Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Malachi 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Now, priests, this command is for you. “Yanzu fa wannan gargaɗi dominku ne, ku firistoci.
2 If you won't listen, or take it to heart to honor my name, says the Father of heaven's armies, I will send the curse on you and curse your blessings. I have already cursed them, because you don't take it to heart. In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
3 I will rebuke your offspring and smear manure on your faces—the manure of your feasts—and you will be carried off with it. “Saboda ku zan tsawata wa zuriyarku; zan watsa kashin dabbobin hadayunku a fuskokinku, a kuma kwashe ku tare da shi.
4 Then you will know I sent this command to you, so my covenant with Levi stands, says the Father of heaven's armies. Za ku kuwa san cewa ni ne na aika muku da wannan gargaɗi domin alkawarina da Lawi yă ci gaba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
5 "My covenant with him was life and peace; I gave them to him to be held with reverence, and he revered me and trembled before my name. “Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai.
6 True instruction was in his mouth, no wrong on his lips. He walked with me in peace and integrity, and turned many from sin. Umarnin gaskiya yana a bakinsa, ba a kuma sami wani ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya tare da ni cikin salama da adalci, ya kuwa juyo da mutane masu yawa daga zunubi.
7 A priest's lips guard knowledge, and people seek instruction from his mouth, for he is the messenger of the Father of heaven's armies. “Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki.
8 But you turned from the way and made many stumble by your instruction; you corrupted the covenant of Levi, says the Father of heaven's armies. Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
9 So I made you despised and low before all the people, because you haven't kept my ways but shown favoritism in your instruction." “Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.”
10 Don't we all have one Father? Didn't one Father create us? Why betray each other, desecrating our fathers' covenant? Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna?
11 Judah is unfaithful; a detestable thing is done in Israel and Jerusalem. Judah has desecrated our Father's holy place, which he loves, and married the daughter of a foreign god. Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah.
12 May our Father cut off from Jacob's tents the man who does this—anyone at all—even one bringing an offering to the Father of heaven's armies. Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.
13 And a second thing you do: you cover our Father's altar with tears, weeping and groaning, because he no longer regards the offering or accepts it gladly from your hand. Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki.
14 You ask, "Why?" Because our Father witnessed between you and the wife of your youth, whom you betrayed—though your companion, your wife by covenant. Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.
15 Didn't the Father make you one with your wife? Body and spirit, you are his. And what does he want? Godly children from your union. So guard your spirit; let no one betray the wife of his youth. Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.
16 "For I hate divorce," says our Father, the Father of Israel, "and whoever covers his garment with violence," says the Father of heaven's armies. So guard your spirit; do not be unfaithful. “Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.
17 You have worn out our Father with your words. Yet you ask, "How have we worn him out?" By saying, "All who do evil are good in his sight, and he delights in them"—or, "Where is the Father of justice?" Kun sa Ubangiji Maɗaukaki ya gaji da maganganunku. Sai kuka ce, “Yaya muka sa ya gaji?” Kun yi haka ta wurin cewa, “Duk waɗanda suke aikata mugunta, mutanen kirki ne a gaban Ubangiji, yana kuwa jin daɗinsu,” kuna kuma cewa, “Ina Allah mai adalci yake?”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]