Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Malachi 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Look, I am sending my messenger, and he will prepare the way before me. Then suddenly the Lord whom you are seeking will come to his temple—the messenger of the covenant in whom you delight. Look, he is coming, says the Father of heaven's armies. “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
2 "But who can endure the day he comes? Who can stand when he appears? He is like a refiner's fire, like a launderer's soap. Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki.
3 He will sit refining and purifying silver; he will purify Levi's sons and refine them like gold and silver, and they will bring offerings to our Father in righteousness. Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci.
4 Then Judah and Jerusalem's offering will please our Father, as in days past, as in former years." Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga Ubangiji, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya.
5 I will come near to judge you, a swift witness against sorcerers, adulterers, those who swear falsely, who cheat the worker of his wages, oppress the widow and orphan, push aside the foreigner, and do not fear me, says the Father of heaven's armies. “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
6 For I, your Father, do not change; therefore you, children of Jacob, have not been destroyed. “Ni Ubangiji ba na canjawa. Shi ya sa ku zuriyar Yaƙub, ba a hallaka ku ƙaƙaf ba.
7 Since your ancestors' days you have turned from my statutes and not kept them. Return to me, and I will return to you, says the Father of heaven's armies. But you ask, 'How are we to return?' Tun zamanin kakanninku, kun juye wa ƙa’idodina baya, ba ku kuma kiyaye su ba. Ku komo gare ni, ni kuma zan koma gare ku,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya za mu koma gare ka?’
8 Will a person rob their Father? Yet you rob me. But you ask, 'How have we robbed you?' In the tenth and the offerings. “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ “A wajen zakka da hadayu.
9 You are cursed with a curse, for you are robbing me—the whole nation of you. Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi.
10 Bring the full tenth into the storehouse, so there's food in my house. Test me in this, says the Father of heaven's armies, and see if I won't open heaven's windows for you and pour out blessing for you until there's no more need. Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
11 I will rebuke the devourer for you, so it will not destroy your ground's fruit, and your vine in the field will not fail to bear, says the Father of heaven's armies. Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
12 Then all nations will call you blessed, for you will be a land of delight, says the Father of heaven's armies. “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
13 Your words were harsh against me, says our Father. But you ask, 'What have we said against you?' “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji. “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’
14 You said, 'Serving God is useless. What have we gained by keeping his charge and walking as mourners before the Father of heaven's armies?' “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki?
15 Now we call the arrogant blessed. Those who do evil prosper; they even test God and escape. A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ”
16 Then those who feared our Father spoke to one another, and he listened and heard. A scroll of remembrance was written before him for those who fear him and treasure his name. Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.
17 They will be mine, says the Father of heaven's armies, on the day I act, my treasured possession. I will spare them as a father spares his son who serves him. “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima.
18 Once more you will see the difference between the righteous and the wicked, between one who serves our Father and one who does not serve him. Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]