Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 21 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Jehoshaphat rested with his ancestors, buried with them in the City of David; his son Jehoram reigned instead. Yehoshafat ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
2 Jehoram's brothers, sons of Jehoshaphat: Azariah, Jehiel, Zechariah, Azariah, Michael, Shephatiah. All these were sons of Jehoshaphat king of Israel. ’Yan’uwan Yehoram, ’ya’yan Yehoshafat maza su ne, Azariya, Yehiyel, Zakariya, Azariyahu, Mika’ilu da Shefatiya. Dukan waɗannan su ne ’ya’yan Yehoshafat sarkin Isra’ila maza.
3 Their father gave them many gifts—silver, gold, precious things—and fortified cities in Judah, but gave the kingdom to Jehoram, because he was firstborn. Mahaifinsu ya ba su kyautai masu yawa na azurfa da zinariya da kayayyaki masu daraja, tare da birane masu katanga a Yahuda, amma ya ba da mulki ga Yehoram domin shi ne ɗan farinsa.
4 Once Jehoram rose over his father's kingdom, he grew strong and killed all his brothers with the sword, and also some of Israel's officials. Sa’ad da Yehoram ya kafa kansa sosai a bisa mulkin mahaifinsa, sai ya kashe dukan ’yan’uwansa da takobi tare da waɗansu sarakunan Isra’ila.
5 Jehoram was thirty-two years old when he became king, and he reigned eight years in Jerusalem. Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas.
6 He walked in the way of Israel's kings, as Ahab's house had done, for Ahab's daughter was his wife, and he did evil in our Father's eyes. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji.
7 Yet our Father would not destroy the house of David, because of the covenant he made with David, and his promise to give him and his sons a lamp forever. Duk da haka, domin alkawarin da Ubangiji ya yi wa Dawuda, Ubangiji bai so yă hallaka gidan Dawuda ba. Ubangiji ya riga ya yi alkawari zai ci gaba da riƙe fitila domin Dawuda da zuriyarsa har abada.
8 In Jehoram's days Edom rebelled against Judah's rule and set up their own king. A zamanin Yehoram, Edom ya tayar wa Yahuda ya kuma naɗa sarkinsa.
9 Jehoram crossed with his commanders and all his chariots. He rose at night and struck the Edomites surrounding him and the chariot commanders. Saboda haka Yehoram ya tafi can tare da shugabannin sojojinsa da kuma dukan keken yaƙinsa. Mutanen Edom suka kewaye shi da shugabannin keken yaƙinsa, amma ya tashi ya fatattaki su da dare.
10 Edom rebelled against Judah's rule to this day; Libnah also rebelled then, because he had abandoned our Father, the God of his ancestors. Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa.
11 He built high places on Judah's hills, led Jerusalem's people to prostitute themselves, and drew Judah astray. Ya gina masujadan kan tudu a tuddan Yahuda, ya kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, ya sa Yahuda suka kauce.
12 A letter came to him from Elijah the prophet: Your Father, God of your ancestor David, says: Because you haven't walked in the ways of your father Jehoshaphat, or the ways of Asa king of Judah, Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.
13 but walked like Israel's kings, led Judah and Jerusalem's people to be unfaithful, as Ahab's house led Israel, and killed your brothers—your father's house—men better than you, Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe ’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.
14 now your Father will strike your people, children, wives, and all your goods with a great plague. Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka, ’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi.
15 You will have a severe intestinal disease, until day by day your intestines come out. Kai kuma za ka kamu da ciwon hanji wanda zai yi ta cinka kowace rana sai har hanjinka sun fito.’ ”
16 Our Father stirred up against Jehoram the spirit of the Philistines and Arabs near the Cushites. Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram
17 They attacked Judah, invaded it, and seized all the goods found in the king's palace, plus his sons and wives, leaving him no son except Jehoahaz, his youngest. Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da ’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa.
18 After all this, our Father struck him with an incurable disease in his intestines. Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki.
19 In time, after two years, his intestines came out because of his disease, and he died in agony. His people made no fire for him, as they had for his ancestors. Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa.
20 He was thirty-two when crowned king; he reigned eight years in Jerusalem. He died unmourned, buried in the City of David, but not among the kings' tombs. Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya mutu, ba ma wanda ya kula, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda, amma ba a makabartan sarakuna ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]