Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Obadiah 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 The vision of Obadiah. This is what the Sovereign Father says about Edom: We have heard a message from our Father, and an envoy sent among the nations—"Rise up! Let us rise against her for battle!" Wahayin Obadiya. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom. Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa, An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa, “Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.”
2 Look, I will make you small among the nations; you will be utterly despised. “Duba, zan maishe ki ƙarama a cikin al’ummai; za a rena ki ƙwarai.
3 The pride of your heart has deceived you, you who live in the clefts of the rock, whose home is the heights, who say to yourself, "Who can bring me down to the ground?" Fariyar zuciyarki ta yaudare ki, ke da kike zama can bisa duwatsu kika kuma yi gidanki a kan ƙwanƙoli, ke da kike ce wa kanki, ‘Wa zai iya saukar da ni ƙasa?’
4 Though you soar like the eagle, though you set your nest among the stars, from there I will bring you down, declares our Father. Ko da yake kina firiya kamar gaggafa kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari, daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji.
5 If thieves came to you, if plunderers came by night—how you have been destroyed!—wouldn't they steal only what they wanted? If grape-pickers came to you, wouldn't they leave some grapes behind? “In ɓarayi suka zo miki, in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare, kash, bala’i zai jira ki ba abin da suke so ne kawai za su sata ba? In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki, ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba?
6 How Esau has been ransacked, his hidden treasures plundered! Amma za a washe Isuwa ƙaƙaf, a kuma yaye ɓoyayyiyar dukiyarsa!
7 All your allies have driven you to the border; those who were at peace with you have deceived you and overpowered you; those who shared your table have set a trap beneath you—and you don't even see it. Dukan waɗanda kike tarayya da su, za su kore ki zuwa iyaka; abokanki kuma za su yaudare ki, su kuma sha ƙarfinki; waɗanda suke cin abincinki, za su sa miki tarko, amma ba za ki gane ba.
8 Will I not on that day, declares our Father, destroy the wise men of Edom and wipe out understanding from the mountain of Esau? “A wannan rana,” in jin Ubangiji, “zan hallaka masu hikimar Edom, zan shafe mutane masu fahima a duwatsun Isuwa.
9 Your warriors will be shattered, Teman, so that everyone on the mountain of Esau will be cut down in the slaughter. Jarumawanki, ya Teman, za su razana, za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.
10 Because of the violence you did to your brother Jacob, shame will cover you, and you will be cut off forever. Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub, za ki sha kunya; za a hallaka ki har abada.
11 On the day you stood by and did nothing, on the day strangers carried off his wealth and foreigners entered his gates and cast lots for Jerusalem—you too were like one of them. A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.
12 But do not gloat over your brother in the day of his misfortune; do not rejoice over the people of Judah in the day of their ruin; do not boast loudly in the day of distress. Bai kamata ki rena ɗan’uwanki a ranar masifarsa ba, ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu, ko ki yi fariya sosai a ranar wahalarsu.
13 Do not enter the gate of my people in the day of their calamity; you of all people, do not gloat over his disaster in the day of his calamity; do not loot his wealth in the day of his calamity. Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba.
14 Do not stand at the crossroads to cut down his fugitives; do not hand over his survivors in the day of distress. Bai kamata ki tsaya a mararraba don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba, ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu a ranar wahalarsu ba.
15 For the day of our Father is near for all the nations. As you have done, it will be done to you; your deeds will come back on your own head. “Ranar Ubangiji ta yi kusa don dukan al’ummai. Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku; ayyukanku za su koma a kanku.
16 For as you drank on my holy mountain, so all the nations will drink continually; they will drink and swallow and become as though they had never been. Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki, haka dukan al’ummai za su yi ta sha, za su sha, su kuma sha su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.
17 But on Mount Zion there will be deliverance, and it will be holy, and the house of Jacob will possess their inheritance. Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto; Dutsen zai zama mai tsarki, gidan Yaƙub kuma zai mallaki gādonsa.
18 The house of Jacob will be a fire and the house of Joseph a flame, and the house of Esau will be stubble; they will burn it and consume it, and there will be no survivor of the house of Esau, for our Father has spoken. Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta, gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta; gidan Isuwa zai zama kamar tattaka, za a kuma sa masa wuta yă ƙone. Babu wanda zai tsira daga gidan Isuwa.” Ni Ubangiji na faɗa.
19 Those of the Negev will possess the mountain of Esau, and those of the foothills the land of the Philistines; they will possess the land of Ephraim and the land of Samaria, and Benjamin will possess Gilead. Mutane daga Negeb za su mamaye duwatsun Isuwa, mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki ƙasar Filistiyawa. Za su mamaye filayen Efraim da Samariya, Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.
20 The exiles of this army of the people of Israel will possess the land of the Canaanites as far as Zarephath, and the exiles of Jerusalem who are in Sepharad will possess the cities of the Negev. Wannan ƙungiyar Isra’ilawan da aka kwashe zuwa bauta da suke a Kan’ana za su mallaki ƙasar har zuwa Zarefat; waɗannan da aka kwashe zuwa bauta daga Urushalima da suke a Sefarad za su mallaki garuruwan Negeb.
21 Deliverers will go up to Mount Zion to rule the mountain of Esau, and the kingdom will belong to our Father. Masu kawo ceto za su haura zuwa Dutsen Sihiyona don su yi mulkin duwatsun Isuwa. Ubangiji ne zai yi mulki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]