Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 22 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The people of Jerusalem made his youngest son Ahaziah king in his place, since the raiders who came with the Arabs into the camp had killed all the older sons. So Ahaziah son of Jehoram king of Judah became king. Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.
2 Ahaziah became king at twenty-two and reigned one year in Jerusalem. His mother was Athaliah, granddaughter of Omri. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.
3 He too followed the ways of Ahab's house, for his mother counseled him to do evil. Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.
4 He did evil in our Father's eyes, like Ahab's house, for after his father's death they were his counselors, to his ruin. Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.
5 He followed their advice too, joining Joram son of Ahab, Israel's king, to fight Hazael king of Aram at Ramoth-gilead, where the Arameans wounded Joram. Ya kuma bi shawararsu sa’ad da ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab sarkin Isra’ila don yă yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Sai Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;
6 So he returned to Jezreel to recover from the wounds he received at Ramah fighting Hazael king of Aram. Ahaziah son of Jehoram king of Judah went down to Jezreel to see Joram son of Ahab, because he was wounded. saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni.
7 Ahaziah's downfall came from our Father when he visited Joram. On arriving, he went out with Jehoram against Jehu son of Nimshi, whom our Father had anointed to destroy the house of Ahab. Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab.
8 As Jehu carried out judgment on Ahab's house, he found Judah's officials and Ahaziah's nephews who served Ahaziah, and killed them. Yayinda Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya sami fadawan Yahuda da kuma ’ya’yan dangin Ahaziya maza, waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su.
9 He searched for Ahaziah, who was captured while hiding in Samaria. They brought him to Jehu and killed him, then buried him, saying, "He is Jehoshaphat's son, who sought our Father with all his heart." So Ahaziah's house had no one strong enough to hold the kingdom. Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.
10 When Athaliah, Ahaziah's mother, saw her son was dead, she set out to destroy all the royal offspring of Judah's house. Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan ’yan gidan sarautar Yahuda.
11 But Jehoshabeath the king's daughter took Joash son of Ahaziah, stealing him from among the royal sons about to be killed, and hid him with his nurse in a bedroom. So Jehoshabeath, King Jehoram's daughter, Jehoiada the priest's wife and Ahaziah's sister, hid him from Athaliah, so she did not kill him. Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.
12 He stayed hidden with them in the house of our Father six years while Athaliah reigned over the land. Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]