Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Jonah 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Now the word of our Father came to Jonah son of Amittai: Maganar Ubangiji ta zo wa Yunana ɗan Amittai cewa,
2 "Get up, go to Nineveh, that great city, and cry out against it, for their evil has risen before me." “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”
3 But Jonah set out to flee to Tarshish, away from our Father's presence. He went down to Joppa, found a ship bound for Tarshish, paid its fare, and boarded to go with them to Tarshish, away from our Father's presence. Amma Yunana ya gudu daga Ubangiji ya nufi Tarshish. Ya gangara zuwa Yaffa, inda ya sami jirgin ruwa mai shirin tashi daga tashar. Bayan ya biya kuɗin tafiya, sai ya shiga jirgi ya kama hanya zuwa Tarshish don yă tsere wa Ubangiji.
4 Then our Father hurled a great wind at the sea; a violent storm arose, and the ship seemed about to break apart. Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa.
5 The sailors were terrified, each crying to his own god. They threw the ship's cargo into the sea to lighten it. But Jonah had gone below deck, where he lay fast asleep. Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa.
6 The captain came and said, "How can you sleep? Get up, call on your god! Maybe he will notice us, and we won't perish." Sai kyaftin ɗin ya je wajensa ya ce masa, “Don me kake barci? Tashi ka kira bisa ga allahnka! Mai yiwuwa yă ji mu, yă cece mu don kada mu hallaka.”
7 The men said to each other, "Come, let's cast lots to find who's to blame for this disaster on us." They cast lots, and it fell on Jonah. Matuƙan jirgin suka ce wa juna, “Ku zo, mu jefa ƙuri’a mu ga wa ke da alhakin wannan masifa.” Sai suka jefa ƙuri’a, ƙuri’ar kuwa ta fāɗa a kan Yunana.
8 They said to him, "Tell us—you who have brought this disaster on us—what do you do? Where do you come from? What is your country? What people are you from?" Saboda haka suka tambaye shi suka ce, “Yanzu, gaya mana, dalilin da ya sa wannan masifa ta zo mana? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Ina ne ƙasarka? Daga wacce kabila ce ka fito?”
9 He answered, "I am a Hebrew, and I fear our Father, the Father of heaven, who made the sea and the dry land." Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”
10 Then the men were terrified and said, "What have you done?" For they knew he was fleeing from our Father's presence, because he had told them. Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.)
11 Then they said to him, "What should we do to you to calm the sea for us?"—for the sea grew stormier and stormier. Sai tekun ya daɗa rikicewa. Sai suka tambaye shi, “Me za mu yi da kai domin tekun yă daina hauka?”
12 He told them, "Lift me up and throw me into the sea, and it will calm for you. I know this great storm came on you because of me." Ya amsa musu ya ce, “Ku ɗauke ni ku jefa a cikin teku, tekun zai kwanta. Na san cewa laifina ne ya jawo wannan babban hadirin da ya auka muku.”
13 Instead the men rowed hard to reach land, but could not, for the sea grew wilder and wilder against them. Maimakon mutanen su yi haka, sai suka yi ƙoƙari su tura jirgin ruwan zuwa bakin teku. Amma ba su iya ba, saboda iskar ta sa tekun ya yi ta ƙara hauka.
14 So they cried out to our Father: "Please, God, don't let us die for taking this man's life. Don't hold us guilty of innocent blood, for you have done as you pleased." Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.”
15 Then they picked Jonah up and hurled him into the sea, and the raging sea grew calm. Sa’an nan suka ɗauki Yunana suka jefar da shi daga jirgin, sai tekun ya kwanta.
16 The men then feared our Father greatly, offered a sacrifice to our Father, and made vows. Ganin haka sai mutanen suka cika da tsoron Ubangiji, suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya, suka yi wa’adi da shi.
17 Now our Father appointed a great fish to swallow Jonah, and Jonah was in the belly of the fish three days and three nights. Amma Ubangiji ya tanada wani babban kifi da zai haɗiye Yunana, Yunana kuwa ya yi yini uku da dare uku a ciki cikin kifin.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]