Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

2 Chronicles 24 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Joash became king at seven, and reigned forty years in Jerusalem. His mother Zibiah was from Beersheba. Yowash yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta a Urushalima shekara arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; ita daga Beyersheba.
2 Joash did what was right in our Father's eyes all the days of Jehoiada the priest. Yowash ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji duka shekarun Yehohiyada firist.
3 Jehoiada chose two wives for him, and Joash had sons and daughters. Yehohiyada ya zaɓi mata biyu dominsa, yana kuma da ’ya’ya maza da ’ya’ya mata.
4 Some time later, Joash set his heart on restoring the house of our Father. Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji.
5 He gathered the priests and Levites, told them, "Go to Judah's cities, collect money from all Israel yearly to repair your Father's house—hurry." But the Levites didn't hurry. Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba.
6 The king summoned Jehoiada the chief priest: "Why haven't you required the Levites to bring the tax from Judah and Jerusalem that Moses, our Father's servant, and the assembly set on Israel for the tent of testimony?" Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?”
7 Athaliah's sons, that wicked woman, broke into our Father's house and even used all the holy things of our Father's house in worship of the Baals. Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al.
8 At the king's order, they made a chest and set it outside our Father's house gate. Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji.
9 They announced in Judah and Jerusalem: bring our Father the tax Moses, our Father's servant, set on Israel in the wilderness. Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada.
10 All the officials and all the people rejoiced, bringing and dropping their gifts into the chest until full. Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika.
11 Whenever the Levites brought the chest to the king's officials and saw it full of money, the royal secretary and chief priest's officer emptied it and returned it to its place. Daily they collected much money. Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa.
12 The king and Jehoiada gave it to workers on our Father's house, who hired masons and carpenters to restore it, and iron and bronze workers to repair our Father's house. Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin.
13 Workers labored; repair progressed by their hands. They restored our Father's house to its form and strengthened it. Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi.
14 When finished, they brought the rest of the money to the king and Jehoiada, making from it articles for our Father's house: vessels for service and burnt offerings, dishes, gold and silver vessels. They offered burnt offerings in our Father's house continually, all Jehoiada's lifetime. Da suka gama, suka kawo sauran kuɗin wa sarki da Yehohiyada, da su ne kuwa aka yi kayayyaki domin hidima da kuma domin hadayun ƙonawa, haka kuma kwanoni da sauran kayayyakin zinariya da azurfa. Muddin Yehohiyada yana raye, aka riƙa kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.
15 Jehoiada grew old and full of years, then died; at his death he was 130 years old. Yanzu Yehohiyada ya tsufa kuma cike da shekaru, ya kuwa mutu yana da shekara ɗari da talatin.
16 They buried him in the City of David among the kings, for doing good in Israel toward our Father and his house. Aka binne shi tare da sarakuna a cikin Birnin Dawuda, saboda kirkin da ya yi a Isra’ila wa Allah da haikalinsa.
17 After Jehoiada died, Judah's officials came and bowed to the king, and he listened to them. Bayan mutuwar Yehohiyada, hafsoshin Yahuda suka zo suka yi mubaya’a wa sarki, ya kuma saurare su.
18 They abandoned our Father's house, God of their ancestors, served Asherah poles and idols—so anger came on Judah and Jerusalem for this guilt. Suka yashe haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa ginshiƙan Ashera da kuma gumaka. Saboda laifinsu, fushin Allah ya sauko a kan Yahuda da Urushalima.
19 Yet our Father sent them prophets to bring them back to himself; they warned them, but they wouldn't listen. Ko da yake Ubangiji ya aiki annabawa zuwa wurin mutane don su dawo da su gare shi, kuma ko da yake sun ba da shaida a kansu, ba su saurara ba.
20 Then the Spirit of our Father came on Zechariah son of Jehoiada the priest. He stood before the people and said, "This is what our Father says: Why break his commands? You won't succeed—you abandoned him, so he abandons you." Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ”
21 They conspired against him, stoning him in our Father's house courtyard at the king's command. Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji.
22 King Joash forgot the kindness Zechariah's father Jehoiada had shown him and killed his son. As Zechariah was dying he said, "May our Father see and require it." Sarki Yowash bai tuna da alherin da Yehohiyada mahaifin Zakariya ya nuna masa ba, sai ya kashe ɗansa, wanda ya ce yayinda yake mutuwa, “Bari Ubangiji yă dubi wannan yă kuma sāka maka.”
23 At the turn of the year Aram's army attacked Joash, invaded Judah and Jerusalem, killed all the people's officials, sent all their plunder to Damascus's king. Da shekara ta kewaye, mayaƙan Aram suka yi gāba da Yowash suka kai hari wa Yahuda da Urushalima suka kuma kashe dukan shugabannin mutane, suka aika da dukan ganima zuwa ga sarkinsu a Damaskus.
24 Though Aram's army came with few men, our Father gave a much larger army into their hand, since Judah abandoned our Father, the God of their ancestors. So judgment fell on Joash. Ko da yake mayaƙan Arameyawa sun zo da mutane kaɗan kawai, Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan sojojin Yahuda mafi yawa, don mutanen Yahuda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu, aka kuma hukunta Yowash.
25 When the Arameans left, leaving him badly wounded, his servants conspired against him for the blood of Jehoiada the priest's son, killing him on his bed. He died and was buried in the City of David, not in the kings' tombs. Sa’ad da Arameyawa suka janye, suka bar Yowash da mummunan rauni. Hafsoshinsa suka haɗa baki a kansa saboda kisan ɗan Yehohiyada firist da ya yi, suka kashe shi a kan gadonsa. Ta haka ya mutu aka kuma binne shi makabartan sarakuna.
26 Conspirators against him: Zabad son of Shimeath, Ammonite woman, and Jehozabad son of Shimrith, Moabite woman. Waɗanda suka haɗa bakin kuwa su ne Zabad ɗan Shimeyat wata mutuniyar Ammon da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.
27 His sons, the many prophecies against him, and rebuilding our Father's house are written in the Book of the Kings' commentary; his son Amaziah reigned in his place. Labarin ’ya’yansa maza, annabce-annabce masu yawa game da shi, da tarihin gyaran haikalin Allah suna a rubuce a rubuce-rubuce a littafin sarakuna. Amaziya ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]