Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Romans 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 What advantage, then, does the Jew have? Or what is the value of circumcision? To, mece ce ribar zama mutumin Yahuda, ko kuwa mene ne amfanin kaciya?
2 Much in every way. First of all, they were entrusted with the very words of our Father. Akwai riba ƙwarai ta kowace hanya! Da farko dai, su ne aka danƙa wa kalmomin nan na Allah.
3 What then? If some were unfaithful, will their unfaithfulness nullify the faithfulness of our Father? Amma a ce waɗansu ba su da bangaskiya fa? Rashin bangaskiyarsu nan zai shafe amincin Allah?
4 No! Let our Father be true, though every person is a liar. As it is written: "You are proven right in your words, and win when judged." Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana, ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”
5 But if our wrongdoing highlights our Father's righteousness, what do we say? Is our Father unjust to bring wrath on us? (I speak in human terms.). Amma in rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah a fili, me za mu ce ke nan? Za mu ce Allah ya yi rashin adalci ke nan da ya saukar da fushinsa a kanmu? (Ina magana kamar yadda mutum zai yi ne.)
6 Certainly not! For then how could our Father judge the world? Sam, ko kusa! Da a ce haka ne, ta yaya Allah zai shari’anta duniya?
7 But if my lie makes our Father's truth overflow to his glory, why am I still judged as a sinner? Wani zai iya ce, “In a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka ƙara ɗaukaka shi, to, ta yaya zan zama mai zunubi, in ƙaryata tana kawo ɗaukaka ga Allah?”
8 Why not say, as some slander us as saying, "Let's do evil so good may come"? Their judgment is deserved. In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.
9 What then? Are we better off? Not at all—we've already charged that Jews and Greeks alike are all under sin's grip, To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi.
10 as it is written: "There is no one righteous, not even one; Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;
11 no one understands; no one seeks our Father. babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
12 All have turned away; together they have become worthless; no one does good, not even one. Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.”
13 Their throat is an open grave; they use their tongues to deceive." "The venom of snakes is under their lips. “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne, harsunansu suna yin ƙarya.” “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
14 Their mouth is full of cursing and bitterness. “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”
15 Their feet are swift to shed blood; “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;
16 ruin and misery mark their ways, hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,
17 and the way of peace they have not known. ba su kuma san hanyar salama ba.”
18 There is no fear of our Father before their eyes." “Babu tsoron Allah a idanunsu.”
19 We know whatever the law says applies to those under it, so every mouth is silenced and the whole world stands accountable to our Father. Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.
20 No one is made right before him by works of the law; the law brings awareness of sin. Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.
21 But now, apart from the law, our Father's righteousness has been revealed, testified to by the Law and the Prophets. Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci.
22 This righteousness of our Father comes through faith in Jesus Christ, to all who believe, for there's no distinction, Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci,
23 since all have sinned and fall short of the glory of our Father, gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,
24 and are justified freely by his grace through the redemption that is in Christ Jesus. an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.
25 Our Father presented him as the atoning sacrifice, through faith in his blood, to show his righteousness, since in his patience he had passed over sins committed before, Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba
26 to show his righteousness now, so he is both just and the justifier of whoever trusts in Jesus. ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.
27 Where then is boasting? Excluded. By what law? Of works? No—by the law of faith. To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya.
28 For we maintain that a person is justified by faith apart from works of the law. Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba.
29 Or is our Father the Father of Jews only? Not the Father of Gentiles too? Yes, of Gentiles too, Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma,
30 since our Father is one, he will justify the circumcised by faith and the uncircumcised through faith. da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin.
31 Do we cancel the law through this faith? Never—we confirm the law. To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]