Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

John 1 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 In the beginning was the Word, and the Word was with our Father, and the Word was God. Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
2 He was in the beginning with our Father. Yana nan tare da Allah tun farar farawa.
3 All things were made through him, and without him not one thing was made that was made. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
4 In him was life, and the life was the light of all people. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
5 The light shines in the darkness, and the darkness has not overcome it. Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.
6 There came a man sent from our Father, whose name was John. Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.
7 He came as a witness, to bear witness about the light, so that all might believe through John's witness. Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.
8 He was not the light, but came to bear witness about the light. Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.
9 The true light, which gives light to everyone, was coming into the world. Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.
10 He was in the world. The world came into being through him, yet did not know him. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.
11 He came to his own, and his own people did not receive him. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.
12 But to all who received him, believing in his name, he gave the right to become children of our Father, Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah
13 children born not of blood nor of the will of flesh nor of the will of man, but of our Father. ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
14 The Word became flesh and lived among us. We saw his glory, the glory of the one and only Son from the Father, full of grace and truth. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
15 John testified about him, crying out, "This is the one I meant: he who comes after me outranks me, since he existed before me." (Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”)
16 For from his fullness we have all received, grace upon grace. Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.
17 For the law was given through Moses; grace and truth came through Jesus Christ. Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.
18 No one has ever seen our Father; the one and only God, close beside the Father, has made him known. Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.
19 This is John's testimony, when the Jews sent priests and Levites from Jerusalem to ask him, "Who are you?" To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne.
20 He confessed, and did not deny, but confessed, "I am not the Christ." Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”
21 So they asked him, "What then? Are you Elijah?" "I am not," he said. "Are you the Prophet?" "No," he answered. Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.”
22 So they asked, "Who are you? We need to give an answer to those who sent us. What do you say about yourself?" A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”
23 He said, "I'm the voice of one crying out in the wilderness, 'Make straight the way of the Lord,' as the prophet Isaiah said." Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”
24 Now they had been sent from the Pharisees. To, waɗansu Farisiyawan da aka aika
25 They asked him, "Why baptize, then, if you're not the Christ, nor Elijah, nor the Prophet?" suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”
26 John answered them, "I baptize with water, but among you stands one you do not know, Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.
27 even he who comes after me, whose sandal strap I am not worthy to untie." Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
28 These things took place in Bethany across the Jordan, where John was baptizing. Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
29 The next day, seeing Jesus coming toward him, he said, "Look! The Lamb of our Father—Jesus—who takes away the sin of the world! Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
30 This is the one I meant: 'After me comes a man who ranks before me, because he was before me.' Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’
31 I didn't know him, but I came baptizing with water so he would be revealed to Israel." Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”
32 John testified: "I saw the Holy Spirit descend from heaven like a dove and remain on him. Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.
33 I didn't know him, but the one who sent me to baptize with water told me, 'The one you see the Holy Spirit come down and stay on—he is the one who baptizes with the Holy Spirit.' Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
34 And I have seen and have borne witness that this is the Son of our Father." Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
35 The next day John was standing again with two of his disciples, Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa.
36 and looking at Jesus as he walked by, he said, "Look! The Lamb of our Father!" Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
37 The two disciples heard him say this, and they followed Jesus. Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.
38 Jesus turned, saw them following, and asked, "What do you seek?" They said, "Rabbi" (meaning Teacher), "where do you stay?" Da juyewa, sai Yesu ya ga suna bin sa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi” (wato, “Malam”), “ina kake da zama?”
39 He told them, "Come and you will see." So they went and saw where he was staying, and remained with him that day—about four in the afternoon. Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.” Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen sa’a ta goma ce kuwa.
40 One of the two who heard John speak and followed Jesus was Andrew, Simon Peter's brother. Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu.
41 He first found his own brother Simon and told him, "We've found the Messiah" (meaning Christ). Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi).
42 He brought him to Jesus. Jesus looked at him and said, "You are Simon the son of John. You will be called Cephas" (meaning Peter). Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan).
43 The next day, Jesus decided to leave for Galilee. He found Philip and said, "Follow me." Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”
44 Now Philip was from Bethsaida, the city of Andrew and Peter. Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne.
45 Philip found Nathanael and told him, "We've found the one Moses wrote of in the Law and the prophets—Jesus, son of Joseph, from Nazareth." Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”
46 Nathanael said, "Can anything good come from Nazareth?" Philip said, "Come and see." Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.”
47 Jesus saw Nathanael approaching and said of him, "Look—a true Israelite, with no deceit in him!" Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci.”
48 Nathanael asked him, "How do you know me?" Jesus answered, "Before Philip called you, while you were under the fig tree, I saw you." Natanayel ya yi tambaya ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka.”
49 Nathanael answered him, "Rabbi, you are the Son of our Father! You are the King of Israel!" Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”
50 Jesus answered him, "You believe because I told you I saw you under the fig tree? You'll see greater things than these." Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”
51 He told him, "Truly, truly, I say to you, you will see heaven opened, and our Father's angels ascending and descending on the Son of Man." Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]