Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 23 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In the seventh year Jehoiada took courage and made a covenant with the commanders of hundreds—Azariah son of Jeroham, Ishmael son of Jehohanan, Azariah son of Obed, Maaseiah son of Adaiah, and Elishaphat son of Zichri. A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri.
2 They traveled through Judah, gathered the Levites from all its cities and the family heads of Israel, and came to Jerusalem. Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima,
3 The whole assembly made a covenant with the king in the house of our Father. Jehoiada told them, "Look, the king's son will reign, as our Father promised about David's sons. dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.
4 Do this: a third of you—priests and Levites entering on the Sabbath—will be gatekeepers at the thresholds. Yanzu ga abin da za ku yi, shi ne, kashi ɗaya bisa uku na firistoci da Lawiyawa waɗanda za su yi aiki a Asabbaci su yi tsaro a ƙofofi,
5 A third at the king's house, a third at the Gate of the Foundation, and all the people in the courts of the house of our Father. kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.
6 Let no one enter the house of our Father except the priests and the serving Levites; they may enter, for they are holy. Everyone else is to keep guard for our Father. Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi.
7 The Levites must surround the king, each with weapon in hand; whoever enters the house is to be put to death. Stay with the king wherever he comes and goes." Lawiyawa za su tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makamansa a hannunsa. Duk wanda ya shiga haikali sai a kashe shi. Ku tsaya kusa da sarki a duk inda ya tafi.”
8 The Levites and all Judah did exactly as Jehoiada the priest commanded. Each took his men—those coming on duty the Sabbath with those going off—since Jehoiada the priest did not dismiss any of the divisions. Lawiyawa da dukan mutanen Yahuda suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa, waɗanda suke aiki a Asabbaci da waɗanda suka gama aiki, gama Yehohiyada firist bai bar waɗansu ɓangarori ba.
9 Jehoiada the priest gave the commanders of hundreds King David's spears and large and small shields, kept in our Father's house. Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah.
10 He stationed all the people, each with weapon in hand, from the south side of the temple to the north side, surrounding the altar, the temple, and the king. Ya kuma sa dukan mutane, kowanne da makaminsa a hannunsa, kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikali.
11 They brought out the king's son, crowned him, gave him the covenant law, and made him king. Jehoiada and his sons anointed him and shouted, "Long live the king!" Yehohiyada da ’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”
12 Hearing the sound of people running and praising the king, Athaliah came to them at our Father's house. Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji.
13 She looked—there was the king standing by his pillar at the entrance, officers and trumpeters beside him, all the people of the land rejoicing and blowing trumpets, singers with instruments leading the praise. Then Athaliah tore her clothes and shouted, "Treason! Treason!" Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”
14 Jehoiada the priest summoned the commanders of hundreds over the army and said, "March her out through the ranks; kill with the sword anyone who follows her." For the priest had said, "Do not kill her in the house of our Father." Yehohiyada firist ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku fitar da ita tsakanin sojoji ku kuma kashe duk wanda ya bi ta da takobi.” Gama firist ya ce, “Kada ku kashe ta a haikalin Ubangiji.”
15 They seized her; when she reached the Horse Gate's entrance by the king's house, they killed her there. Saboda haka suka kama ta yayinda take kaiwa mashigin Ƙofar Doki a filin fada, a can suka kashe ta.
16 Then Jehoiada made a covenant among himself, all the people, and the king to be our Father's people. Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji.
17 All the people went to Baal's temple and tore it down, smashed its altars and idols, and killed Mattan, Baal's priest, before the altars. Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan.
18 Jehoiada put the Levite priests in charge of our Father's house, whom David had assigned there, to offer burnt offerings to our Father, as written in Moses' law, with joy and song as David had ordered. Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.
19 He stationed gatekeepers at the gates of our Father's house so no one unclean in any way could enter. Ya kuma sa matsaran ƙofofi a ƙofofin haikalin Ubangiji don kada wani da ba shi da tsarki yă shiga.
20 He took the commanders of hundreds, the nobles, the rulers of the people, and all the people of the land, and brought the king down from the house of our Father, through the Upper Gate into the king's house, and seated him on the royal throne. Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin Ubangiji. Suka shiga fada ta Ƙofar Bisa suka kuma zaunar da sarki a kujerar sarauta,
21 All the people of the land rejoiced, and the city grew calm, for Athaliah was killed with the sword. sai dukan mutanen ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya samu zaman lafiya domin an kashe Ataliya da takobi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]