Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Romans 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 So you have no excuse, whoever you are, when you judge another—in judging them you condemn yourself, since you do the same things. Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa.
2 Now we know that our Father's judgment rightly falls on those who do such things. Yanzu mun san cewa hukuncin Allah a kan masu aikata waɗannan abubuwa daidai ne.
3 Do you think, whoever judges others for such things while doing them yourself, that you'll escape our Father's judgment? Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?
4 Or do you despise the riches of his kindness and restraint and patience, not realizing that our Father's kindness is meant to lead you to repentance? Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?
5 But because of your hard, unrepentant heart, you are storing up wrath for yourself, for the day of wrath when our Father's righteous judgment will be revealed. Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci.
6 He will repay each person according to what they have done. Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.”
7 To those who through persistent good work seek glory, honor, and immortality, he will give eternal life. Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami.
8 But those who are self-seeking, reject the truth, and follow wickedness face wrath and rage. Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu.
9 Trouble and distress for everyone who does evil—the Jew first, then the Greek, Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai,
10 but glory, honor, and peace for all who do good—Jew first, then Greek too. amma akwai ɗaukaka, girma da salama ga duk mutumin da yake aikata alheri, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai.
11 For our Father shows no favoritism. Gama Allah ba ya nuna bambanci.
12 Sinners without the law also perish without it; sinners under the law will be judged by it. Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su.
13 For not those who hear the law are righteous before our Father, but those who obey it will be justified. Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci.
14 Indeed, when Gentiles, who do not have the law, do by nature what the law requires, the law is at work within them, even though they do not have the law. Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar.
15 They show the law's work written on their hearts, their conscience bearing witness, and their conflicting thoughts accusing or defending them. To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su.
16 This happens on the day our Father judges everyone's secrets through Jesus Christ—so my gospel says. Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.
17 But if you call yourself a Jew, rely on the law, and boast in our Father, To, kai, da kake kiran kanka mutumin Yahuda; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah;
18 if you know our Father's will and approve what is excellent because you are instructed by the law, in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka;
19 if you're convinced you are a guide for the blind, a light for those in darkness, in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu,
20 a corrector of the foolish, teacher of the immature, holding in the law the shape of knowledge and truth. mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya
21 You teach others—do you not teach yourself? You preach against stealing—do you steal? to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata?
22 You who tell others not to commit adultery—do you commit it? You who detest idols—do you rob temples? Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi?
23 You who boast in the law, do you dishonor our Father by breaking the law? Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar?
24 As it is written: "Our Father's name is blasphemed among the nations because of you." Kamar yadda yake a rubuce, “Ana saɓon sunan Allah a cikin Al’ummai saboda ku.”
25 Circumcision helps if you keep the law; break it, and your circumcision becomes being uncircumcised. Kaciya tana da amfani in kana kiyaye dokar, amma in kana karya dokar, ka zama kamar ba a yi maka kaciya ba.
26 So if the uncircumcised keep the law's requirements, won't their uncircumcision be counted as circumcision? In marasa kaciya suna kiyaye dokar, ashe, ba za a ɗauke su kamar an yi musu kaciya ba?
27 The physically uncircumcised who keep the law will judge you who, with the letter and circumcision, break the law. Wanda ba shi da kaciya ta jiki duk da haka yana biyayya da dokar zai iya hukunta ka, kai da kake karya dokar, ko da yake kana da rubutaccen tsarin dokar an kuma yi maka kaciya.
28 For being a Jew isn't merely about the outside, nor circumcision merely about the body. Mutum ba mutumin Yahuda ba ne in shi mutumin Yahuda ne kawai a jiki, haka kuma kaciya ba a waje ko a jiki kawai ba.
29 Rather, one is a Jew inwardly, circumcision being of the heart, by the Spirit, not the written code; that one's praise is not from people but from our Father. A’a, mutum mutumin Yahuda ne in shi mutumin Yahuda ne a zuci; kuma kaciya ita ce kaciya ta zuci, ta wurin Ruhu, ba ta wurin rubutaccen doka ba. Irin wannan mutum yana samun yabo daga Allah ne, ba ɗan adam ba.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]