Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 20 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Later, Moabites and Ammonites, with some Meunites, came to make war on Jehoshaphat. Bayan wannan, Mowabawa da Ammonawa tare da waɗansu Meyunawa suka zo su yaƙi Yehoshafat.
2 Messengers came and reported to Jehoshaphat, "A vast army comes against you from beyond the Dead Sea, from Edom, already at Hazazon-tamar" (En-gedi). Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat, “Ga babban runduna tana zuwa a kanka daga Edom, daga ƙetaren Teku, daga Aram. Ta ma kai Hazazon Tamar” (wato, En Gedi).
3 Jehoshaphat was afraid, so he set himself to seek our Father, and proclaimed a fast throughout Judah. A firgice, Yehoshafat ya yanke shawara yă nemi nufin Ubangiji, ya kuma yi shelar azumi a dukan Yahuda.
4 Judah gathered to seek our Father; from every town of Judah they came to seek him. Mutanen Yahuda suka taru gaba ɗaya don su nemi taimako daga wurin Ubangiji, tabbatacce suka fito daga kowane garin Yahuda don su neme shi.
5 Then Jehoshaphat stood up in the assembly of Judah and Jerusalem, in our Father's house, before the new courtyard. Sa’an nan Yehoshafat ya miƙe tsaye a taron Yahuda da Urushalima a haikalin Ubangiji a sabon filin
6 He said: "O our Father, God of our ancestors, are you not our Father in heaven? You rule all kingdoms of nations. Power and might are in your hand; none can stand against you. ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanninmu, ba kai ne Allah wanda yake sama ba? Kana mulki a bisa dukan mulkokin ƙasashe. Iko da girma suna a hannunka, kuma ba wanda zai iya tsayayya da kai.
7 Our Father, didn't you drive out this land's people before your people Israel, giving it forever to Abraham your friend's descendants? Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka?
8 They have lived in it and have built you a sanctuary in it for your name, saying, Sun yi zama a cikinta suka kuma yi gina wuri mai tsarki a cikinta domin Sunanka cewa,
9 if disaster comes on us—sword of judgment, plague, or famine—we'll stand before this house and before you, for your name is in this house, and cry out to you in our distress, and you'll hear and save. ‘In masifa ta zo mana, ko takobin hukunci, ko annoba ko yunwa, za mu tsaya a gabanka a gaban wannan haikalin da yake ɗauke da Sunanka, mu kuma yi kuka gare ka cikin azaba, za ka kuwa ji mu, ka cece mu.’
10 Now: Ammon, Moab, and Mount Seir—you would not let Israel invade them when they came from Egypt; Israel turned away from them and did not destroy them. “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.
11 See how they repay us, coming to drive us from the possession you gave us to inherit. Yau ga yadda suke so su biya mu. Su suke so su kore mu daga ƙasar da ka ba mu gādo.
12 Our Father, won't you judge them? We're powerless against this vast army coming against us; we don't know what to do, but our eyes are on you." Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Gama ba mu da ƙarfin fuskantar wannan babbar rundunar da take so ta yaƙe mu. Ba mu san abin da za mu yi ba, mu dai mun zuba maka ido.”
13 All Judah stood there before our Father, with their little ones, their wives, and their children. Dukan mazan Yahuda, tare da matansu da yaransu da ƙananansu, suka tsaya a gaban Ubangiji.
14 Then our Father's Spirit came on Jahaziel son of Zechariah, son of Benaiah, son of Jeiel, son of Mattaniah, a Levite of Asaph's line, amid the assembly. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron.
15 He said: "Listen, all Judah, Jerusalem's residents, and King Jehoshaphat. This is what our Father says to you: Do not fear or be terrified by this vast army—the battle isn't yours but our Father's. Ya ce, “Saurara, Sarki Yehoshafat da dukan waɗanda suke zama a Yahuda da Urushalima! Ga abin da Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku ji tsoro ko ku fid da zuciya saboda wannan babbar runduna. Gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah.
16 Tomorrow go down against them: they're climbing the Ziz ascent; you'll find them at the valley's end, facing the Jeruel wilderness. Gobe ku fito ku gangara ku yaƙe su. Za su yi ta haurawa ta Mashigin Ziz, ku kuwa za ku same su a ƙarshen kwari a Hamadan Yeruwel.
17 You won't need to fight this battle. Take your places, stand firm, and watch our Father rescue you, Judah and Jerusalem. Don't fear or lose heart. March out against them tomorrow, for our Father is with you.'" Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’ ”
18 Jehoshaphat bowed face-down, and all Judah and Jerusalem's people fell in worship before our Father. Yehoshafat ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada a gaban Ubangiji.
19 Then the Levites from the Kohathites and Korahites stood to praise our Father, Israel's God, with a loud voice raised high. Sa’an nan waɗansu Lawiyawa daga Kohatawa da Korayawa suka tashi tsaye suka yabe Ubangiji, Allah na Isra’ila, da babbar murya sosai.
20 At dawn they went out to Tekoa's wilderness. As they went out, Jehoshaphat stood and said, "Hear me, Judah and people of Jerusalem. Trust your Father and you'll stand firm; trust his prophets and you'll succeed." Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.”
21 After consulting the people, Jehoshaphat appointed singers to our Father to praise his holy splendor, marching ahead of the army: "Give thanks to our Father, for his faithful love endures forever." Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa, “Ku yi godiya ga Ubangiji, gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
22 As they began to sing and praise, our Father set ambushes against the Ammonites, Moabites, and the people of Mount Seir who were attacking Judah, and they were struck down. Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi.
23 Ammon and Moab turned against Mount Seir's people to destroy and annihilate them; once Seir's people were finished, Ammon and Moab turned and slaughtered each other. Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna.
24 When Judah reached the wilderness lookout and looked toward the vast army, they saw only corpses fallen on the ground—no one had escaped. Sa’ad da mutanen Yahuda suka zo wurin da yake fuskantar hamada, suka duba ta wajen babban rundunar, sai suka ga gawawwaki birjik a ƙasa; babu wani wanda ya kuɓuta.
25 Jehoshaphat and his people came to plunder the dead, finding abundant goods, clothing, and valuables—too much to carry, so gathering it took three days. Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna kwasar ganimar saboda yawanta.
26 On day four, they gathered at the Valley of Beracah and praised our Father there—so it's named Valley of Beracah to this day. A rana ta huɗu sai suka taru a Kwarin Beraka, inda suka yabi Ubangiji. Wannan ne ya sa ake kiransa Kwarin Beraka har wa yau.
27 All the men of Judah and Jerusalem, Jehoshaphat leading, returned there with joy, for our Father gave them joy over their enemies. Sa’an nan Yehoshafat ya jagoranci dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka dawo da farin ciki zuwa Urushalima, gama Ubangiji ya ba su dalilin farin ciki a kan abokan gābansu.
28 They entered Jerusalem with harps, lyres, and trumpets, and went to the house of our Father. Suka shiga Urushalima suka shiga haikalin Ubangiji da kiɗin molaye da sarewa da kuma garayu.
29 Fear of our Father fell on all the surrounding kingdoms when they heard our Father fought Israel's enemies. Tsoron Allah ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji yadda Ubangiji ya yi yaƙi a kan abokan gāban Isra’ila.
30 So Jehoshaphat's kingdom was at peace, for his Father gave him rest on every side. Mulkin Yehoshafat kuwa ya zauna lafiya, gama Allahnsa ya ba shi hutu a kowane gefe.
31 Jehoshaphat reigned over Judah, crowned at thirty-five, twenty-five years in Jerusalem; his mother, Azubah daughter of Shilhi. Ta haka Yehoshafat ya yi mulki a bisa Yahuda. Yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba ce, ’yar Shilhi.
32 He walked in his father Asa's ways, never turning aside, doing right in our Father's eyes. Ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa bai kuwa kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
33 Yet the high places stayed; the people still had not set their hearts on their ancestors' God. Duk da haka ba a kawar da masujadai kan tudu ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.
34 Jehoshaphat's other acts, first to last, are in Jehu son of Hanani's records, found in the Book of Kings of Israel. Sauran ayyukan mulkin Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a tarihin Yehu ɗan Hanani, waɗanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra’ila.
35 Later Jehoshaphat king of Judah allied with Ahaziah king of Israel, who did evil. Daga baya, Yehoshafat sarkin Yahuda ya haɗa kai da Ahaziya sarkin Isra’ila, wanda yake da laifin mugunta.
36 He joined with him to build a fleet of trading ships to go to Tarshish, built at Ezion-geber. Ya yarda da shi su gina jiragen ruwan kasuwanci. Bayan aka gina waɗannan a Eziyon Geber,
37 Eliezer son of Dodavahu of Mareshah prophesied against Jehoshaphat: "For allying with Ahaziah, our Father broke your work apart." The ships wrecked and couldn't sail to Tarshish. Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]