Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

Malachi 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 This is the word of our Father to Israel, delivered through Malachi. Annabci, wannan ita ce maganar Ubangiji ga Isra’ila ta wurin Malaki.
2 "I have loved you," says our Father. "But you ask, 'How have you loved us?' Wasn't Esau Jacob's brother?" declares our Father. "Yet I loved Jacob, “Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub,
3 but Esau I hated. I made his hill country wasteland, left his inheritance to desert jackals." amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”
4 Edom may say, "We are shattered, but we will rebuild the ruins." But the Father of heaven's armies says: "They may build, but I will tear down. They will be called the Wicked Land, the people our Father stays angry with forever." Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji.
5 Your own eyes will see it, and you'll say, 'Great is our Father—beyond Israel's borders!' Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’
6 "A son honors his father, a servant his master. If I am a father, where is my honor? If a master, where is my respect? says the Father of heaven's armies to you priests who despise my name. But you ask, 'How have we despised your name?'" “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’
7 "You put unclean food on my altar, then ask, 'How have we made you unclean?' By calling our Father's table despised. “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne.
8 When you offer a blind animal, isn't that evil? Offer the lame and sick—isn't that evil? Present it to your governor—will he be pleased with you? Will he accept you?" says the Father of heaven's armies. Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.
9 "Now plead with our Father to be gracious to us. With such offerings from your hands, will he accept any of you?" says the Father of heaven's armies. “To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.
10 "If only one of you would shut the doors, so you would not light useless fires on my altar! I take no pleasure in you," says the Father of heaven's armies, "and I will accept no offering from your hands. “Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
11 From sunrise to sunset my name will be great among the nations. Everywhere incense and pure offerings will be brought to my name, because my name will be great among the nations," says the Father of heaven's armies. Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
12 "But you desecrate it, saying the Sovereign Father's table is unclean and its food may be despised." “Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’
13 "You say, 'What a burden!' and snort at it in contempt," says the Father of heaven's armies. "You bring stolen, lame, and diseased animals as offerings—should I accept them from you?" says our Father. Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji.
14 "Cursed is the cheat who has a sound male in his flock and vows it, but sacrifices a defective animal to the Sovereign Father. For I am a great King," says the Father of heaven's armies, "and my name is to be feared among the nations." “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]