. Ya yi tebur goma ya kuma sa su cikin haikalin, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya kuma yi kwanonin yayyafawa guda ɗari.
9 He made the priests' court, the great court, its doors, and plated their doors with bronze. Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla.
10 He placed the Sea on the south side, at the southeast corner. Ya sa ƙaton kwano mai suna Teku a gefen kudu, a kusurwa kudu maso gabas.
11 Huram made the pots, shovels, and basins. So Huram finished the work he did for King Solomon in the house of our Father: Ya kuma yi tukwane da manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama aikin da ya yi wa Sarki Solomon a cikin haikalin Allah.
12 the two pillars; the two bowl-shaped capitals atop the pillars; the two networks covering those capitals; Ginshiƙai biyu; kwanoni biyu masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai; jeri biyu na tuƙaƙƙen adon kwanonin yayyafawa masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai;
13 400 pomegranates for the two networks, two rows each, covering the two capital bowls on the pillars; rumman ɗari huɗu don jeri biyu na tuƙaƙƙe (layi biyu na rumman don kowane tuƙaƙƙe, mai adon kwano mai siffar kwartaniya a bisan ginshiƙai);
14 the stands and the basins on the stands; dakalai da darunansu;
15 the one Sea and the twelve oxen beneath it. ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa;
16 Pots, shovels, meat forks, and all their utensils—Huram-abi made these for King Solomon, for our Father's house, of polished bronze. tukwane, manyan cokula, cokula masu yatsu don nama da dukan kayayyakin da suka shafi wannan. Dukan kayayyakin da Huram-Abi ya yi domin Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji an yi su da gogaggen tagulla ne.
17 The king had them cast in clay molds in the Jordan plain between Succoth and Zeredah. Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda.
18 Solomon made all these items in such quantity that the bronze weight could not be determined. Dukan waɗannan abubuwa da Solomon ya yi suna da tsada ƙwarai har suka kai nauyin tagullar da ya fi misali.
19 Solomon made all the furnishings for our Father's house: the golden altar and tables with the bread of the Presence. Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke a cikin haikalin Allah. Bagaden zinariya; teburin da ake ajiye burodin Kasancewa;
20 The pure gold lampstands with their lamps, to burn before the inner sanctuary as prescribed; wurin ajiye fitila na zinariya zalla tare da fitilunsu, don ƙonawa a gaban wuri mai tsarki na ciki kamar yadda aka tsara;
21 the gold flowers, lamps, and tongs (these were of the purest gold). aikin zānen furannin zinariya da fitilu da abin ɗiban wuta (an yi su da zinariya zalla);
22 Pure gold: the wick trimmers, sprinkling bowls, dishes, censers, and the temple's doorways—inner doors to the Most Holy Place, and the main hall's doors. arautaki; kwanonin yayyafawa, kwanoni da hantsuka; da kuma ƙofofin zinariya na haikali, ƙofofi na ciki zuwa Wuri Mafi Tsarki da kuma ƙofofin babban zaure.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]