Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 19 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Jehoshaphat king of Judah returned safely to his house in Jerusalem. Sa’ad da Yehoshafat sarkin Yahuda ya dawo zuwa fadansa a Urushalima lafiya,
2 Jehu son of Hanani the seer met King Jehoshaphat and asked, "Should you help the wicked and love those who hate our Father? For this, wrath from our Father is on you. Yehu mai duba, ɗan Hanani, ya fita don yă tarye shi, ya kuma ce wa sarki, “Ya yi kyau ke nan da ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji? Da yake ka yi haka fushin Ubangiji yana a kanka
3 Still, good is found in you: you cleared the Asherah poles from the land and set your heart to seek our Father." Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da ginshiƙan Ashera a ƙasar, ka kuma sa zuciyarka a kan neman Allah.”
4 Jehoshaphat lived in Jerusalem, then went out again among the people, from Beersheba to Ephraim's hill country, turning them back to our Father, God of their ancestors. Yehoshafat ya zauna a Urushalima, ya kuma fita yana shiga cikin mutane daga Beyersheba zuwa ƙasar tudun Efraim ya kuma juyar da su ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
5 He appointed judges in the land, in all the fortified cities of Judah, city by city. Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar.
6 He told the judges, "See what you do—you judge not for people but for our Father, and he is with you in every case you decide. Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.
7 Now let fear of our Father be on you. Watch and act, for with our Father there is no injustice, no favoritism, no bribery." Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”
8 Also in Jerusalem, Jehoshaphat appointed some Levites, priests, and heads of Israel's ancestral families to render the judgment of our Father and to settle disputes; they returned to Jerusalem. A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.
9 He commanded them: "Act this way, in fear of our Father, faithfully and wholeheartedly. Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku.
10 Whenever your brothers in their cities bring you a dispute—over bloodshed, or over law and commandment, statutes and rulings—warn them, so they don't incur guilt before our Father, bringing wrath on you and your brothers. Do this, and you will not incur guilt. Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.
11 Now, Amariah the chief priest oversees you in every matter of our Father; Zebadiah son of Ishmael, leader of Judah's tribe, in every matter of the king. The Levites serve as officials before you. Be strong and act—may our Father be with those who do good." “Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji, Zebadiya ɗan Ishmayel kuwa, shugabanku a kan dukan al’amuran da suka shafi sarki, Lawiyawa kuma za su zama a matsayin manya a gabanku. Ku yi abubuwa da ƙarfin hali, bari kuma Ubangiji yă kasance tare da masu yin gaskiya.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]